حمٓ
HA MIM[1]
1- Duba Suratul Baqara aya ta 1, hashiya ta 8.
وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ
Na rantse da Littafi mai bayyanawa (shi ne Alqur’ani)
إِنَّآ أَنزَلۡنَٰهُ فِي لَيۡلَةٖ مُّبَٰرَكَةٍۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ
Lalle Mu Muka saukar da shi a cikin dare mai albarka[1]. Lalle Mu Mun kasance Masu gargaxi
1- Shi ne daren Lailatul Qadari. Duba Suratul Qadri.
فِيهَا يُفۡرَقُ كُلُّ أَمۡرٍ حَكِيمٍ
A cikinsa ne (daren) ake fasalta kowane tabbataccen al’amari (na wannan shekara)[1]
1- Watau al’amarin da ya shafi rabon arziqi da tsawon rai da sauran abubuwa da Allah ya qaddara za su faru a wannan shekarar.
أَمۡرٗا مِّنۡ عِندِنَآۚ إِنَّا كُنَّا مُرۡسِلِينَ
Al’amari ne (da Muke fasaltawa) daga wurinmu. Lalle Mun kasance Mu ne Masu aikowa (da manzanni)
رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Don rahama daga Ubangijinka. Lalle shi Mai ji ne, Masani
رَبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ
Ubangijin sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu; idan kun kasance masu sakankancewa
لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ رَبُّكُمۡ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi, Shi ne Yake rayarwa Yake kuma kashewa; (Shi ne) Ubangijinku kuma Ubangijin iyayenku na farko
بَلۡ هُمۡ فِي شَكّٖ يَلۡعَبُونَ
A’a, su dai suna cikin shakka ne, suna wasanni
فَٱرۡتَقِبۡ يَوۡمَ تَأۡتِي ٱلسَّمَآءُ بِدُخَانٖ مُّبِينٖ
Sai ka saurari ranar da sama za ta zo da hayaqi bayyananne[1]
1- Shi ne hayaqi da idanuwansu za su riqa nuna musu, shi saboda tsananin yunwa.
يَغۡشَى ٱلنَّاسَۖ هَٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٞ
Zai lulluve (idanuwan) mutane; wannan azaba ce mai raxaxi
رَّبَّنَا ٱكۡشِفۡ عَنَّا ٱلۡعَذَابَ إِنَّا مُؤۡمِنُونَ
(Za su ce): “Ya Ubangijinmu, Ka yaye mana wannan azaba, lalle mu masu yin imani ne.”
أَنَّىٰ لَهُمُ ٱلذِّكۡرَىٰ وَقَدۡ جَآءَهُمۡ رَسُولٞ مُّبِينٞ
Ta ina wa’azi zai amfane su, alhali kuwa haqiqa Manzo mai bayani ya zo musu?
ثُمَّ تَوَلَّوۡاْ عَنۡهُ وَقَالُواْ مُعَلَّمٞ مَّجۡنُونٌ
Sannan suka juya masa baya suka ce: “Ai wani ne ya koya masa, (kuma shi) tavavve ne
إِنَّا كَاشِفُواْ ٱلۡعَذَابِ قَلِيلًاۚ إِنَّكُمۡ عَآئِدُونَ
Lalle Mu Masu yaye muku azabar ne xan lokaci kaxan. Lalle (kuma) ku masu komawa ne
يَوۡمَ نَبۡطِشُ ٱلۡبَطۡشَةَ ٱلۡكُبۡرَىٰٓ إِنَّا مُنتَقِمُونَ
(Ka tuna) ranar da za Mu damqe su babbar damqa[1], lalle Mu Masu sakawa ne
1- Ita ce ranar yaqin Badar lokacin da Allah ya damqi manyan kafiran Makka aka karkashe su.
۞وَلَقَدۡ فَتَنَّا قَبۡلَهُمۡ قَوۡمَ فِرۡعَوۡنَ وَجَآءَهُمۡ رَسُولٞ كَرِيمٌ
Haqiqa kuma Mun jarrabi mutanen Fir’auna tun kafin su, kuma Manzo mai karamci ya zo musu
أَنۡ أَدُّوٓاْ إِلَيَّ عِبَادَ ٱللَّهِۖ إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ
(Da cewa): “Ku ba ni bayin Allah (watau Banu Isra’ila); lalle ni Manzo ne amintacce a gare ku
وَأَن لَّا تَعۡلُواْ عَلَى ٱللَّهِۖ إِنِّيٓ ءَاتِيكُم بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ
“Kuma kada ku yi wa Allah girman kai; lalle ni zan kawo muku hujjoji mabayyana
وَإِنِّي عُذۡتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمۡ أَن تَرۡجُمُونِ
“Kuma lalle ni ina neman tsari na Ubangijina kuma Ubangijinku, don kada ku jefe ni
وَإِن لَّمۡ تُؤۡمِنُواْ لِي فَٱعۡتَزِلُونِ
“Idan kuma ba ku yi imani da ni ba sai ku qyale ni.”
فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ قَوۡمٞ مُّجۡرِمُونَ
Sai ya roqi Ubangijinsa cewa: “Lalle waxannan mutane ne masu manyan laifuka.”
فَأَسۡرِ بِعِبَادِي لَيۡلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ
Sai (aka ce masa): “Ka tafi da bayina da daddare, lalle ku za a biyo bayanku
وَٱتۡرُكِ ٱلۡبَحۡرَ رَهۡوًاۖ إِنَّهُمۡ جُندٞ مُّغۡرَقُونَ
“Kuma ka bar kogi a tsaye cak (bayan tsallakewa); lalle su runduna ne da za a nutsar.”
كَمۡ تَرَكُواْ مِن جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٖ
Sun bar gonaki da kuma idanuwan ruwa masu yawa
وَزُرُوعٖ وَمَقَامٖ كَرِيمٖ
Da kuma shuke-shuke da wurin zama mai daraja
وَنَعۡمَةٖ كَانُواْ فِيهَا فَٰكِهِينَ
Da kuma kayan jin daxi da suka kasance masu ni’imtuwa da su
كَذَٰلِكَۖ وَأَوۡرَثۡنَٰهَا قَوۡمًا ءَاخَرِينَ
Kamar haka ne; sai Muka kuma gadar da su ga wasu mutane daban (su ne Banu Isra’ila)
فَمَا بَكَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلسَّمَآءُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَا كَانُواْ مُنظَرِينَ
Sannan (halittun) sama da na qasa ba su yi alhininsu ba, ba su kuma kasance ababen saurara wa ba
وَلَقَدۡ نَجَّيۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ مِنَ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡمُهِينِ
Haqiqa kuma Mun tserar da Banu Isra’ila daga azabar wulaqanci