عَمَّ يَتَسَآءَلُونَ
Game da me suke tambayar junansu?
Tarayya :
عَنِ ٱلنَّبَإِ ٱلۡعَظِيمِ
Game da labari ne mai girma[1]
1- Watau Alqur’ani wanda ya qunshi magana a kan ranar alqiyama da za a yi wa mutane hisabi a ciki.
ٱلَّذِي هُمۡ فِيهِ مُخۡتَلِفُونَ
Wanda game da shi ne suke savani
كَلَّا سَيَعۡلَمُونَ
Ba haka ne ba, da sannu za su sani[1]
1- Watau za su san mummunan sakamakon qaryata shi da suke yi.
ثُمَّ كَلَّا سَيَعۡلَمُونَ
Sannan kuma tabbas, da sannu za su sani
أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ مِهَٰدٗا
Yanzu ba mu sanya qasa shimfixa ba?
وَٱلۡجِبَالَ أَوۡتَادٗا
Duwatsu kuma turaku?
وَخَلَقۡنَٰكُمۡ أَزۡوَٰجٗا
Muka kuma halicce ku bibbiyu (watau maza da mata)?
وَجَعَلۡنَا نَوۡمَكُمۡ سُبَاتٗا
Muka kuma sanya baccinku (ya zama) hutu?
وَجَعَلۡنَا ٱلَّيۡلَ لِبَاسٗا
Muka kuma sanya dare (ya zama) sutura[1]?
1- Watau idan ya lulluve da duhunsa.
وَجَعَلۡنَا ٱلنَّهَارَ مَعَاشٗا
Muka kuma sanya yini don neman abinci?
وَبَنَيۡنَا فَوۡقَكُمۡ سَبۡعٗا شِدَادٗا
Muka kuma gina (sammai) bakwai qarfafa a sama da ku?
وَجَعَلۡنَا سِرَاجٗا وَهَّاجٗا
Muka kuma sanya wata fitila mai tsananin haske (watau rana)?
وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلۡمُعۡصِرَٰتِ مَآءٗ ثَجَّاجٗا
Muka kuma saukar da ruwa mai kwarara daga (hadari) da ya batse da ruwa?
لِّنُخۡرِجَ بِهِۦ حَبّٗا وَنَبَاتٗا
Domin Mu fitar da qwayoyi da tsirrai da shi?
وَجَنَّـٰتٍ أَلۡفَافًا
Da kuma gonaki masu itatuwa sassarqe da juna?
إِنَّ يَوۡمَ ٱلۡفَصۡلِ كَانَ مِيقَٰتٗا
Lalle ranar hukunci ta kasance (rana ce) mai tsayayyen lokaci
يَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِ فَتَأۡتُونَ أَفۡوَاجٗا
Ranar da za a busa qaho[1] sai ku zo jama’a-jama’a
1- Watau busa ta biyu.
وَفُتِحَتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتۡ أَبۡوَٰبٗا
Aka kuma buxe sama sai ta zama qofofi[1]
1- Watau inda mala’iku za su yi ta sauka da umarnin Allah.
وَسُيِّرَتِ ٱلۡجِبَالُ فَكَانَتۡ سَرَابًا
Aka kuma tafiyar da duwatsu sai suka zama kawalwalniya
إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتۡ مِرۡصَادٗا
Lalle Jahannama ta kasance madakata ce
لِّلطَّـٰغِينَ مَـَٔابٗا
Makoma ce ga masu xagawa
لَّـٰبِثِينَ فِيهَآ أَحۡقَابٗا
Masu zama ne a cikinta shekaru aru-aru
لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرۡدٗا وَلَا شَرَابًا
Ba sa xanxanar wani sanyi a cikinta ko wani abin sha
إِلَّا حَمِيمٗا وَغَسَّاقٗا
Sai tafasasshen ruwa da ruwan mugunya
جَزَآءٗ وِفَاقًا
Don sakayya da ta dace
إِنَّهُمۡ كَانُواْ لَا يَرۡجُونَ حِسَابٗا
Lalle su sun kasance ba sa tsoron hisabi
وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا كِذَّابٗا
Suka kuma qaryata ayoyinmu iyakar qaryatawa
وَكُلَّ شَيۡءٍ أَحۡصَيۡنَٰهُ كِتَٰبٗا
Kuma kowane abu Mun qididdige shi a rubuce
فَذُوقُواْ فَلَن نَّزِيدَكُمۡ إِلَّا عَذَابًا
(Sai a ce da su): To ku xanxana, don ba za Mu qara muku ba sai dai wata azaba.”