وَٱلطُّورِ
Na rantse da dutsen Xuri
وَكِتَٰبٖ مَّسۡطُورٖ
Da kuma rubutaccen littafi
فِي رَقّٖ مَّنشُورٖ
Cikin buxaxxiyar takardar fata
وَٱلۡبَيۡتِ ٱلۡمَعۡمُورِ
Da kuma Al-Baitul-Ma’amur[1]
1- Shi ne xakin da ke a sama ta bakwai, wanda a koyaushe dandazon mala’iku suke raya shi da bautar Allah.
وَٱلسَّقۡفِ ٱلۡمَرۡفُوعِ
Da kuma rufi abin xaukakawa[1]
1- Watau sama abar xaukakawa kamar rufi.
وَٱلۡبَحۡرِ ٱلۡمَسۡجُورِ
Da kuma kogi cikakke maqil
إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ لَوَٰقِعٞ
Lalle azabar Ubangijinka tabbas mai aukuwa ce
مَّا لَهُۥ مِن دَافِعٖ
Ba wani mai ingije ta
يَوۡمَ تَمُورُ ٱلسَّمَآءُ مَوۡرٗا
A ranar da sama za ta yi matsananciyar jujjuyawa
وَتَسِيرُ ٱلۡجِبَالُ سَيۡرٗا
Duwatsu kuma su riqa tafiya (suna barin wurarensu)
فَوَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
To tsananin azaba a wanan ranar ya tabbata ga masu qaryatawa
ٱلَّذِينَ هُمۡ فِي خَوۡضٖ يَلۡعَبُونَ
Waxanda suke wasanni cikin varna
يَوۡمَ يُدَعُّونَ إِلَىٰ نَارِ جَهَنَّمَ دَعًّا
A ranar da za a ingiza su zuwa ga wutar Jahannama ingizawa
هَٰذِهِ ٱلنَّارُ ٱلَّتِي كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ
(Za a ce da su): “Wannan ita ce wutar da kuka kasance kuna qaryatawa
أَفَسِحۡرٌ هَٰذَآ أَمۡ أَنتُمۡ لَا تُبۡصِرُونَ
“Yanzu sihiri ne wannan ko kuwa ku ne ba kwa gani?
ٱصۡلَوۡهَا فَٱصۡبِرُوٓاْ أَوۡ لَا تَصۡبِرُواْ سَوَآءٌ عَلَيۡكُمۡۖ إِنَّمَا تُجۡزَوۡنَ مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
“To ku shige ta, sai ku yi haquri ko kada ku yi haquri duk xaya ne; ana saka muku ne kawai da abin da kuka kasance kuna aikatawa.”
إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّـٰتٖ وَنَعِيمٖ
Lalle masu tsoron Allah suna cikin gidajen Aljanna da ni’ima
فَٰكِهِينَ بِمَآ ءَاتَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡ وَوَقَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡ عَذَابَ ٱلۡجَحِيمِ
Suna masu more abin da Ubangijisu Ya ba su, Ubangijinsu kuma Ya tserar da su daga azabar Jahima
كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Ku ci ku sha cikin jin xaxi saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa
مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ سُرُرٖ مَّصۡفُوفَةٖۖ وَزَوَّجۡنَٰهُم بِحُورٍ عِينٖ
Kuna masu kishingixa a kan gadaje waxanda aka jera su sahu-sahu; Muka kuma aura musu ‘yan matan Hurul-Ini
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱتَّبَعَتۡهُمۡ ذُرِّيَّتُهُم بِإِيمَٰنٍ أَلۡحَقۡنَا بِهِمۡ ذُرِّيَّتَهُمۡ وَمَآ أَلَتۡنَٰهُم مِّنۡ عَمَلِهِم مِّن شَيۡءٖۚ كُلُّ ٱمۡرِيِٕۭ بِمَا كَسَبَ رَهِينٞ
Waxanda kuwa suka yi imani, zuriyarsu kuma suka bi su a imani, za Mu haxa su da zuriyarsu[1], ba kuma za Mu tauye musu komai ba na aikinsu. Kowane mutum jingina ne ga abin da ya tsuwurwurta[2]
1- Watau sai Allah ya xaukaka darajar ‘ya’yansu don su haxu wuri guda a Aljanna, ko da kuwa ayyukan ‘ya’yan ba su kai na iyayen ba.
2- Watau ana tsare shi don abin da ya aikata kaxai, ba za a kama shi ne da laifin wani ba.
وَأَمۡدَدۡنَٰهُم بِفَٰكِهَةٖ وَلَحۡمٖ مِّمَّا يَشۡتَهُونَ
Muka kuma daxe su da abin marmari da nama irin wanda suke sha’awa
يَتَنَٰزَعُونَ فِيهَا كَأۡسٗا لَّا لَغۡوٞ فِيهَا وَلَا تَأۡثِيمٞ
A cikinta (Aljannar) suna musayan kofuna na giya da babu wani zancen banza game da ita, kuma babu wani zunubi
۞وَيَطُوفُ عَلَيۡهِمۡ غِلۡمَانٞ لَّهُمۡ كَأَنَّهُمۡ لُؤۡلُؤٞ مَّكۡنُونٞ
Wasu yara nasu kuma waxanda suke kamar lu’u-lu’un da yake cikin kwasfa suna kaiwa da komowa a kansu
وَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ يَتَسَآءَلُونَ
Kuma shashinsu ya fuskanci shashi suna tambayar juna
قَالُوٓاْ إِنَّا كُنَّا قَبۡلُ فِيٓ أَهۡلِنَا مُشۡفِقِينَ
Suka ce: “Lalle sanda muke cikin iyalinmu (a duniya) kafin wannan, mun kasance masu tsoron azabar Allah
فَمَنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡنَا وَوَقَىٰنَا عَذَابَ ٱلسَّمُومِ
“Sai Allah Ya yi mana baiwa ya kiyaye mu azabar wuta
إِنَّا كُنَّا مِن قَبۡلُ نَدۡعُوهُۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡبَرُّ ٱلرَّحِيمُ
“Lalle mu mun kasance a da can muna bauta masa; lalle shi Mai kyautatawa ne, Mai jin qai.”
فَذَكِّرۡ فَمَآ أَنتَ بِنِعۡمَتِ رَبِّكَ بِكَاهِنٖ وَلَا مَجۡنُونٍ
To ka yi wa’azi, don ba za ka zama boka ba ko mahaukaci saboda ni’imar Ubangijinka
أَمۡ يَقُولُونَ شَاعِرٞ نَّتَرَبَّصُ بِهِۦ رَيۡبَ ٱلۡمَنُونِ
A’a, cewa dai suka yi: “Shi mawaqi ne da muke saurara masa hanyar halaka.”