ٱقۡرَأۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلَّذِي خَلَقَ
Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, Wanda Ya yi halitta
Tarayya :
خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِنۡ عَلَقٍ
Ya halicci mutum daga gudan jini[1]
1- Watau bayan yana xigon maniyyi.
ٱقۡرَأۡ وَرَبُّكَ ٱلۡأَكۡرَمُ
Ka yi karatu alhali Ubangijinka Shi ne mafi karamci
ٱلَّذِي عَلَّمَ بِٱلۡقَلَمِ
Wanda Ya koyar ta (hanyar) alqalami
عَلَّمَ ٱلۡإِنسَٰنَ مَا لَمۡ يَعۡلَمۡ
Ya koyar da mutum abin da bai sani ba
كَلَّآ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَيَطۡغَىٰٓ
Tabbas! Lalle (jinsin) mutum haqiqa yana yin xagawa
أَن رَّءَاهُ ٱسۡتَغۡنَىٰٓ
Don ya ga kansa yana cikin wadata
إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلرُّجۡعَىٰٓ
Lalle kuma zuwa ga Ubangijinka ne makomar (taka) take
أَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي يَنۡهَىٰ
Ka ba ni labarin wanda yake hana
عَبۡدًا إِذَا صَلَّىٰٓ
Bawa yayin da ya yi salla
أَرَءَيۡتَ إِن كَانَ عَلَى ٱلۡهُدَىٰٓ
Ka ba ni labari idan (shi Bawan) ya kasance a kan shiriya
أَوۡ أَمَرَ بِٱلتَّقۡوَىٰٓ
Ko kuma ya yi umarni da taqawa
أَرَءَيۡتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰٓ
Ka ba ni labari idan (shi mai hanawar) ya qaryata ya kuma ba da baya
أَلَمۡ يَعۡلَم بِأَنَّ ٱللَّهَ يَرَىٰ
Shin bai sani ba cewa lalle Allah Yana ganin (sa)?
كَلَّا لَئِن لَّمۡ يَنتَهِ لَنَسۡفَعَۢا بِٱلنَّاصِيَةِ
A’aha! Tabbas idan bai hanu ba to za Mu ja shi ta makwarkwaxar kai
نَاصِيَةٖ كَٰذِبَةٍ خَاطِئَةٖ
Makwarkwaxar kai mai qaryatawa, mai aikata laifi
فَلۡيَدۡعُ نَادِيَهُۥ
To ya kirawo majalisar tasa
سَنَدۡعُ ٱلزَّبَانِيَةَ
Mu kuma lalle za Mu kirawo (mala’iku) zabaniyawa
كَلَّا لَا تُطِعۡهُ وَٱسۡجُدۡۤ وَٱقۡتَرِب۩
Faufau! Kada ka bi shi, ka kuma yi salla, ka kusanta (ga Allah)