Sura: Suratu Luqman

Aya : 1

الٓمٓ

ALIF LAM MIM[1]


1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8..


Sura: Suratu Luqman

Aya : 2

تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡحَكِيمِ

Waxannan ayoyin littafi ne mai hikima



Sura: Suratu Luqman

Aya : 3

هُدٗى وَرَحۡمَةٗ لِّلۡمُحۡسِنِينَ

Shiriya ne da rahama ga masu kyautatawa



Sura: Suratu Luqman

Aya : 4

ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ يُوقِنُونَ

Waxanda suke tsai da salla suke kuma ba da zakka alhali su kuma suna masu sakankancewa da ranar lahira



Sura: Suratu Luqman

Aya : 5

أُوْلَـٰٓئِكَ عَلَىٰ هُدٗى مِّن رَّبِّهِمۡۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

Waxannan suna kan shiriya daga Ubangijinsu; waxannan su ne masu rabauta



Sura: Suratu Luqman

Aya : 6

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَشۡتَرِي لَهۡوَ ٱلۡحَدِيثِ لِيُضِلَّ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَيَتَّخِذَهَا هُزُوًاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ

Daga mutane kuma akwai wanda yake sayen zantuka na sharholiya[1] don ya vatar (da mutane) daga hanyar Allah ba tare da wani ilimi ba, yana kuma riqon ta abar yi wa izgili. (Irin) waxannan azaba mai wulaqantarwa ta tabbata gare su


1- Watau kamar waqoqin banza da kaxa-kaxe da labaru marasa manufa, don ya shagaltar da mutane daga sauraren Alqur’ani, ya vatar da su daga addinin Allah.


Sura: Suratu Luqman

Aya : 7

وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ءَايَٰتُنَا وَلَّىٰ مُسۡتَكۡبِرٗا كَأَن لَّمۡ يَسۡمَعۡهَا كَأَنَّ فِيٓ أُذُنَيۡهِ وَقۡرٗاۖ فَبَشِّرۡهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ

Idan kuma ana karanta masa ayoyinmu sai ya juya yana mai girman kai kamar bai ji su ba, kamar a ce akwai wani nauyi a cikin kunnuwansa; to ka yi masa albishir da azaba mai raxaxi



Sura: Suratu Luqman

Aya : 8

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَهُمۡ جَنَّـٰتُ ٱلنَّعِيمِ

Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari suna da (sakamakon) gidajen Aljanna na ni’ima



Sura: Suratu Luqman

Aya : 9

خَٰلِدِينَ فِيهَاۖ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٗاۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Suna madawwama a cikinsu; alqawarin Allah kuwa gaskiya ne. Kuma Shi Mabuwayi ne, Mai hikima



Sura: Suratu Luqman

Aya : 10

خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ بِغَيۡرِ عَمَدٖ تَرَوۡنَهَاۖ وَأَلۡقَىٰ فِي ٱلۡأَرۡضِ رَوَٰسِيَ أَن تَمِيدَ بِكُمۡ وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَآبَّةٖۚ وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوۡجٖ كَرِيمٍ

Ya halicci sammai ba tare da wani ginshiqi da kuke ganin sa ba, Ya kuma kafa manya-manyan duwatsu a cikin qasa don kada ta riqa tangal-tangal da ku, Ya kuma yaxa kowace irin dabba a cikinta. Kuma Mun saukar da ruwa daga sama sai Muka tsirar da kowane irin dangin tsiro mai qayatarwa



Sura: Suratu Luqman

Aya : 11

هَٰذَا خَلۡقُ ٱللَّهِ فَأَرُونِي مَاذَا خَلَقَ ٱلَّذِينَ مِن دُونِهِۦۚ بَلِ ٱلظَّـٰلِمُونَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ

Wannan (ita ce) halittar Allah, sai ku nuna min abin da waxanda ba Shi ba suka halitta. A’a, su dai azzalumai suna cikin vata ne mabayyani



Sura: Suratu Luqman

Aya : 12

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا لُقۡمَٰنَ ٱلۡحِكۡمَةَ أَنِ ٱشۡكُرۡ لِلَّهِۚ وَمَن يَشۡكُرۡ فَإِنَّمَا يَشۡكُرُ لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ حَمِيدٞ

Haqiqa kuma Mun bai wa Luqumanu[1] hikima cewa: “Ka yi godiya ga Allah. Kuma duk wanda yake godewa to yana godewa ne don kansa, wanda kuwa ya kafirta to lalle Allah Mawadaci ne, Sha-yabo.”


1- Wani salihin bawa ne da Allah ya hore masa hikima da ilimi. Wasu masana tarihi sun ce yarayu ne a zamanin Annabi Dawud ().


Sura: Suratu Luqman

Aya : 13

وَإِذۡ قَالَ لُقۡمَٰنُ لِٱبۡنِهِۦ وَهُوَ يَعِظُهُۥ يَٰبُنَيَّ لَا تُشۡرِكۡ بِٱللَّهِۖ إِنَّ ٱلشِّرۡكَ لَظُلۡمٌ عَظِيمٞ

Kuma (ka tuna) lokacin da Luqumanu ya ce da xansa a yayin da yake yi masa wa’azi: “Ya kai xanxana, kada ka yi shirka da Allah; lalle ita shirka zalunci ne mai girma



Sura: Suratu Luqman

Aya : 14

وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ حَمَلَتۡهُ أُمُّهُۥ وَهۡنًا عَلَىٰ وَهۡنٖ وَفِصَٰلُهُۥ فِي عَامَيۡنِ أَنِ ٱشۡكُرۡ لِي وَلِوَٰلِدَيۡكَ إِلَيَّ ٱلۡمَصِيرُ

Kuma Mun yi wa mutum wasiyya game da iyayensa, mahaifiyarsa ta xauke shi a cikinta rauni a kan rauni, yaye shi kuwa a cikin shekara biyu ne, saboda haka ka gode min da kuma iyayenka, makoma gare Ni take



Sura: Suratu Luqman

Aya : 15

وَإِن جَٰهَدَاكَ عَلَىٰٓ أَن تُشۡرِكَ بِي مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٞ فَلَا تُطِعۡهُمَاۖ وَصَاحِبۡهُمَا فِي ٱلدُّنۡيَا مَعۡرُوفٗاۖ وَٱتَّبِعۡ سَبِيلَ مَنۡ أَنَابَ إِلَيَّۚ ثُمَّ إِلَيَّ مَرۡجِعُكُمۡ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Idan kuma suka matsa maka kan ka yi tarayya da Ni game da abin da ba ka da wani sani a kansa, to kada ka bi su; kuma ka yi zaman duniya da su ta kyakkyawar hanya; ka kuma bi hanyar wanda ya mayar da al’amarinsa gare Ni. Sannan kuma zuwa gare Ni ne kawai makomarku, sai in ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa



Sura: Suratu Luqman

Aya : 16

يَٰبُنَيَّ إِنَّهَآ إِن تَكُ مِثۡقَالَ حَبَّةٖ مِّنۡ خَرۡدَلٖ فَتَكُن فِي صَخۡرَةٍ أَوۡ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ أَوۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَأۡتِ بِهَا ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَطِيفٌ خَبِيرٞ

(Luqumanu ya ci gaba da cewa): “Ya kai xanxana, lalle ita (kyakkyawa ko mummuna) in ta kasance daidai da qwayar komayya, sannan kuma ta zamanto cikin qaton dutse ko kuma cikin sammai ko cikin qasa, to Allah zai zo da ita. Lalle Allah Mai tausasawa ne, Masanin (komai)



Sura: Suratu Luqman

Aya : 17

يَٰبُنَيَّ أَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ وَأۡمُرۡ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَٱنۡهَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَآ أَصَابَكَۖ إِنَّ ذَٰلِكَ مِنۡ عَزۡمِ ٱلۡأُمُورِ

“Ya kai xanxana, ka tsayar da salla kuma ka yi umarni da aikata alheri, ka kuma hana aikata mummunan aiki, kuma ka yi haquri bisa duk abin da ya same ka; lalle wannan yana daga manyan al’amura



Sura: Suratu Luqman

Aya : 18

وَلَا تُصَعِّرۡ خَدَّكَ لِلنَّاسِ وَلَا تَمۡشِ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَرَحًاۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ كُلَّ مُخۡتَالٖ فَخُورٖ

“Kada kuma ka riqa xauke wa mutane fuskarka[1], kuma kada ka yi tafiya a ban qasa kana mai taqama. Lalle Allah ba Ya son duk wani mai taqama, mai fariya


1- Watau yana umartar sa da ya zama mai sakin fuska da haba-haba da jama’a.


Sura: Suratu Luqman

Aya : 19

وَٱقۡصِدۡ فِي مَشۡيِكَ وَٱغۡضُضۡ مِن صَوۡتِكَۚ إِنَّ أَنكَرَ ٱلۡأَصۡوَٰتِ لَصَوۡتُ ٱلۡحَمِيرِ

“Kuma ka tsakaita tafiyarka, kuma ka yi qasa-qasa da muryarka. Lalle mafi munin muryoyi ita ce muryar jakai.”



Sura: Suratu Luqman

Aya : 20

أَلَمۡ تَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ سَخَّرَ لَكُم مَّا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَأَسۡبَغَ عَلَيۡكُمۡ نِعَمَهُۥ ظَٰهِرَةٗ وَبَاطِنَةٗۗ وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَٰدِلُ فِي ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَلَا هُدٗى وَلَا كِتَٰبٖ مُّنِيرٖ

Yanzu ba kwa gani cewa Allah Ya hore muku abin da yake cikin sammai da kuma abin da yake cikin qasa, Ya kuma cika muku ni’imominsa na sarari da na voye? Daga mutane kuma akwai waxanda suke jayayya game da Allah ba tare da wani ilimi ko wata shiriya ba, ba kuma tare da wani littafi mai haskakawa ba



Sura: Suratu Luqman

Aya : 21

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱتَّبِعُواْ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُواْ بَلۡ نَتَّبِعُ مَا وَجَدۡنَا عَلَيۡهِ ءَابَآءَنَآۚ أَوَلَوۡ كَانَ ٱلشَّيۡطَٰنُ يَدۡعُوهُمۡ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ

Idan kuma aka ce da su: “Ku bi abin da Allah Ya saukar”, sai su ce: “A’a, mu muna bin abin da muka sami iyayenmu ne a kansa.” Yanzu (sa yi haka) ko da Shaixan ya zamanto yana kiran su zuwa ga azaba ta (wuta) mai ruruwa?



Sura: Suratu Luqman

Aya : 22

۞وَمَن يُسۡلِمۡ وَجۡهَهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِ وَهُوَ مُحۡسِنٞ فَقَدِ ٱسۡتَمۡسَكَ بِٱلۡعُرۡوَةِ ٱلۡوُثۡقَىٰۗ وَإِلَى ٱللَّهِ عَٰقِبَةُ ٱلۡأُمُورِ

Wanda kuma ya miqa kansa ga Allah, yana kuma mai kyautatawa[1], to haqiqa ya yi riqo da igiya qwaqqwara. Kuma qarshen al’amura zuwa ga Allah ne


1- Watau ya kaxaita Allah da bauta, ya kuma kyautata aikinsa.


Sura: Suratu Luqman

Aya : 23

وَمَن كَفَرَ فَلَا يَحۡزُنكَ كُفۡرُهُۥٓۚ إِلَيۡنَا مَرۡجِعُهُمۡ فَنُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

Duk kuwa wanda ya kafirta, to kada kafircinsa ya vata maka rai. Zuwa gare Mu ne kawai makomarsu take, sai Mu ba su labarin abin da suka aikata. Lalle Allah Masanin abin da yake cikin qiraza ne



Sura: Suratu Luqman

Aya : 24

نُمَتِّعُهُمۡ قَلِيلٗا ثُمَّ نَضۡطَرُّهُمۡ إِلَىٰ عَذَابٍ غَلِيظٖ

Za Mu jiyar da su daxi xan kaxan sannan Mu tilasta su zuwa ga azaba mai kauri



Sura: Suratu Luqman

Aya : 25

وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُۚ قُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Tabbas kuma in ka tambaye su: “Wane ne ya halicci sammai da qasa?” Tabbas za su ce: “Allah ne.” To ka ce: “Alhamdu lillahi.” A’a, yawancinsu dai ba sa sanin (haka)



Sura: Suratu Luqman

Aya : 26

لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡغَنِيُّ ٱلۡحَمِيدُ

Abin da yake cikin sammai da qasa na Allah ne. Lalle Allah Shi ne Mawadaci, Sha-yabo



Sura: Suratu Luqman

Aya : 27

وَلَوۡ أَنَّمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ مِن شَجَرَةٍ أَقۡلَٰمٞ وَٱلۡبَحۡرُ يَمُدُّهُۥ مِنۢ بَعۡدِهِۦ سَبۡعَةُ أَبۡحُرٖ مَّا نَفِدَتۡ كَلِمَٰتُ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

Idan kuwa da a ce, duk bishiyar da take bayan qasa alqaluma ne, kogi kuma (ya zama tawadarsu), bayansa kuma akwai wasu kogunan guda bakwai qari a kansa to kalmomin Allah ba za su qare ba. Lalle Allah Mabuwayi ne, Mai hikima



Sura: Suratu Luqman

Aya : 28

مَّا خَلۡقُكُمۡ وَلَا بَعۡثُكُمۡ إِلَّا كَنَفۡسٖ وَٰحِدَةٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٌ

Halittarku da tayar da ku bai wuce tamkar na rai xaya ba. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani



Sura: Suratu Luqman

Aya : 29

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ يَجۡرِيٓ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى وَأَنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

Yanzu ba ka gani cewa Allah Yana shigar da dare cikin rana, Yana kuma shigar da rana cikin dare, Ya kuma hore (muku) rana da wata, kowannensu yana tafiya zuwa ga lokaci iyakantacce, kuma lalle Allah Masanin abin da kuke aikatawa ne?



Sura: Suratu Luqman

Aya : 30

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدۡعُونَ مِن دُونِهِ ٱلۡبَٰطِلُ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡكَبِيرُ

Wannan kuwa (suna samuwa ne) saboda Allah Shi ne Gaskiya, lalle kuma abin da suke bauta wa ba Shi ba qarya ne, lalle kuma Shi Allah Maxaukaki ne, Mai girma