Ku yi rige-rige zuwa ga gafarar Allah da Aljannarsa wadda aka yi wa muminai alqawarinta. (Aljanna) ita ce babbar ni’ima daga Allah, Yana yin baiwarta ga wanda Ya ga dama. Don haka ka sanya manufarka ta zamo ita ce rabauta da samun yardarsa.
Rigegeniya Wurin Aikata Alheri
Aljanna ba ta wanda ya voye fushinsa ba ce kawai, a’a, ta haxa da wanda ya ciyar a halin yalwa da halin qunci ya kuma yi wa mutane afuwa. Hanyar zuwa ga samun yardar Allah a cike take da ayyukan kyautatawa (ihsani).
Ku yi rige-rige zuwa neman gafara daga Ubangijinku da Aljanna wadda faxinta kamar faxin sammai da qasa yake, an tanade ta don waxanda suka yi imani da Allah da manzanninsa. Wannan falalar Allah ce da Yake ba da ita ga wanda Ya ga dama. Allah kuwa Ma’abocin falala ne, Mai girma
Suratul Hadid-21
Ku yi rige-rige zuwa ga gafarar Allah da Aljannarsa wadda aka yi wa muminai alqawarinta. (Aljanna) ita ce babbar ni’ima daga Allah, Yana yin baiwarta ga wanda Ya ga dama. Don haka ka sanya manufarka ta zamo ita ce rabauta da samun yardarsa.
#Gafarar_Allah #Rige-rige_Zuwa_Aikata Alheri.
Aljanna yalwatacciya ce kamar sammai da qasa. An tanadeta ne don muminai. Babbar kyauta daga Allah yana bayar da ita ga wanda ya ga dama.
Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara ta musamman daga wajen Ubangijinku, da kuma Aljanna wadda faxinta yake daidai da sammai da qasa, an yi tanadinta domin masu taqawa ,(Su ne) waxanda suke ciyarwa a cikin halin yalwa da halin qunci, kuma masu voye fushi kuma masu yin afuwa ga mutane. Allah kuwa Yana son masu kyautatawa" (Aali Imran: 133-134
Aljanna ba ta wanda ya voye fushinsa ba ce kawai, a’a, ta haxa da wanda ya ciyar a halin yalwa da halin qunci ya kuma yi wa mutane afuwa. Hanyar zuwa ga samun yardar Allah a cike take da ayyukan kyautatawa (ihsani).
#Rahama #Kyautatawa.
“Yi gaggawa zuwa ga samun gafarar Allah da Aljannarsa mai girma, ta hanyar ciyarwa da haquri, da voye fushi, waxannan su ne siffofin masu taqawa. Duk wanda yake yi wa mutane afuwa, to zai sami soyayyar Allah.”
Kuma (ka tuna) ma’abocin kifi (wato Yunusa) lokacin da ya tafi yana cike da fushi[1], sannan ya zaci cewa ba za Mu quntata masa ba, sai ya kira (Mu) a cikin duffai[2] yana cewa: “Ba wani abin bauta da gaskiya sai Kai (ya Allah), tsarki ya tabbata a gare Ka, lallai ni na kasance cikin azzalumai!,Sai Muka amsa masa Muka kuma tserar da shi daga baqin ciki. Kamar haka kuwa Muke tserar da muminai” (Al-Anbiya: 87-88)
A lokacin da rayuwa ta yi maka qunci, duhu ya lulluve zuciyarka, to ka tuna addu’ar ma’abocin kifi (wato Yunus): (Watau), la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin.
Allah Ta’ala Yana amsa wa duk wanda ya tsantsanta tuba gare shi.
#Tuba_Karvar_Addu’a
Yayin da ake cikin baqin ciki da damuwa, fakewa da Allah shi ne tsira. Kamar yadda ma’abocin kifi (Yunus) ya tsira daga duhun cikin kifi. Allah ya tserar da duk wanda ya yi imani ya nemi agajinsa
Shi ne Wanda Yake tafiyar da ku a tudu da cikin ruwa, har lokacin da kuka shiga cikin jiragen ruwa, (jiragen) kuwa suka yi gudu da su tare da iska mai daxi, suka kuma yi farin ciki da su (jiragen) sai kuma wata iska mai qarfi ta zo musu; raqumin ruwa kuma ya zo musu ta kowane wuri, suka kuma tabbatar cewa dai su kam an rutsa da su, sai kuma suka roqi Allah suna masu tsarkake addini gare Shi (suna cewa): “Tabbas idan Ka tserar da mu daga wannan, lalle haqiqa za mu zamo cikin masu godiya.”To lokacin da Ya tserar da su sai ga su suna varna a bayan qasa ba da gaskiya ba. Ya ku mutane, haqiqa (sakamakon) varnarku a kanku kawai yake; ku xan ji daxin rayuwar duniya; sannan (daga qarshe) zuwa gare Mu ne makomarku take, sannan mu ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa
Suratu Yunus:22-23
A lokacin da musibu suka tsananta a garemu, mu kuma koma ga Allah tare da ikhlasi, to tsira zai zo ta inda ba ma tsammani, sai dai qalubale na haqiqa shi ne biyan wannan tseratarwar bayan an tsira ta hanyar godiya da rashin dulmiyewa cikin wuce iyaka.
#Godiya._Ga Allah_Cika Ni’ima
A yayin da abubuwa za su rikice mana, rayuwa ta yi tsanani a garemu, a nan za mu gane rauninmu a gaban girman Allah, mu fake a wurinsa da ikhlasi. Sai dai ibtila’i na haqiqa shi ne, yadda halinmu zai kasance bayan mun tsira.
An qawata wa mutane son sha’awace-sha’awace na mata da ‘ya’ya da dukiya mai yawa abar tarawa ta zinariya da azurfa da kuma kiwatattun dawaki da dabbobi na gida da amfanin gona. Waxannan duk morewa ce ta rayuwar duniya; Allah kuwa a wurinsa ne kyakkyawar makoma take
Suratu Ali-Imra :14
Qyaleqyali a wannan duniyar abu ne mai ruxarwa, wanda ya haxa da samun dukiya da tara zurriya da alamomin qarfi. Sai dai dukkansu suna komawa abubuwan da suke gushewa. Don haka yin qoqari wurin samun abin da ke wurin Allah shi ne abin nema na haqiqa, kuma shi ne kyakkyawar makoma a lahira, kuma ita ce babbar rabauta.
#Lahira-Alherin- #Duniya-Mai-Gushewa Ne
Abubuwan sha’awace-sha’awace da suka qunshi dukiya da xa da qawa ta duniya suna fizgar mutane. Sai kuma suna kasancewa abubuwa ne da suke na xan lokaci. Amma kyakkyawar makoma kuwa tana wurin Allah ga dukkan wanda ya kyautata niyya ya yi qoqarin samun xaukaka da himmarsa.
Ku sani cewa, ita dai rayuwar duniya ba wata aba ba ce sai wasa da sharholiya da qyale-qyale da kuma fariya a tsakaninku da takara wajan nuna yawan dukiya da ‘ya’yaye; ta yi kama da ruwan saman da tsirransa suka bai wa manoma sha’awa, sannan duk ya bushe, sai ka gan shi fatsi-fatsi, sannan kuma ya zama dudduga; a lahira kuwa akwai azaba mai tsanani da gafara daga Allah da kuma yarda. Rayuwar duniya ba komai ba ce sai jin daxi mai ruxi
Suratul Hadid:20
Duniya ba wata aba ba ce face wasa da sharholiya da qyale-qyale da mutane suke yi wa junansu fariya da ita, suke gasar tara dukiyoyi da ‘ya’yaye a cikinta. Misalinta (duniyar) kuwa shi ne, kamar shuka ce ta za ta bushe ta zama dudduga a ranar lahira. Sakamako na haqiqa kuwa shi ne: ko dai azaba mai tsanani ko kuma gafara da samun yarda daga Allah.
#Duniya_Mai Gushewa ce #Lahira_Wanzajjiya ce
Rayuwar duniya tana bayyana a sura mai haskakawa bisa siffar wasa da qyale-qyale, sai dai kuma makomarta kamar makomar shukar da za ta bushe ce ta zama dudduga. Ka tuna fa cewa, lahira ita ce matabbata, ko dai a samu gafara da yardar Allah ko kuma azaba mai tsanani.
Duniya_Jin daxi Mai Ruxarwa#Lahira_Ita Tafi Alheri.
Kyakkyawan (abu) da mummuna ba za su zama xaya ba. To ka ture mummuna da abin da ya fi kyau, to sai ka ga wanda yake tsakaninsa da kai gaba ce, ya zamanto kamar wani masoyi ne na qut ،da qut Ba kowa ake bai wa wannan kyakkyawar xabi’ar ba sai waxanda suka yi haquri, ba kowa ake bai wa ita ba sai mai babban rabo
Suratu Fussilat-34
Kyakkyawan (abu) da mummuna ba za su zama xaya ba. Ka kasance cikin masu ture mummuna da kyakkyawa, sau da yawa maqiyinka zai iya canjawa ya koma masoyi na qut da qut. Wannan matsayi ne da babu mai kaiwa gareshi sai masu haquri da ma’abota babban rabo.
#Kyakkyawa-da Haquri #Xabi’un-Musulunci
Duk yadda zalinci ya kai, ka kawar (da mummuna) da abin da ya fi kyau, maqiyinka zai iya canjawa ya koma aboki makusanci. Babu waxanda ke samun wannan falalar sai rayuka masu haquri da kuma ma’abota babban rabo.
Kuma idan kun yi tafiya a bayan qasa, to babu laifi a kanku ku yi sallar qasaru[1], in kun ji tsoron kafirai su fitine ku[2]. Lalle kafirai sun kasance maqiya ne, masu bayyana qiyayya a gare ku
Suratun Nisa’i:101
Allah Ta’ala Ya halatta yin qasaru yayin tafiya da lokacin jihadi don tsare muminai daga cutarwar kafirai. Rahamar Musulunci tana bayyana wurin sauqaqe ibadu yayin da buqatar hakan ta taso.
#Sauqaqe-Salla #Rahamar-Musulunci
Yayin da kake zaune a gari da lokacin da kake a halin tafiya, ka tuna cewa, Musulunci addini ne na rahama da sauqi, Musulunci ya halatta yin qasaru a salla yayin da ka ji tsoron fitinar abokan gaba. Maqiyinku a bayyane yake, sai dai kuma rahamar Allah tafi yalwa
Allah yana cewa: “Idan kuma suka ji maganar banza sai su kau da kai daga gare ta, sai kuma su ce: “(Sakamakon) ayyukanmu yana gare mu, ku kuma na ayyukanku yana gare ku, kun kuvuta daga gare mu, ba ruwanmu da wawaye!”’” (Al-Qasas: 55)
Lokacin da za ka bijirar da kanka ga yasasshiyar magana da zancen banza, ka tuna cewa, mumini na gaskiya yana kawar da kai daga barinsa, yana zavar kuvuta. (Sakamakon) Ayyukanmu yana gare mu, ku kuma ayyukanku yana gare ku, ba ruwanmu da wawaye.
#Xaukaka_Ta Hanyar Xabi’u #Kawar da kai daga varna.
Kawar da kai da maganar banza na daga cikin xabi’un bayin Allah Mai Rahama. Muna cewa: “(Sakamakon) Ayyukanmu yana gare mu, ku kuma na ayyukanku yana gare ku, ba ma neman jayayya tare wawaye, kuvuta ita ce hanyarmu.
Shin ka ga wanda ya mayar da son zuciyarsa (shi ne) abin bautarsa, to yanzu kai za ka zama mai kiyaye shi (daga bin son zuciyarsa)?
Suratul Furqan:43
Duk wanda ya biye wa son zuciyarsa, ya mayar da shi abin bautarsa, to zai nisanta daga gaskiya. Kada ka zama mai kiyaye wanda ya zavi vatansa (a kan gaskiya), don kowane mutum sai an tambaye shi a kan abubuwan da ya zavar wa kansa.
Bin_son zuciya #Nauyin_Xaixaiku
Kashedinka da sanya bin son zuciya ya zamar maka abin bauta, don (yin hakan) tafarkin vata ne. Mu ba kowa ba ne face masu faxakarwa da yin nasiha. Saboda kowane (mutum) za a tambaye shi game da abubuwan da ya zavar wa kansa a gaban Allah.