Sura: Suratul Munafiqun

Aya : 1

إِذَا جَآءَكَ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ قَالُواْ نَشۡهَدُ إِنَّكَ لَرَسُولُ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ إِنَّكَ لَرَسُولُهُۥ وَٱللَّهُ يَشۡهَدُ إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ لَكَٰذِبُونَ

Idan munafukai suka zo maka sai suka ce: “Muna shaidawa cewa lalle kai Manzon Allah ne.” Allah kuma Yana sane da cewa kai tabbas Manzonsa ne, kuma Allah Yana shaidawa cewa munafukai tabbas qarya suke yi



Sura: Suratul Munafiqun

Aya : 2

ٱتَّخَذُوٓاْ أَيۡمَٰنَهُمۡ جُنَّةٗ فَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ إِنَّهُمۡ سَآءَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Sun xauki rantse-rantsensu garkuwa, saboda haka suka kange (mutane) daga hanyar Allah. Lalle su abin da suka kasance suna aikatawa ya munana



Sura: Suratul Munafiqun

Aya : 3

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ ءَامَنُواْ ثُمَّ كَفَرُواْ فَطُبِعَ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَهُمۡ لَا يَفۡقَهُونَ

Wannan kuwa saboda cewa sun yi imani sannan suka kafirta, sai aka rufe zukatansu, saboda haka su ba sa fahimta



Sura: Suratul Munafiqun

Aya : 4

۞وَإِذَا رَأَيۡتَهُمۡ تُعۡجِبُكَ أَجۡسَامُهُمۡۖ وَإِن يَقُولُواْ تَسۡمَعۡ لِقَوۡلِهِمۡۖ كَأَنَّهُمۡ خُشُبٞ مُّسَنَّدَةٞۖ يَحۡسَبُونَ كُلَّ صَيۡحَةٍ عَلَيۡهِمۡۚ هُمُ ٱلۡعَدُوُّ فَٱحۡذَرۡهُمۡۚ قَٰتَلَهُمُ ٱللَّهُۖ أَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ

Idan ka gan su sai jikkunansu su qayatar da kai; idan kuma suka yi magana za ka saurari maganarsu; kai ka ce su wasu gumaguman itatuwa ne a jingine[1]; suna tsammanin kowace irin kururuwa saboda su ne. Su ne maqiya, saboda haka ka yi hattara da su. Allah kuma Ya la’ance su; ta ina ne ake karkatar da su?


1- Watau dai wannan cika fuskar duka fankanfayau ne, ba sa fahimtar komai daga bayanan da Annabi () yake yi.


Sura: Suratul Munafiqun

Aya : 5

وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ تَعَالَوۡاْ يَسۡتَغۡفِرۡ لَكُمۡ رَسُولُ ٱللَّهِ لَوَّوۡاْ رُءُوسَهُمۡ وَرَأَيۡتَهُمۡ يَصُدُّونَ وَهُم مُّسۡتَكۡبِرُونَ

Idan kuma aka ce da su: “Ku zo Manzon Allah ya nema muku gafara,” sai su kau da kansu, sai ka gan su suna bijirewa, alhalin suna masu girman kai



Sura: Suratul Munafiqun

Aya : 6

سَوَآءٌ عَلَيۡهِمۡ أَسۡتَغۡفَرۡتَ لَهُمۡ أَمۡ لَمۡ تَسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ لَن يَغۡفِرَ ٱللَّهُ لَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ

Duk xaya ne game da su, ka nema musu gafara, ko ba ka nema musu gafara ba, Allah ba zai gafarta musu ba har abada. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane fasiqai



Sura: Suratul Munafiqun

Aya : 7

هُمُ ٱلَّذِينَ يَقُولُونَ لَا تُنفِقُواْ عَلَىٰ مَنۡ عِندَ رَسُولِ ٱللَّهِ حَتَّىٰ يَنفَضُّواْۗ وَلِلَّهِ خَزَآئِنُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَٰكِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ لَا يَفۡقَهُونَ

Su ne waxanda suke cewa: “Kada ku ciyar da waxanda suke wurin Manzon Allah har sai sun dare[1]”. Alhali kuwa taskokin sammai da qasa na Allah ne, sai dai kuma munafukai ba sa ganewa


1- Watau su daina taimaka wa sahabbai faqirai da suke tare da Manzon Allah () har sai sun waste sun bar shi.


Sura: Suratul Munafiqun

Aya : 8

يَقُولُونَ لَئِن رَّجَعۡنَآ إِلَى ٱلۡمَدِينَةِ لَيُخۡرِجَنَّ ٱلۡأَعَزُّ مِنۡهَا ٱلۡأَذَلَّۚ وَلِلَّهِ ٱلۡعِزَّةُ وَلِرَسُولِهِۦ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ وَلَٰكِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ لَا يَعۡلَمُونَ

Suna cewa: “Tabbas idan muka koma Madina, lalle mafi daraja zai fitar da mafi wulaqanci daga cikinta[1]”. Alhali kuwa girma na Allah ne da Manzonsa da kuma muminai, sai dai kuma munafukai ba sa sanin (haka)


1- Watau shugaban munafukai na Madina Abdullahi xan Ubayyu xan Salul shi ne yake faxa wa Annabi () wannan mummunar maganar.


Sura: Suratul Munafiqun

Aya : 9

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُلۡهِكُمۡ أَمۡوَٰلُكُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُكُمۡ عَن ذِكۡرِ ٱللَّهِۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada dukiyoyinku da ‘ya’yanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah[1]. Duk wanda ya aikata haka kuwa, to waxannan su ne tavavvu


1- Watau su xauke muku hankali daga salla da sauran farillan Musulunci da zikirin Allah.


Sura: Suratul Munafiqun

Aya : 10

وَأَنفِقُواْ مِن مَّا رَزَقۡنَٰكُم مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ فَيَقُولَ رَبِّ لَوۡلَآ أَخَّرۡتَنِيٓ إِلَىٰٓ أَجَلٖ قَرِيبٖ فَأَصَّدَّقَ وَأَكُن مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Kuma ku ciyar daga abin da Muka arzuta ku tun kafin mutuwa ta zo wa xayanku sannan ya riqa cewa: “Ya Ubangijina, me ya hana Ka saurara min zuwa wani xan lokaci na kusa sai in ba da gaskiya in kuma zama cikin bayi nagari.”



Sura: Suratul Munafiqun

Aya : 11

وَلَن يُؤَخِّرَ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِذَا جَآءَ أَجَلُهَاۚ وَٱللَّهُ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ

Allah kuwa ba zai tava saurara wa wani rai ba idan ajalinsa ya zo. Allah kuwa Masanin abin da kuke aikatawa ne