إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتۡ
Idan sama ta tsattsage
Tarayya :
وَإِذَا ٱلۡكَوَاكِبُ ٱنتَثَرَتۡ
Idan kuma taurari suka farfaxo suka tarwatse
وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ فُجِّرَتۡ
Idan kuma koguna aka harhaxe su
وَإِذَا ٱلۡقُبُورُ بُعۡثِرَتۡ
Idan kuma qaburbura aka fito da matattun da ke cikinsu
عَلِمَتۡ نَفۡسٞ مَّا قَدَّمَتۡ وَأَخَّرَتۡ
Kowane rai ya san abin da ya gabatar da wanda ya jirkintar
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡإِنسَٰنُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ ٱلۡكَرِيمِ
Ya kai mutum, me ya ruxe ka ne game da Ubangijinka Mai karamci?
ٱلَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّىٰكَ فَعَدَلَكَ
Wanda Ya halicce ka Ya kuma daidaita ka Ya miqar da kai[1]?
1- Watau ya lura da girman ni’imar da ya yi masa yayin da bai yi masa irin halittar jaki ba ko ta biri ko ta kare.
فِيٓ أَيِّ صُورَةٖ مَّا شَآءَ رَكَّبَكَ
Ya harhaxa ka cikin irin surar da Ya ga dama?
كَلَّا بَلۡ تُكَذِّبُونَ بِٱلدِّينِ
A’a dai, kawai dai kuna qaryata ranar sakamako ne
وَإِنَّ عَلَيۡكُمۡ لَحَٰفِظِينَ
Kuma lalle akwai masu kula da ku[1]
1- Watau mala’iku.
كِرَامٗا كَٰتِبِينَ
Masu daraja marubuta
يَعۡلَمُونَ مَا تَفۡعَلُونَ
Suna sane da abin da kuke aikatawa
إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ لَفِي نَعِيمٖ
Lalle mutanen kirki tabbas suna cikin ni’ima
وَإِنَّ ٱلۡفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٖ
Lalle kuma fajirai tabbas suna cikin (wutar) Jahima
يَصۡلَوۡنَهَا يَوۡمَ ٱلدِّينِ
Za su qonu da ita ranar sakamako
وَمَا هُمۡ عَنۡهَا بِغَآئِبِينَ
Kuma su ba masu rabuwa ne da ita ba
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ
Kuma kai me ya sanar da kai mece ce ranar sakamako?
ثُمَّ مَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ
Sannan me ya sanar da kai mece ce ranar sakamako?
يَوۡمَ لَا تَمۡلِكُ نَفۡسٞ لِّنَفۡسٖ شَيۡـٔٗاۖ وَٱلۡأَمۡرُ يَوۡمَئِذٖ لِّلَّهِ
(Ita ce) ranar da wani rai ba ya mallakar wani amfani ga wani rai; al’amari kuwa (gaba xayansa) a wannan ranar yana ga Allah