قَدۡ أَفۡلَحَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ
Haqiqa muminai sun rabauta
ٱلَّذِينَ هُمۡ فِي صَلَاتِهِمۡ خَٰشِعُونَ
(Su ne) waxanda suke masu qasqantar da kai a cikin sallarsu
وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَنِ ٱللَّغۡوِ مُعۡرِضُونَ
Kuma waxanda suke masu kau da kai daga yasasshiyar magana
وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِلزَّكَوٰةِ فَٰعِلُونَ
Kuma waxanda suke masu aiwatar da zakka
وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِفُرُوجِهِمۡ حَٰفِظُونَ
Kuma waxanda suke masu kiyaye farjinsu
إِلَّا عَلَىٰٓ أَزۡوَٰجِهِمۡ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ فَإِنَّهُمۡ غَيۡرُ مَلُومِينَ
Sai dai ga matayensu ko kuma qwara-qwaransu, to lalle su ba abin zargi ba ne
فَمَنِ ٱبۡتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡعَادُونَ
Sannan duk wanda ya nemi (wata hanya) ba waxannan ba, to waxannan su ne masu qetare iyaka
وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِأَمَٰنَٰتِهِمۡ وَعَهۡدِهِمۡ رَٰعُونَ
Kuma waxanda suke masu kiyaye amanarsu da kuma alqawarinsu
وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَوَٰتِهِمۡ يُحَافِظُونَ
Kuma waxanda suke kiyaye sallolinsu
أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡوَٰرِثُونَ
Waxannan su ne magada
ٱلَّذِينَ يَرِثُونَ ٱلۡفِرۡدَوۡسَ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Waxanda suke gadar (Aljannar) Firdausi, su madawwama ne a cikinta
وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِن سُلَٰلَةٖ مِّن طِينٖ
Kuma haqiqa Mun halicci mutum daga tataccen tavo
ثُمَّ جَعَلۡنَٰهُ نُطۡفَةٗ فِي قَرَارٖ مَّكِينٖ
Sannan Muka mai da shi maniyyi cikin wuri amintacce
ثُمَّ خَلَقۡنَا ٱلنُّطۡفَةَ عَلَقَةٗ فَخَلَقۡنَا ٱلۡعَلَقَةَ مُضۡغَةٗ فَخَلَقۡنَا ٱلۡمُضۡغَةَ عِظَٰمٗا فَكَسَوۡنَا ٱلۡعِظَٰمَ لَحۡمٗا ثُمَّ أَنشَأۡنَٰهُ خَلۡقًا ءَاخَرَۚ فَتَبَارَكَ ٱللَّهُ أَحۡسَنُ ٱلۡخَٰلِقِينَ
Sannan Muka mayar da maniyyin ya zama gudan jini, sai gudan jinin ya zama tsoka, sai Muka mai da tsokar qasusuwa, sannan Muka lulluve qasusuwan da nama, sannan kuma Muka mai da shi wata halitta daban. To albarkatun Allah sun yawaita, Wanda Shi ne Mafi gwanintar masu halitta
ثُمَّ إِنَّكُم بَعۡدَ ذَٰلِكَ لَمَيِّتُونَ
Sannan kuma lalle tabbas bayan haka za ku mutu
ثُمَّ إِنَّكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ تُبۡعَثُونَ
Sannan kuma haqiqa za a tashe ku ranar Alqiyama
وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا فَوۡقَكُمۡ سَبۡعَ طَرَآئِقَ وَمَا كُنَّا عَنِ ٱلۡخَلۡقِ غَٰفِلِينَ
Kuma haqiqa Mun halicci hanyoyi bakwai a sama da ku, ba Mu kuma zama gafalallu ba game da halittar
وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءَۢ بِقَدَرٖ فَأَسۡكَنَّـٰهُ فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَإِنَّا عَلَىٰ ذَهَابِۭ بِهِۦ لَقَٰدِرُونَ
Muka kuma saukar da ruwa daga sama daidai gwargwado, sai Muka zaunar da shi a cikin qasa, kuma lalle Mu Masu iko ne a kan kawar da shi
فَأَنشَأۡنَا لَكُم بِهِۦ جَنَّـٰتٖ مِّن نَّخِيلٖ وَأَعۡنَٰبٖ لَّكُمۡ فِيهَا فَوَٰكِهُ كَثِيرَةٞ وَمِنۡهَا تَأۡكُلُونَ
Sai Muka samar muku gonaki na dabinai da inabai da shi (ruwan), kuna kuma da kayan marmari masu yawa a cikinsu (gonakin), kuma daga gare su kuke ci
وَشَجَرَةٗ تَخۡرُجُ مِن طُورِ سَيۡنَآءَ تَنۢبُتُ بِٱلدُّهۡنِ وَصِبۡغٖ لِّلۡأٓكِلِينَ
Kuma (Mun halitta muku) wata bishiya da take fitowa a (dutsen) Xuri Sina’a, tana fito da man (zaitun) kuma mahaxin abinci ne
وَإِنَّ لَكُمۡ فِي ٱلۡأَنۡعَٰمِ لَعِبۡرَةٗۖ نُّسۡقِيكُم مِّمَّا فِي بُطُونِهَا وَلَكُمۡ فِيهَا مَنَٰفِعُ كَثِيرَةٞ وَمِنۡهَا تَأۡكُلُونَ
Kuma lalle akwai izina a gare ku game da dabbobin ni’ima[1]; Muna shayar da ku daga abin da yake cikinsu[2], kuma kuna da amfani mai yawa daga gare su, daga gare su kuma kuke ci
1- Su ne raquma da shanu da tumaki da awaki.
2- Shi ne tataccen nono.
وَعَلَيۡهَا وَعَلَى ٱلۡفُلۡكِ تُحۡمَلُونَ
A kansu da kuma a kan jirgin ruwa ake xaukar ku
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ فَقَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓۚ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Haqiqa kuma Mun aiko Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta in ba Shi ba; me ya sa ne ba za ku yi taqawa ba.”
فَقَالَ ٱلۡمَلَؤُاْ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَوۡمِهِۦ مَا هَٰذَآ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ يُرِيدُ أَن يَتَفَضَّلَ عَلَيۡكُمۡ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَأَنزَلَ مَلَـٰٓئِكَةٗ مَّا سَمِعۡنَا بِهَٰذَا فِيٓ ءَابَآئِنَا ٱلۡأَوَّلِينَ
Sai manya-manyan da suka kafirce daga mutanen nasa suka ce: “Ai wannan ba kowa ba ne face mutum irinku, yana so ne ya samu fifiko a kanku, kuma da Allah Ya ga dama da sai Ya saukar da mala’iku, mu ba mu tava jin irin wannan ba daga iyayenmu na farko
إِنۡ هُوَ إِلَّا رَجُلُۢ بِهِۦ جِنَّةٞ فَتَرَبَّصُواْ بِهِۦ حَتَّىٰ حِينٖ
“Ba kowa ba ne shi in ban da mutum da yake da (tavin) aljan, sai ku saurara masa har zuwa wani xan lokaci.”
قَالَ رَبِّ ٱنصُرۡنِي بِمَا كَذَّبُونِ
Ya ce: “Ubangijina Ka taimake ni game da abin da suka qaryata ni a kansa.”
فَأَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡهِ أَنِ ٱصۡنَعِ ٱلۡفُلۡكَ بِأَعۡيُنِنَا وَوَحۡيِنَا فَإِذَا جَآءَ أَمۡرُنَا وَفَارَ ٱلتَّنُّورُ فَٱسۡلُكۡ فِيهَا مِن كُلّٖ زَوۡجَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِ وَأَهۡلَكَ إِلَّا مَن سَبَقَ عَلَيۡهِ ٱلۡقَوۡلُ مِنۡهُمۡۖ وَلَا تُخَٰطِبۡنِي فِي ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ إِنَّهُم مُّغۡرَقُونَ
Sai Muka yiwo masa wahayi cewa: “Ka sassaqa jirgin ruwa a qarqashin kulawarmu da umarninmu, sannan idan umarninmu (na hallaka su) ya zo, kuma tanderu ya vuvvugo da ruwa, sai ka saka ma’aurata guda biyu daga kowane jinsi a cikinsa, da kuma iyalanka, sai wanda kalmar (halaka) ta rigaya a kansa daga cikinsu; kuma kada ka ce min komai game da waxanda suka kafirta; lalle su waxanda za a nutsar ne
فَإِذَا ٱسۡتَوَيۡتَ أَنتَ وَمَن مَّعَكَ عَلَى ٱلۡفُلۡكِ فَقُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي نَجَّىٰنَا مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ
“To idan kai da waxanda suke tare da kai kuka daidaita a kan jirgin, sai ka ce: “Na gode wa Allah wanda Ya tserar da mu daga mutane azzalumai.”
وَقُل رَّبِّ أَنزِلۡنِي مُنزَلٗا مُّبَارَكٗا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلۡمُنزِلِينَ
Kuma ka ce: “Ubangijina Ka saukar da ni masauki mai albarka, Kai ne kuwa Fiyayyen masu saukarwa.”
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ وَإِن كُنَّا لَمُبۡتَلِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi, Mu kuma haqiqa Mun kasance Masu jarrabawa ne