وَٱلسَّمَآءِ وَٱلطَّارِقِ
Na rantse da sama da (tauraro) mai zuwa cikin dare
Tarayya :
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلطَّارِقُ
Me ya sanar da kai mai zuwa cikin dare?
ٱلنَّجۡمُ ٱلثَّاقِبُ
Tauraro ne mai keta (duhu) da haskensa
إِن كُلُّ نَفۡسٖ لَّمَّا عَلَيۡهَا حَافِظٞ
Ba wani rai face akwai mai tsaron sa
فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ مِمَّ خُلِقَ
To mutum ya duba mana, daga me aka halicce shi?
خُلِقَ مِن مَّآءٖ دَافِقٖ
An halicce shi ne daga wani ruwa mai ingizar juna[1]
1- Watau maniyyi.
يَخۡرُجُ مِنۢ بَيۡنِ ٱلصُّلۡبِ وَٱلتَّرَآئِبِ
Mai fita daga tsakanin tsatso da karankarma[1]
1- Watau daga tsakanin qashin bayan namiji da qasusuwan qirjinsa.
إِنَّهُۥ عَلَىٰ رَجۡعِهِۦ لَقَادِرٞ
Lalle Shi (Allah) Mai iko ne a kan dawo da shi
يَوۡمَ تُبۡلَى ٱلسَّرَآئِرُ
A ranar da za a bayyana asirai[1]
1- Watau abubuwan da suke cikin zukata na niyyoyi da aqidu da sauransu.
فَمَا لَهُۥ مِن قُوَّةٖ وَلَا نَاصِرٖ
To ba shi da wani qarfi ko wani mataimaki
وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلرَّجۡعِ
Na rantse da sama ma’abociyar dawo (da ruwa)
وَٱلۡأَرۡضِ ذَاتِ ٱلصَّدۡعِ
Da kuma qasa ma’abociyar tsagewa (shuka ta fito)
إِنَّهُۥ لَقَوۡلٞ فَصۡلٞ
Lalle shi (Alqur’ani) magana ce mai tsage gaskiya
وَمَا هُوَ بِٱلۡهَزۡلِ
Kuma shi ba zancen banza ba ne
إِنَّهُمۡ يَكِيدُونَ كَيۡدٗا
Lalle su (kafirai) suna qulla mummunan makirci
وَأَكِيدُ كَيۡدٗا
Ni kuma ina shirya musu mummunan sakamako
فَمَهِّلِ ٱلۡكَٰفِرِينَ أَمۡهِلۡهُمۡ رُوَيۡدَۢا
To sai ka saurara wa kafirai, ka saurara musu kaxan