Sura: Suratul Hujurat

Aya : 1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُقَدِّمُواْ بَيۡنَ يَدَيِ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku wuce gaban Allah da Manzonsa[1], kuma ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Mai ji ne, Masani


1- Watau wajen aikata wani aiki ko faxar wata magana kafin su saurari abin da Allah da Manzonsa () za su faxa.


Sura: Suratul Hujurat

Aya : 2

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَرۡفَعُوٓاْ أَصۡوَٰتَكُمۡ فَوۡقَ صَوۡتِ ٱلنَّبِيِّ وَلَا تَجۡهَرُواْ لَهُۥ بِٱلۡقَوۡلِ كَجَهۡرِ بَعۡضِكُمۡ لِبَعۡضٍ أَن تَحۡبَطَ أَعۡمَٰلُكُمۡ وَأَنتُمۡ لَا تَشۡعُرُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku xaga muryoyinku sama da muryar Annabi, kada kuma ku xaga masa murya wajen yin magana kamar yadda shashinku yake xaga wa shashi, don kada ayyukanku su lalace alhali kuwa ku ba ku sani ba



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 3

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَغُضُّونَ أَصۡوَٰتَهُمۡ عِندَ رَسُولِ ٱللَّهِ أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱمۡتَحَنَ ٱللَّهُ قُلُوبَهُمۡ لِلتَّقۡوَىٰۚ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَأَجۡرٌ عَظِيمٌ

Lalle waxanda suke yin qasa-qasa da muryoyinsu a wurin Manzon Allah, waxannan su ne waxanda Allah Ya jarrabi zukatansu da imani. Suna da (sakamakon) gafara da lada mai girma



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 4

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُنَادُونَكَ مِن وَرَآءِ ٱلۡحُجُرَٰتِ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡقِلُونَ

Lalle waxanda suke kiran ka ta bayan xakuna[1] yawancinsu ba su da hankali


1- Watau xakunan matan Annabi (). Ana nufin mutanen qauye masu zuwa Madina wurin Annabi () don wata buqata.


Sura: Suratul Hujurat

Aya : 5

وَلَوۡ أَنَّهُمۡ صَبَرُواْ حَتَّىٰ تَخۡرُجَ إِلَيۡهِمۡ لَكَانَ خَيۡرٗا لَّهُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Da za su yi haquri har sai ka fito wurinsu da ya fiye musu alheri. Allah kuma Mai gafara ne, Mai jin qai



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 6

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِن جَآءَكُمۡ فَاسِقُۢ بِنَبَإٖ فَتَبَيَّنُوٓاْ أَن تُصِيبُواْ قَوۡمَۢا بِجَهَٰلَةٖ فَتُصۡبِحُواْ عَلَىٰ مَا فَعَلۡتُمۡ نَٰدِمِينَ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan wani fasiqi ya zo muku da wani labari, to ku yi bincike, don kada ku cuci mutane cikin rashin sani, sannan ku wayi gari kuna masu nadama game da abin da kuka aikata



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 7

وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ فِيكُمۡ رَسُولَ ٱللَّهِۚ لَوۡ يُطِيعُكُمۡ فِي كَثِيرٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡرِ لَعَنِتُّمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ حَبَّبَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡإِيمَٰنَ وَزَيَّنَهُۥ فِي قُلُوبِكُمۡ وَكَرَّهَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡكُفۡرَ وَٱلۡفُسُوقَ وَٱلۡعِصۡيَانَۚ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلرَّـٰشِدُونَ

Kuma ku sani cewa Manzon Allah yana cikinku. Da zai biye muku game da al’amura masu yawa, tabbas da kun wahala, sai dai kuma Allah Ya sa muku son imani Ya kuma qawata shi a cikin zukatanku, Ya kuma sa muku qin kafirci da fasiqanci da savo. Waxannan su ne shiryayyu



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 8

فَضۡلٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَنِعۡمَةٗۚ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

(Wannan) falala ce daga Allah da kuma ni’ima, Allah kuwa Masani ne, Mai hikima



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 9

وَإِن طَآئِفَتَانِ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱقۡتَتَلُواْ فَأَصۡلِحُواْ بَيۡنَهُمَاۖ فَإِنۢ بَغَتۡ إِحۡدَىٰهُمَا عَلَى ٱلۡأُخۡرَىٰ فَقَٰتِلُواْ ٱلَّتِي تَبۡغِي حَتَّىٰ تَفِيٓءَ إِلَىٰٓ أَمۡرِ ٱللَّهِۚ فَإِن فَآءَتۡ فَأَصۡلِحُواْ بَيۡنَهُمَا بِٱلۡعَدۡلِ وَأَقۡسِطُوٓاْۖ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُقۡسِطِينَ

Idan kuma wasu qungiyoyi biyu na muminai suka yaqi junansu sai ku yi sulhu a tsakaninsu; to idan xayarsu ta yi ta’adda a kan xayar, to sai ku yaqi wadda ta yi ta’addar har sai ta komo zuwa bin umarnin Allah. Idan ta komo sai ku yi sulhu a tsakaninsu bisa adalci, ku kuma yi adalci; lalle Allah Yana son masu adalci



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 10

إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ إِخۡوَةٞ فَأَصۡلِحُواْ بَيۡنَ أَخَوَيۡكُمۡۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ

Lalle muminai ‘yan’uwan juna ne, sai ku yi sulhu a tsakanin ‘yan’uwanku. Kuma ku kiyaye dokokin Allah don a ji qan ku



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 11

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا يَسۡخَرۡ قَوۡمٞ مِّن قَوۡمٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُونُواْ خَيۡرٗا مِّنۡهُمۡ وَلَا نِسَآءٞ مِّن نِّسَآءٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُنَّ خَيۡرٗا مِّنۡهُنَّۖ وَلَا تَلۡمِزُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ وَلَا تَنَابَزُواْ بِٱلۡأَلۡقَٰبِۖ بِئۡسَ ٱلِٱسۡمُ ٱلۡفُسُوقُ بَعۡدَ ٱلۡإِيمَٰنِۚ وَمَن لَّمۡ يَتُبۡ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada wasu mutane su yi wa wasu mutane izgili, mai yiwuwa ne su zamanto sun fi su alheri, kuma kada wasu mata (su yi wa) wasu mata (izgili), mai yiwuwa ne su zamanto sun fi su alheri; kada kuma ku riqa aibata junanku, kuma kada ku riqa jifan juna da munanan laquba (da kuke qi). Tir da sunan fasiqanci bayan imani. Wanda duk bai tuba ba, to waxannan su ne azzalumai



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 12

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱجۡتَنِبُواْ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلظَّنِّ إِنَّ بَعۡضَ ٱلظَّنِّ إِثۡمٞۖ وَلَا تَجَسَّسُواْ وَلَا يَغۡتَب بَّعۡضُكُم بَعۡضًاۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمۡ أَن يَأۡكُلَ لَحۡمَ أَخِيهِ مَيۡتٗا فَكَرِهۡتُمُوهُۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ تَوَّابٞ رَّحِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku nisanci yawancin zace-zace, lalle shashin zace-zace laifi ne; kada kuma ku riqa binciken laifukan wasu, kuma kada shashinku ya riqa gibar shashi. Yanzu xayanku zai so ya ci naman xan’uwansa matacce? To sai kuka qi shi. To ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Mai karvar tuba ne, Mai jin qai



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 13

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّا خَلَقۡنَٰكُم مِّن ذَكَرٖ وَأُنثَىٰ وَجَعَلۡنَٰكُمۡ شُعُوبٗا وَقَبَآئِلَ لِتَعَارَفُوٓاْۚ إِنَّ أَكۡرَمَكُمۡ عِندَ ٱللَّهِ أَتۡقَىٰكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٞ

Ya ku mutane, lalle Mu Muka halicce ku daga namiji da mace, Muka kuma sanya ku al’ummu da qabilu don ku san juna. Lalle mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku taqawa. Lalle Allah Masanin sarari ne, Masanin voye



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 14

۞قَالَتِ ٱلۡأَعۡرَابُ ءَامَنَّاۖ قُل لَّمۡ تُؤۡمِنُواْ وَلَٰكِن قُولُوٓاْ أَسۡلَمۡنَا وَلَمَّا يَدۡخُلِ ٱلۡإِيمَٰنُ فِي قُلُوبِكُمۡۖ وَإِن تُطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ لَا يَلِتۡكُم مِّنۡ أَعۡمَٰلِكُمۡ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

(Larabawa) qauyawa suka ce: “Mun yi imani.” Ka ce: “Ba ku yi imani ba, sai dai ku ce ‘mun musulunta’, don kuwa imani bai riga ya shiga zukatanku ba; idan kuwa kuka bi Allah da Manzonsa, to ba zai tauye muku wani abu daga (ladan) ayyukanku ba. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai rahama.”



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 15

إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ثُمَّ لَمۡ يَرۡتَابُواْ وَجَٰهَدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۚ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلصَّـٰدِقُونَ

Muminai kawai su ne waxanda suka yi imani da Allah da Manzonsa, sannan ba su yi kokwanto ba, suka kuma yi yaqi da dukiyoyinsu da rayukansu a hanyar Allah, Waxannan su ne masu gaskiya



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 16

قُلۡ أَتُعَلِّمُونَ ٱللَّهَ بِدِينِكُمۡ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ

Ka ce: “Yanzu kwa riqa sanar da Allah addininku, alhali kuwa Allah Yana sane da abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa? Allah kuwa Masanin komai ne.”



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 17

يَمُنُّونَ عَلَيۡكَ أَنۡ أَسۡلَمُواْۖ قُل لَّا تَمُنُّواْ عَلَيَّ إِسۡلَٰمَكُمۖ بَلِ ٱللَّهُ يَمُنُّ عَلَيۡكُمۡ أَنۡ هَدَىٰكُمۡ لِلۡإِيمَٰنِ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Suna yi maka gorin sun musulunta; ka ce: “Kada ku yi min gorin musuluntarku; a’a, Allah ne ma zai yi muku gori don Ya shiryar da ku zuwa ga imani, idan kun kasance masu gaskiya.”



Sura: Suratul Hujurat

Aya : 18

إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ غَيۡبَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ

Lalle Allah Yana sane da abin da yake voye a sammai da qasa, Allah kuma Mai ganin abin da kuke aikatawa ne