Sura: Suratu Muhammad

Aya : 1

ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ أَضَلَّ أَعۡمَٰلَهُمۡ

Waxanda suka kafirta suka kuma toshe hanyar Allah, to (Allah) Ya lalata ayyukansu[1]


1- Watau ba za su sami lada ba a kan ayyuka na qwarai da suka yi. Hakanan ayyukansu da suke yi na qoqarin rushe Musulunci haqansu ba zai cimma ruwa ba.


Sura: Suratu Muhammad

Aya : 2

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَءَامَنُواْ بِمَا نُزِّلَ عَلَىٰ مُحَمَّدٖ وَهُوَ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّهِمۡ كَفَّرَ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَأَصۡلَحَ بَالَهُمۡ

Waxanda kuwa suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, kuma suka gaskata abin da aka saukar wa Muhammadu alhali kuwa shi ne gaskiya daga Ubangijinsu, sai (Allah) Ya kankare musu munanan ayyukansu, Ya kuma gyara musu halayensu



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 3

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱتَّبَعُواْ ٱلۡبَٰطِلَ وَأَنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّبَعُواْ ٱلۡحَقَّ مِن رَّبِّهِمۡۚ كَذَٰلِكَ يَضۡرِبُ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ أَمۡثَٰلَهُمۡ

Wannan (sakamako) kuwa saboda waxanda suka kafirta sun bi varna, waxanda kuwa suka yi imani sun bi shiriya daga Ubangijinsu. Kamar haka ne Allah Yake buga wa mutane misalansu



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 4

فَإِذَا لَقِيتُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَضَرۡبَ ٱلرِّقَابِ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَثۡخَنتُمُوهُمۡ فَشُدُّواْ ٱلۡوَثَاقَ فَإِمَّا مَنَّۢا بَعۡدُ وَإِمَّا فِدَآءً حَتَّىٰ تَضَعَ ٱلۡحَرۡبُ أَوۡزَارَهَاۚ ذَٰلِكَۖ وَلَوۡ يَشَآءُ ٱللَّهُ لَٱنتَصَرَ مِنۡهُمۡ وَلَٰكِن لِّيَبۡلُوَاْ بَعۡضَكُم بِبَعۡضٖۗ وَٱلَّذِينَ قُتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَلَن يُضِلَّ أَعۡمَٰلَهُمۡ

To idan kuka haxu da waxanda suka kafirta sai ku sare wuyoyinsu har lokacin da kuka yi musu jina-jina, sai ku tsananta xauri[1]; to bayan nan ko dai yafewa su tafi bayan (kun ribace su), ko kuma karvar fansa har sai yaqi ya lafa. Wannan abu haka yake, da kuma Allah Ya ga dama da Ya yi nasara a kansu (ko da ba yaqi), sai dai kuma (Ya yi haka ne) don Ya jarrabi shashinku da shashi. Waxanda kuwa aka kashe su a hanyar Allah, to ba zai tava lalata ayyukansa ba


1- Watau Musulmi su kama su a matsayin ribatattun yaqi.


Sura: Suratu Muhammad

Aya : 5

سَيَهۡدِيهِمۡ وَيُصۡلِحُ بَالَهُمۡ

Zai shirye su Ya kuma kyautata halinsu



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 6

وَيُدۡخِلُهُمُ ٱلۡجَنَّةَ عَرَّفَهَا لَهُمۡ

Ya kuma shigar da su Aljannar da Ya sanar da ita gare su



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 7

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِن تَنصُرُواْ ٱللَّهَ يَنصُرۡكُمۡ وَيُثَبِّتۡ أَقۡدَامَكُمۡ

Ya ku waxanda suka yi imani idan kuka taimaki Allah, to zai taimake ku, Ya kuma tabbatar da dugaduganku



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 8

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَتَعۡسٗا لَّهُمۡ وَأَضَلَّ أَعۡمَٰلَهُمۡ

Waxanda kuwa suka kafirce to kaiconsu, (Allah) kuma Ya lalata ayyukansu[1]


1- Watau ba za su sami ladan wani aiki nasu na qwarai ba, kuma ayyukansu na qoqarin rushe Musulunci ba za su yi nasara ba.


Sura: Suratu Muhammad

Aya : 9

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَرِهُواْ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأَحۡبَطَ أَعۡمَٰلَهُمۡ

Wannan kuwa saboda cewa sun qi abin da Allah Ya saukar, sai Ya lalata ayyukansu



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 10

۞أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ دَمَّرَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡۖ وَلِلۡكَٰفِرِينَ أَمۡثَٰلُهَا

Yanzu ba za su yi tafiya a bayan qasa ba sai su duba yaya qarshen waxanda suka gabace su ya kasance? Allah Ya hallaka su; kafirai kuma suna da (sakamako) kwatankwacinsa



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 11

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ مَوۡلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَأَنَّ ٱلۡكَٰفِرِينَ لَا مَوۡلَىٰ لَهُمۡ

Wannan kuwa saboda lalle Allah ne Majivincin al’amuran waxanda suka yi imani, lalle kuma su kafirai ba su da wani majivinci



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 12

إِنَّ ٱللَّهَ يُدۡخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يَتَمَتَّعُونَ وَيَأۡكُلُونَ كَمَا تَأۡكُلُ ٱلۡأَنۡعَٰمُ وَٱلنَّارُ مَثۡوٗى لَّهُمۡ

Lalle Allah Yana shigar da waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari gidajen Aljanna (waxanda) qoramu suke gudana ta qarqashinsu; waxanda kuwa suka kafirta suna jin daxi (a duniya), suna kuma ta ciye-ciye kamar yadda dabbobi suke yi, wuta ce kuma makomarsu



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 13

وَكَأَيِّن مِّن قَرۡيَةٍ هِيَ أَشَدُّ قُوَّةٗ مِّن قَرۡيَتِكَ ٱلَّتِيٓ أَخۡرَجَتۡكَ أَهۡلَكۡنَٰهُمۡ فَلَا نَاصِرَ لَهُمۡ

Alqaryu nawa ne waxanda suka fi alqaryarka wadda ta fitar da kai qarfi, Mun hallakar da su, don haka ba su da wani mai taimakon su



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 14

أَفَمَن كَانَ عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّهِۦ كَمَن زُيِّنَ لَهُۥ سُوٓءُ عَمَلِهِۦ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَهۡوَآءَهُم

Yanzu waxanda suka kasance a kan hujja daga Ubangijinsu, sa yi daidai da waxanda aka qawata musu mummuna aikinsu, suka kuma bi son zuciyarsu?



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 15

مَّثَلُ ٱلۡجَنَّةِ ٱلَّتِي وُعِدَ ٱلۡمُتَّقُونَۖ فِيهَآ أَنۡهَٰرٞ مِّن مَّآءٍ غَيۡرِ ءَاسِنٖ وَأَنۡهَٰرٞ مِّن لَّبَنٖ لَّمۡ يَتَغَيَّرۡ طَعۡمُهُۥ وَأَنۡهَٰرٞ مِّنۡ خَمۡرٖ لَّذَّةٖ لِّلشَّـٰرِبِينَ وَأَنۡهَٰرٞ مِّنۡ عَسَلٖ مُّصَفّٗىۖ وَلَهُمۡ فِيهَا مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ وَمَغۡفِرَةٞ مِّن رَّبِّهِمۡۖ كَمَنۡ هُوَ خَٰلِدٞ فِي ٱلنَّارِ وَسُقُواْ مَآءً حَمِيمٗا فَقَطَّعَ أَمۡعَآءَهُمۡ

Kwatankwacin Aljannar da aka yi wa masu taqawa alqawari da ita shi ne, a cikinta akwai qoramu na ruwa ba gurvatacce ba, da kuma qoramu na nono da xanxanonsa bai canja ba, da qoramu na giya masu daxi ga mashaya, da qoramu na tatacciyar zuma, kuma suna da kowane irin nau’i na ‘ya’yan itace da kuma gafara daga Ubangijinsu. Yanzu (masu waxannan sa yi) daidai da waxanda za su dawwama a cikin wuta a kuma shayar da su ruwa tafasasshe, sai ya yayyanke kayan cikinsu?



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 16

وَمِنۡهُم مَّن يَسۡتَمِعُ إِلَيۡكَ حَتَّىٰٓ إِذَا خَرَجُواْ مِنۡ عِندِكَ قَالُواْ لِلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ مَاذَا قَالَ ءَانِفًاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ طَبَعَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَهۡوَآءَهُمۡ

Daga cikinsu kuma akwai waxanda suke sauraron ka, har lokacin da suka fita daga wurinka sai su ce da waxanda aka bai wa ilimi: “Shin me ma ya ce xazu?” Waxannan su ne waxanda Allah Ya toshe zukatansu suka kuma bi son ransu



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 17

وَٱلَّذِينَ ٱهۡتَدَوۡاْ زَادَهُمۡ هُدٗى وَءَاتَىٰهُمۡ تَقۡوَىٰهُمۡ

Waxanda kuwa suka shiryu Ya qara musu shiriya, Ya kuma kimsa musu taqawarsu



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 18

فَهَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّا ٱلسَّاعَةَ أَن تَأۡتِيَهُم بَغۡتَةٗۖ فَقَدۡ جَآءَ أَشۡرَاطُهَاۚ فَأَنَّىٰ لَهُمۡ إِذَا جَآءَتۡهُمۡ ذِكۡرَىٰهُمۡ

Ai ba wani abu da suke sauraro sai alqiyama ta zo musu farat xaya; to haqiqa alamominta sun zo[1]. To qaqa tunawar tasu za ta zame musu idan abin (alqiyamar) ta zo musu ne?


1- Daga cikinsu akwai aiko da Manzon Allah () da tsagewar wata gida biyu da ya faru a Makka.


Sura: Suratu Muhammad

Aya : 19

فَٱعۡلَمۡ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لِذَنۢبِكَ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مُتَقَلَّبَكُمۡ وَمَثۡوَىٰكُمۡ

To ka sani cewa, babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma ka nemi gafarar zunubanka da na muminai maza da mata, Allah kuma Yana sane da kai-kawonku (na rana) da kuma wurin kwanciyarku (da daddare)



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 20

وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَوۡلَا نُزِّلَتۡ سُورَةٞۖ فَإِذَآ أُنزِلَتۡ سُورَةٞ مُّحۡكَمَةٞ وَذُكِرَ فِيهَا ٱلۡقِتَالُ رَأَيۡتَ ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ يَنظُرُونَ إِلَيۡكَ نَظَرَ ٱلۡمَغۡشِيِّ عَلَيۡهِ مِنَ ٱلۡمَوۡتِۖ فَأَوۡلَىٰ لَهُمۡ

Waxanda kuma suka yi imani suna cewa: “Me ya hana a saukar da wata sura (wadda za ta ba mu damar yin yaqi)?” Sannan lokacin da aka saukar da wata sura mai xauke da hukunci aka kuma ambaci yaqi a cikinta, sai ka ga waxanda suke da raunin imani a zukatansu (watau munafukai), suna kallon ka kamar kallon wanda yake cikin magagin mutuwa. To abin da ya fiye musu



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 21

طَاعَةٞ وَقَوۡلٞ مَّعۡرُوفٞۚ فَإِذَا عَزَمَ ٱلۡأَمۡرُ فَلَوۡ صَدَقُواْ ٱللَّهَ لَكَانَ خَيۡرٗا لَّهُمۡ

(Shi ne) yin biyayya da magana mai kyau. To idan al’amarin yaqi ya tabbata, to da za su nuna wa Allah gaskiyarsu, da ya fi musu alhairi



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 22

فَهَلۡ عَسَيۡتُمۡ إِن تَوَلَّيۡتُمۡ أَن تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَتُقَطِّعُوٓاْ أَرۡحَامَكُمۡ

Shin ba kwa ganin idan kuka ba da baya (daga bin Allah) sai ku yi varna a bayan qasa, ku kuma yanke zumuntarku?



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 23

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَعَنَهُمُ ٱللَّهُ فَأَصَمَّهُمۡ وَأَعۡمَىٰٓ أَبۡصَٰرَهُمۡ

Waxannan su ne waxanda Allah Ya la’ance su, sai Ya kurumtar da su, Ya kuma makantar da ganinsu



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 24

أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ ٱلۡقُرۡءَانَ أَمۡ عَلَىٰ قُلُوبٍ أَقۡفَالُهَآ

Yanzu ba za su yi tunani na basira ba (game da) Alqur’ani ba, ko kuwa akwai wani rufi ne a kan zukatansu?



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 25

إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱرۡتَدُّواْ عَلَىٰٓ أَدۡبَٰرِهِم مِّنۢ بَعۡدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ ٱلۡهُدَى ٱلشَّيۡطَٰنُ سَوَّلَ لَهُمۡ وَأَمۡلَىٰ لَهُمۡ

Lalle waxanda suka yi ridda suka koma baya, bayan kuwa shiriya ta bayyana a gare su, to Shaixan ne ya qawata musu ya kuma yi musu shifta



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 26

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَالُواْ لِلَّذِينَ كَرِهُواْ مَا نَزَّلَ ٱللَّهُ سَنُطِيعُكُمۡ فِي بَعۡضِ ٱلۡأَمۡرِۖ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ إِسۡرَارَهُمۡ

Wannan kuwa saboda lalle su, sun ce wa waxanda suka qi bin abin da Allah Ya saukar: “Za mu bi ku a wasu al’amura.” Allah kuwa Yana sane da asiransu



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 27

فَكَيۡفَ إِذَا تَوَفَّتۡهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَضۡرِبُونَ وُجُوهَهُمۡ وَأَدۡبَٰرَهُمۡ

To yaya za su zama lokacin da mala’iku za su karvi rayukansu suna dukan fuskokinsu da bayansu?



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 28

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ ٱتَّبَعُواْ مَآ أَسۡخَطَ ٱللَّهَ وَكَرِهُواْ رِضۡوَٰنَهُۥ فَأَحۡبَطَ أَعۡمَٰلَهُمۡ

Wannan kuwa saboda lalle su, sun bi abin da yake fusata Allah suka kuma qi bin yardarsa, sai ya rusa ayyukansa



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 29

أَمۡ حَسِبَ ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ أَن لَّن يُخۡرِجَ ٱللَّهُ أَضۡغَٰنَهُمۡ

Ko kuwa waxanda suke da cuta a cikin zukatansu suna tsammanin cewa Allah ba zai fito da qulle-qullen zukatansu ba ne?



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 30

وَلَوۡ نَشَآءُ لَأَرَيۡنَٰكَهُمۡ فَلَعَرَفۡتَهُم بِسِيمَٰهُمۡۚ وَلَتَعۡرِفَنَّهُمۡ فِي لَحۡنِ ٱلۡقَوۡلِۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ أَعۡمَٰلَكُمۡ

Kuma da Mun ga dama da tabbas Mun nuna maka su (watau munafukai), to tabbas da ka gane su da alamominsu. Kuma tabbas za ka iya gane su ta hanyar salon maganarsu. Allah kuma Yana sane da ayyukanku