Sura: Suratut Tahrim

Aya : 1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ لِمَ تُحَرِّمُ مَآ أَحَلَّ ٱللَّهُ لَكَۖ تَبۡتَغِي مَرۡضَاتَ أَزۡوَٰجِكَۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Ya kai wannan Annabi, don me kake haramta abin da Allah Ya halatta maka[1]; kana neman yardar matanka. Allah kuwa Mai gafara ne, Mai jin qai


1- Watau kamar yin sa-xaka da kuyangarsa ko shan zuma.


Sura: Suratut Tahrim

Aya : 2

قَدۡ فَرَضَ ٱللَّهُ لَكُمۡ تَحِلَّةَ أَيۡمَٰنِكُمۡۚ وَٱللَّهُ مَوۡلَىٰكُمۡۖ وَهُوَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡحَكِيمُ

Haqiqa Allah Ya farlanta muku kaffarar rantse-rantsenku[1]. Allah kuwa (Shi ne) Majivincin al’amarinku, Shi ne kuma Masani, Mai hikima


1- Kamar yadda aka yi bayani a Suratul Ma’ida aya ta 89.


Sura: Suratut Tahrim

Aya : 3

وَإِذۡ أَسَرَّ ٱلنَّبِيُّ إِلَىٰ بَعۡضِ أَزۡوَٰجِهِۦ حَدِيثٗا فَلَمَّا نَبَّأَتۡ بِهِۦ وَأَظۡهَرَهُ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ عَرَّفَ بَعۡضَهُۥ وَأَعۡرَضَ عَنۢ بَعۡضٖۖ فَلَمَّا نَبَّأَهَا بِهِۦ قَالَتۡ مَنۡ أَنۢبَأَكَ هَٰذَاۖ قَالَ نَبَّأَنِيَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡخَبِيرُ

Kuma (ka tuna) lokacin da Annabi ya asirta wani zance ga wata daga matansa[1], to lokacin da ta ba da labarinsa Allah kuma Ya bayyana masa shi, sai ya sanar da (ita) sashinsa ya kuma kawar da kai ga wani sashi; to yayin da ya ba ta labarinsa sai ta ce: “Wane ne ya ba ka labarin wannan?” Sai ya ce: “Masani Mai zuzzurfan ilimi ne Ya ba ni labarinsa.”


1- Ita ce Hafsa ().


Sura: Suratut Tahrim

Aya : 4

إِن تَتُوبَآ إِلَى ٱللَّهِ فَقَدۡ صَغَتۡ قُلُوبُكُمَاۖ وَإِن تَظَٰهَرَا عَلَيۡهِ فَإِنَّ ٱللَّهَ هُوَ مَوۡلَىٰهُ وَجِبۡرِيلُ وَصَٰلِحُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۖ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ بَعۡدَ ذَٰلِكَ ظَهِيرٌ

Idan (ku biyun)[1] kuka tuba zuwa ga Allah, to haqiqa zukatanku sun riga sun karkata; idan kuwa kuka haxe masa kai, to lalle Allah Shi ne Majivincin al’amarinsa, da Jibrilu da salihan muminai; mala’iku ma bayan wannan masu taimakawa ne


1- Watau Hafsa da A’isha, Allah ya yarda da su.


Sura: Suratut Tahrim

Aya : 5

عَسَىٰ رَبُّهُۥٓ إِن طَلَّقَكُنَّ أَن يُبۡدِلَهُۥٓ أَزۡوَٰجًا خَيۡرٗا مِّنكُنَّ مُسۡلِمَٰتٖ مُّؤۡمِنَٰتٖ قَٰنِتَٰتٖ تَـٰٓئِبَٰتٍ عَٰبِدَٰتٖ سَـٰٓئِحَٰتٖ ثَيِّبَٰتٖ وَأَبۡكَارٗا

Tabbas idan ya sake ku Ubangijinsa zai musanya masa wasu matan fiye da ku (su zama) Musulmi, muminai, masu biyayya, masu tuba, masu bautar Allah, masu azumi, zawarawa da ‘yanmata



Sura: Suratut Tahrim

Aya : 6

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ قُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ وَأَهۡلِيكُمۡ نَارٗا وَقُودُهَا ٱلنَّاسُ وَٱلۡحِجَارَةُ عَلَيۡهَا مَلَـٰٓئِكَةٌ غِلَاظٞ شِدَادٞ لَّا يَعۡصُونَ ٱللَّهَ مَآ أَمَرَهُمۡ وَيَفۡعَلُونَ مَا يُؤۡمَرُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku kare kawunanku da iyalanku daga wuta (wadda) makamashinta mutane ne da duwatsu, masu kula da ita mala’iku ne masu kaushin hali, masu tsananin gaske, ba sa sava wa Allah abin da Ya umarce su, suna kuma aikata abin da ake umartar su



Sura: Suratut Tahrim

Aya : 7

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَا تَعۡتَذِرُواْ ٱلۡيَوۡمَۖ إِنَّمَا تُجۡزَوۡنَ مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Ya ku waxanda suka kafirta, kada ku kawo wani hanzari a yau; ana saka muku ne kawai da abin da kuka kasance kuna aikatawa



Sura: Suratut Tahrim

Aya : 8

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ تُوبُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ تَوۡبَةٗ نَّصُوحًا عَسَىٰ رَبُّكُمۡ أَن يُكَفِّرَ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَيُدۡخِلَكُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ يَوۡمَ لَا يُخۡزِي ٱللَّهُ ٱلنَّبِيَّ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥۖ نُورُهُمۡ يَسۡعَىٰ بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَبِأَيۡمَٰنِهِمۡ يَقُولُونَ رَبَّنَآ أَتۡمِمۡ لَنَا نُورَنَا وَٱغۡفِرۡ لَنَآۖ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku tuba zuwa ga Allah tuba na gaskiya, tabbas Ubangijinku zai kankare muku kurakuranku Ya kuma shigar da ku gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, a ranar da Allah ba zai kunyata Manzo da waxanda suka yi imani tare da shi ba; haskensu yana tafe a gabansu da damansu suna cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka sa haskenmu ya xore, Ka kuma gafarta mana; lalle Kai Mai iko ne a kan komai.”



Sura: Suratut Tahrim

Aya : 9

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ جَٰهِدِ ٱلۡكُفَّارَ وَٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱغۡلُظۡ عَلَيۡهِمۡۚ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

Ya kai wannan Annabi, ka yaqi kafirai da munafukai, ka kuma tsananta musu. Makomarsu kuma Jahannama ce; makoma kuwa ta munana



Sura: Suratut Tahrim

Aya : 10

ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱمۡرَأَتَ نُوحٖ وَٱمۡرَأَتَ لُوطٖۖ كَانَتَا تَحۡتَ عَبۡدَيۡنِ مِنۡ عِبَادِنَا صَٰلِحَيۡنِ فَخَانَتَاهُمَا فَلَمۡ يُغۡنِيَا عَنۡهُمَا مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـٔٗا وَقِيلَ ٱدۡخُلَا ٱلنَّارَ مَعَ ٱلدَّـٰخِلِينَ

Allah Ya ba da wani misali ga waxanda suka kafirta da matar Nuhu da matar Luxu; sun kasance qarqashin (igiyar auren) wasu bayi su biyu salihai daga bayinmu, sai suka ha’ince su[1], saboda haka ba su wadatar musu komai ba (daga azabar) Allah, aka kuma ce: “Ku shiga wuta tare da masu shiga.”


1- Watau suka kafirce musu, suka riqa hana mutane bin addinin Allah, suka kuma riqa goyon bayan kafirai.


Sura: Suratut Tahrim

Aya : 11

وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱمۡرَأَتَ فِرۡعَوۡنَ إِذۡ قَالَتۡ رَبِّ ٱبۡنِ لِي عِندَكَ بَيۡتٗا فِي ٱلۡجَنَّةِ وَنَجِّنِي مِن فِرۡعَوۡنَ وَعَمَلِهِۦ وَنَجِّنِي مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Allah kuma Ya ba da wani misali ga waxanda suka yi imani da matar Fir’auna lokacin da ta ce: “Ya Ubangijina, Ka gina min gida a wurinka cikin Aljanna, Ka kuma tserar da ni daga Fir’auna da aikinsa, kuma Ka tserar da ni daga azzaluman mutane.”



Sura: Suratut Tahrim

Aya : 12

وَمَرۡيَمَ ٱبۡنَتَ عِمۡرَٰنَ ٱلَّتِيٓ أَحۡصَنَتۡ فَرۡجَهَا فَنَفَخۡنَا فِيهِ مِن رُّوحِنَا وَصَدَّقَتۡ بِكَلِمَٰتِ رَبِّهَا وَكُتُبِهِۦ وَكَانَتۡ مِنَ ٱلۡقَٰنِتِينَ

Da kuma Maryamu ‘yar Imrana wadda ta kiyaye matuncinta, sai Muka masa busa daga Ruhinmu[1], ta kuma gaskata ayoyin Ubangijinta da littattafansa, ta kuma kasance daga masu biyayya ga Allah


1- Watau Allah ya umarci Mala’ika Jibrilu () ya yi busa a gare ta.