إِذَا زُلۡزِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ زِلۡزَالَهَا
Idan aka girgiza qasa matuqar girgiza ta
Tarayya :
وَأَخۡرَجَتِ ٱلۡأَرۡضُ أَثۡقَالَهَا
Qasar kuma ta fitar da nauyaye-nauyayenta[1]
1- Watau ta fitar da mutanen da ke cikinta da sauran ma’adanan qarqashinta.
وَقَالَ ٱلۡإِنسَٰنُ مَا لَهَا
Mutum kuma ya ce: “Me ya same ta?”
يَوۡمَئِذٖ تُحَدِّثُ أَخۡبَارَهَا
A wannan ranar ne za ta ba da labaranta[1]
1- Watau ayyukan da aka yi a kanta masu kyau da munana.
بِأَنَّ رَبَّكَ أَوۡحَىٰ لَهَا
Don Ubangijinka Ya umarce ta (da yin haka)
يَوۡمَئِذٖ يَصۡدُرُ ٱلنَّاسُ أَشۡتَاتٗا لِّيُرَوۡاْ أَعۡمَٰلَهُمۡ
A wannan ranar mutane za su fito a warwatse, don a nuna musu ayyukansu
فَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٍ خَيۡرٗا يَرَهُۥ
To duk wanda ya yi aikin alheri daidai da zarra zai gan shi
وَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖ شَرّٗا يَرَهُۥ
Wanda kuma duk ya yi aikin sharri daidai da zarra zai gan shi