Sura: Suratul Hashr

Aya : 1

سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa ya tsarkake Allah; Shi ne kuwa Mabuwayi, Mai hikima



Sura: Suratul Hashr

Aya : 2

هُوَ ٱلَّذِيٓ أَخۡرَجَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ مِن دِيَٰرِهِمۡ لِأَوَّلِ ٱلۡحَشۡرِۚ مَا ظَنَنتُمۡ أَن يَخۡرُجُواْۖ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُم مَّانِعَتُهُمۡ حُصُونُهُم مِّنَ ٱللَّهِ فَأَتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِنۡ حَيۡثُ لَمۡ يَحۡتَسِبُواْۖ وَقَذَفَ فِي قُلُوبِهِمُ ٱلرُّعۡبَۚ يُخۡرِبُونَ بُيُوتَهُم بِأَيۡدِيهِمۡ وَأَيۡدِي ٱلۡمُؤۡمِنِينَ فَٱعۡتَبِرُواْ يَـٰٓأُوْلِي ٱلۡأَبۡصَٰرِ

Shi ne wanda Ya fitar da waxanda suka kafirce daga ma’abota littafi[1] daga gidajensu a fitarwa ta farko. Ba ku yi tsammanin cewa za su fita ba, su kuma sun zaci ganuwoyinsu za su kare su daga Allah, sai Allah Ya zo musu ta inda ba su yi tsammani ba; Ya kuma jefa tsoro a cikin zukatansu. Suka riqa rushe gidajensu da hannayensu da kuma hannayen muminai, to sai ku luru da kyau ya ku ma’abota basira


1- Su ne Yahudawan Banun Nadhir waxanda Annabi () ya kore su daga Madina bayan sun yi yunqurin kashe shi.


Sura: Suratul Hashr

Aya : 3

وَلَوۡلَآ أَن كَتَبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمُ ٱلۡجَلَآءَ لَعَذَّبَهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابُ ٱلنَّارِ

Ba don Allah Ya qaddara musu ficewa ba, lalle da Ya azabtar da su a duniya, a lahira kuma suna da azabar wuta



Sura: Suratul Hashr

Aya : 4

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ شَآقُّواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥۖ وَمَن يُشَآقِّ ٱللَّهَ فَإِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Wannan kuwa saboda cewa sun sava wa Allah da Manzonsa ne, duk kuwa wanda ya sava wa Allah da Manzonsa, to lalle Allah Mai tsananin uquba ne



Sura: Suratul Hashr

Aya : 5

مَا قَطَعۡتُم مِّن لِّينَةٍ أَوۡ تَرَكۡتُمُوهَا قَآئِمَةً عَلَىٰٓ أُصُولِهَا فَبِإِذۡنِ ٱللَّهِ وَلِيُخۡزِيَ ٱلۡفَٰسِقِينَ

Duk abin da kuka sare na wata bishiyar dabino ko kuka bar ta a tsaye a kan tushiyoyinta, to da izinin Allah ne, don kuma Ya kunyata fasiqai



Sura: Suratul Hashr

Aya : 6

وَمَآ أَفَآءَ ٱللَّهُ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ مِنۡهُمۡ فَمَآ أَوۡجَفۡتُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ خَيۡلٖ وَلَا رِكَابٖ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يُسَلِّطُ رُسُلَهُۥ عَلَىٰ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Kuma duk abin da Allah Ya bai wa Manzonsa na wata dukiya tasu (don falalarsa), to ba wani hari kuka kai na dawaki ko raquma[1] ba saboda shi, sai dai kuma Allah Shi ne Yake xora manzanninsa a kan wanda Ya ga dama. Allah kuwa Mai iko ne a kan komai


1- Watau ku sami dukiya ba tare da yaqi ba.


Sura: Suratul Hashr

Aya : 7

مَّآ أَفَآءَ ٱللَّهُ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡقُرَىٰ فَلِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِ كَيۡ لَا يَكُونَ دُولَةَۢ بَيۡنَ ٱلۡأَغۡنِيَآءِ مِنكُمۡۚ وَمَآ ءَاتَىٰكُمُ ٱلرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَمَا نَهَىٰكُمۡ عَنۡهُ فَٱنتَهُواْۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Abin da Allah ya bai wa Manzonsa na wata dukiya daga mutanen alqaryu, to na Allah ne da Manzonsa da kuma danginsa na kusa[1] da marayu da miskinai da matafiyin (da guzuri ya yanke wa), don kada ya zama mai juyawa tsakanin mawadata daga cikinku. Kuma abin da Manzo ya ba ku sai ku karve shi, abin kuma da ya hana ku sai ku hanu. Ku kuma kiyaye dokokin Allah; lalle Allah Mai tsananin uquba ne


1- Watau Banu Hashim da Banul Muxxalib, waxanda aka haramta musu karvar sadaka ko zakka.


Sura: Suratul Hashr

Aya : 8

لِلۡفُقَرَآءِ ٱلۡمُهَٰجِرِينَ ٱلَّذِينَ أُخۡرِجُواْ مِن دِيَٰرِهِمۡ وَأَمۡوَٰلِهِمۡ يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٗا وَيَنصُرُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓۚ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلصَّـٰدِقُونَ

(Za a bayar da dukiyar) ga matalauta da suka yi hijira waxanda aka fitar da su daga gidajensu da dukiyoyinsu don neman falala daga Allah da yardarsa, suna kuma taimakon (addinin) Allah da Manzonsa. Waxannan su ne masu gaskiya



Sura: Suratul Hashr

Aya : 9

وَٱلَّذِينَ تَبَوَّءُو ٱلدَّارَ وَٱلۡإِيمَٰنَ مِن قَبۡلِهِمۡ يُحِبُّونَ مَنۡ هَاجَرَ إِلَيۡهِمۡ وَلَا يَجِدُونَ فِي صُدُورِهِمۡ حَاجَةٗ مِّمَّآ أُوتُواْ وَيُؤۡثِرُونَ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ وَلَوۡ كَانَ بِهِمۡ خَصَاصَةٞۚ وَمَن يُوقَ شُحَّ نَفۡسِهِۦ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

Da kuma waxanda suka tanadi gida (mutanen Madina) suka kuma (karvi) imani gabaninsu (masu hijira), suna son waxanda suka yi hijira zuwa gare su, ba sa samun wani qyashi a zukatansu game da abin da aka ba su (masu hijira), suna kuma fifita (masu hijira) a kan kawunansu, ko da kuwa suna da tsananin buqata. Duk kuwa wanda aka kiyaye shi daga son kansa, to waxannan su ne masu babban rabo



Sura: Suratul Hashr

Aya : 10

وَٱلَّذِينَ جَآءُو مِنۢ بَعۡدِهِمۡ يَقُولُونَ رَبَّنَا ٱغۡفِرۡ لَنَا وَلِإِخۡوَٰنِنَا ٱلَّذِينَ سَبَقُونَا بِٱلۡإِيمَٰنِ وَلَا تَجۡعَلۡ فِي قُلُوبِنَا غِلّٗا لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ رَبَّنَآ إِنَّكَ رَءُوفٞ رَّحِيمٌ

Duk kuma waxanda suka zo daga bayansu suna cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka gafarta mana mu da ‘yan’uwanmu waxanda suka rigaye mu yin imani, kada kuma Ka sanya wata qullata a zukatanmu game da waxanda suka yi imani, ya Ubangijinmu, lalle Kai Mai tausayawa ne, Mai jin qai.”



Sura: Suratul Hashr

Aya : 11

۞أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ نَافَقُواْ يَقُولُونَ لِإِخۡوَٰنِهِمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ لَئِنۡ أُخۡرِجۡتُمۡ لَنَخۡرُجَنَّ مَعَكُمۡ وَلَا نُطِيعُ فِيكُمۡ أَحَدًا أَبَدٗا وَإِن قُوتِلۡتُمۡ لَنَنصُرَنَّكُمۡ وَٱللَّهُ يَشۡهَدُ إِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ

Ba ka ga waxanda suka yi munafunci suna ce wa ‘yan’uwansu waxanda suka kafirta daga ma’abota littafi: “Tabbas idan aka fitar da ku, lalle za mu fita tare da ku, ba kuma za mu bi wani mutum game da ku ba har adaba, kuma idan aka yaqe ku tabbas za mu taimake ku.” Allah kuma Ya san tabbas qarya suke yi



Sura: Suratul Hashr

Aya : 12

لَئِنۡ أُخۡرِجُواْ لَا يَخۡرُجُونَ مَعَهُمۡ وَلَئِن قُوتِلُواْ لَا يَنصُرُونَهُمۡ وَلَئِن نَّصَرُوهُمۡ لَيُوَلُّنَّ ٱلۡأَدۡبَٰرَ ثُمَّ لَا يُنصَرُونَ

Tabbas idan aka fitar da su ba za su fita tare da su ba, kuma tabbas idan aka yaqe su ba za su taimake su ba, tabbas kuwa idan ma sun taimake su xin, lalle za su gudu su ba da baya, sannan kuma ba za a ba su nasara ba



Sura: Suratul Hashr

Aya : 13

لَأَنتُمۡ أَشَدُّ رَهۡبَةٗ فِي صُدُورِهِم مِّنَ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَفۡقَهُونَ

Tabbas ku suka fi tsoro a zukatansu fiye da Allah. Wannan kuwa saboda su mutane ne da ba sa fahimta



Sura: Suratul Hashr

Aya : 14

لَا يُقَٰتِلُونَكُمۡ جَمِيعًا إِلَّا فِي قُرٗى مُّحَصَّنَةٍ أَوۡ مِن وَرَآءِ جُدُرِۭۚ بَأۡسُهُم بَيۡنَهُمۡ شَدِيدٞۚ تَحۡسَبُهُمۡ جَمِيعٗا وَقُلُوبُهُمۡ شَتَّىٰۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَعۡقِلُونَ

Ba sa yaqar ku a tare sai a cikin wasu alqaryu katangaggu ko ta bayan katangu. Yaqi a tsakaninsu mai tsanani ne. Za ka tsammaci kansu a haxe yake, alhali zukatansu a rarrabe suke. Wannan kuwa saboda cewar su mutane ne da ba sa hankalta



Sura: Suratul Hashr

Aya : 15

كَمَثَلِ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ قَرِيبٗاۖ ذَاقُواْ وَبَالَ أَمۡرِهِمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Sun yi kama da waxanda suke a gabaninsu ba da daxewa ba, sun xanxani azabar al’amarinsu, suna kuma da (sakamakon) azaba mai raxaxi



Sura: Suratul Hashr

Aya : 16

كَمَثَلِ ٱلشَّيۡطَٰنِ إِذۡ قَالَ لِلۡإِنسَٰنِ ٱكۡفُرۡ فَلَمَّا كَفَرَ قَالَ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّنكَ إِنِّيٓ أَخَافُ ٱللَّهَ رَبَّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Sun yi kama da Shaixan lokacin da ya ce wa mutum: “Ka kafirta.” To yayin da ya kafirta sai ya ce: “Lalle ni ba ruwana da kai, lalle ni ina tsoron Allah Ubangijin talikai.”



Sura: Suratul Hashr

Aya : 17

فَكَانَ عَٰقِبَتَهُمَآ أَنَّهُمَا فِي ٱلنَّارِ خَٰلِدَيۡنِ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ جَزَـٰٓؤُاْ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Sai qarshen al’amarinsu ya kasance cewa su duka biyun masu dawwama ne cikin wuta. Wannan kuwa shi ne sakamakon azzalumai



Sura: Suratul Hashr

Aya : 18

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَلۡتَنظُرۡ نَفۡسٞ مَّا قَدَّمَتۡ لِغَدٖۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kuma kowane rai ya dubi abin da ya gabatar don gobe (lahira); ku kuma kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Masanin abin da kuke aikatawa ne



Sura: Suratul Hashr

Aya : 19

وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ نَسُواْ ٱللَّهَ فَأَنسَىٰهُمۡ أَنفُسَهُمۡۚ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

Kada kuma ku zama kamar waxanda suka manta da Allah, sai Ya mantar da su kawunansu. Waxannan su ne fasiqai



Sura: Suratul Hashr

Aya : 20

لَا يَسۡتَوِيٓ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۚ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ

‘Yan wuta da ‘yan Aljanna ba za su yi daidai ba. ‘Yan Aljanna su ne masu rabauta



Sura: Suratul Hashr

Aya : 21

لَوۡ أَنزَلۡنَا هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ عَلَىٰ جَبَلٖ لَّرَأَيۡتَهُۥ خَٰشِعٗا مُّتَصَدِّعٗا مِّنۡ خَشۡيَةِ ٱللَّهِۚ وَتِلۡكَ ٱلۡأَمۡثَٰلُ نَضۡرِبُهَا لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ

Da za Mu saukar da wannan Alqur’ani ga wani dutse, da lalle ka gan shi yana mai qasqantar da kai mai tsattsagewa don tsoron Allah. Waxannan misalan Muna buga wa mutane su ne don su yi tunani



Sura: Suratul Hashr

Aya : 22

هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِۖ هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلرَّحِيمُ

Shi ne Allah wanda babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi; Masanin voye da sarari; kuma Shi ne Mai rahama, Mai jin qai



Sura: Suratul Hashr

Aya : 23

هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡقُدُّوسُ ٱلسَّلَٰمُ ٱلۡمُؤۡمِنُ ٱلۡمُهَيۡمِنُ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡجَبَّارُ ٱلۡمُتَكَبِّرُۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

Shi ne Allah wanda babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi; Shi ne Sarki, Mai tsarki, Amintacce, Mai amintarwa, Mai kula da komai, Mabuwayi, Mai tsananin qarfi; Mai nuna isa. Allah Ya tsarkaka daga abin da suke tara (Shi da shi)



Sura: Suratul Hashr

Aya : 24

هُوَ ٱللَّهُ ٱلۡخَٰلِقُ ٱلۡبَارِئُ ٱلۡمُصَوِّرُۖ لَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ يُسَبِّحُ لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Shi ne Allah Mahalicci, Mai qagawa Mai surantawa[1]; Yana da sunaye mafiya kyau. Duk abin da yake cikin sammai da qasa yana tsarkake Shi; kuma Shi Mabuwayi ne, Mai hikima


1- Watau mai suranta kamannin abin da ya halitta yadda ya ga dama.