ٱقۡتَرَبَ لِلنَّاسِ حِسَابُهُمۡ وَهُمۡ فِي غَفۡلَةٖ مُّعۡرِضُونَ
Lokacin yi wa mutane hisabi ya kusanto, alhali suna cikin gafala (suna) masu bijirewa
مَا يَأۡتِيهِم مِّن ذِكۡرٖ مِّن رَّبِّهِم مُّحۡدَثٍ إِلَّا ٱسۡتَمَعُوهُ وَهُمۡ يَلۡعَبُونَ
Ba wata tunatarwa sabowa (wato Alqur’ani) da za ta zo musu daga Ubangijinsu face sai sun saurare ta suna masu wasa
لَاهِيَةٗ قُلُوبُهُمۡۗ وَأَسَرُّواْ ٱلنَّجۡوَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ هَلۡ هَٰذَآ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡۖ أَفَتَأۡتُونَ ٱلسِّحۡرَ وَأَنتُمۡ تُبۡصِرُونَ
Zukatansu suna cikin gafala. Waxanda suka yi zalunci kuma suka voye abin da suka tattauna (na cewa): “Wannan ba wani ne in ban da mutum kamarku; yanzu kwa riqa bin sihiri alhali kuwa ku kuna gani?”
قَالَ رَبِّي يَعۡلَمُ ٱلۡقَوۡلَ فِي ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Ya ce: “Ubangijina Yana sane da (kowace) magana a cikin sammai da qasa; Shi kuwa Mai ji ne, Masani
بَلۡ قَالُوٓاْ أَضۡغَٰثُ أَحۡلَٰمِۭ بَلِ ٱفۡتَرَىٰهُ بَلۡ هُوَ شَاعِرٞ فَلۡيَأۡتِنَا بِـَٔايَةٖ كَمَآ أُرۡسِلَ ٱلۡأَوَّلُونَ
A’a, cewa dai suka yi: “Ai (shi Alqur’ani) tarkacen mafarki ne, a’a, shi (Muhammadu) qago shi ya yi, a’a, shi mawaqi dai ne, to sai ya zo mana da wata aya kamar yadda aka aiko wa mutanen farko.”
مَآ ءَامَنَتۡ قَبۡلَهُم مِّن قَرۡيَةٍ أَهۡلَكۡنَٰهَآۖ أَفَهُمۡ يُؤۡمِنُونَ
Ai babu wata al’umma da ta yi imani a gabaninsu wadda Muka hallaka; shin yanzu su za su yi imani?
وَمَآ أَرۡسَلۡنَا قَبۡلَكَ إِلَّا رِجَالٗا نُّوحِيٓ إِلَيۡهِمۡۖ فَسۡـَٔلُوٓاْ أَهۡلَ ٱلذِّكۡرِ إِن كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ
Kuma ba Mu aiko (wasu manzanni) gabaninka ba sai mazaje da Muke yi musu wahayi; to ku tambayi ma’abota sani idan ya zamana ku ba ku sani ba
وَمَا جَعَلۡنَٰهُمۡ جَسَدٗا لَّا يَأۡكُلُونَ ٱلطَّعَامَ وَمَا كَانُواْ خَٰلِدِينَ
Kuma ba Mu sanya su jiki ne da ba sa cin abinci ba, kuma ba su zamanto masu dawwama ba
ثُمَّ صَدَقۡنَٰهُمُ ٱلۡوَعۡدَ فَأَنجَيۡنَٰهُمۡ وَمَن نَّشَآءُ وَأَهۡلَكۡنَا ٱلۡمُسۡرِفِينَ
Sannan Muka cika musu alqawari, sai Muka tserar da su da waxanda Muke ga damar (tserarwa) kuma Muka hallakar da mavarnata
لَقَدۡ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكُمۡ كِتَٰبٗا فِيهِ ذِكۡرُكُمۡۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Haqiqa Mun saukar muku da littafi (wanda) a cikinsa akwai xaukakarku[1]; me ya sa ba kwa hankalta?
1- Watau za su samu xaukaka duniya da lahira idan sun yi imani da shi, suka yi aiki da karantarwarsa.
وَكَمۡ قَصَمۡنَا مِن قَرۡيَةٖ كَانَتۡ ظَالِمَةٗ وَأَنشَأۡنَا بَعۡدَهَا قَوۡمًا ءَاخَرِينَ
Al’ummu nawa ne kuma Muka hallakar (waxanda) suka kasance azzulumai, Muka kuma halicci wasu mutanen daban bayansu?
فَلَمَّآ أَحَسُّواْ بَأۡسَنَآ إِذَا هُم مِّنۡهَا يَرۡكُضُونَ
Lokacin da suka fara jin azabarmu sai ga su suna guje mata
لَا تَرۡكُضُواْ وَٱرۡجِعُوٓاْ إِلَىٰ مَآ أُتۡرِفۡتُمۡ فِيهِ وَمَسَٰكِنِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تُسۡـَٔلُونَ
(Aka ce da su): “Kada ku gudu, ku dawo zuwa ga abin da aka ni’imta ku da shi, da kuma gidajenku don a yi muku tambayoyi[1].”
1- Watau a kan rayuwarsu ta tamore da bushasha. Ana faxa musu haka a cikin izgili da tsokana.
قَالُواْ يَٰوَيۡلَنَآ إِنَّا كُنَّا ظَٰلِمِينَ
Suka ce: “Kaiconmu, lallai mu kam mun kasance azzalumai!”
فَمَا زَالَت تِّلۡكَ دَعۡوَىٰهُمۡ حَتَّىٰ جَعَلۡنَٰهُمۡ حَصِيدًا خَٰمِدِينَ
Sannan waccan (maganar tasu) ba su daina faxar ta ba har Muka mai da su girbabbu, matattu
وَمَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَآءَ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا لَٰعِبِينَ
Kuma ba Mu halicci sama da qasa da kuma abin da yake tsakaninsu don wasa ba
لَوۡ أَرَدۡنَآ أَن نَّتَّخِذَ لَهۡوٗا لَّٱتَّخَذۡنَٰهُ مِن لَّدُنَّآ إِن كُنَّا فَٰعِلِينَ
In da Mun yi nufin Mu riqi (abin) da zai shagaltar (mata ko xa), to da sai Mu riqe shi daga waxanda suke a wurinmu, idan har za Mu yi hakan
بَلۡ نَقۡذِفُ بِٱلۡحَقِّ عَلَى ٱلۡبَٰطِلِ فَيَدۡمَغُهُۥ فَإِذَا هُوَ زَاهِقٞۚ وَلَكُمُ ٱلۡوَيۡلُ مِمَّا تَصِفُونَ
A’a, ba haka ba ne, Muna jefa gaskiya a kan qarya, sai ta yi rugu-rugu da ita, sai (ka gan ta) ta vace vat. Kuma tsananin azaba ya tabbata a gare ku saboda abin da kuke siffanta (Shi da shi)[1]
1- Watau na cewa yana da mata ko xa ko abokin tarayya.
وَلَهُۥ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَمَنۡ عِندَهُۥ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ عَنۡ عِبَادَتِهِۦ وَلَا يَسۡتَحۡسِرُونَ
Duk kuwa waxanda suke sammai da qasa nasa ne, kuma waxanda suke wurinsa ba sa girman kai game da bauta masa, kuma ba sa gajiya
يُسَبِّحُونَ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ لَا يَفۡتُرُونَ
Suna tasbihi dare da rana ba sa qosawa
أَمِ ٱتَّخَذُوٓاْ ءَالِهَةٗ مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ هُمۡ يُنشِرُونَ
Shin ko sun riqi wasu ababen bauta a nan qasa ne waxanda suke raya matattu?
لَوۡ كَانَ فِيهِمَآ ءَالِهَةٌ إِلَّا ٱللَّهُ لَفَسَدَتَاۚ فَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ رَبِّ ٱلۡعَرۡشِ عَمَّا يَصِفُونَ
Da ya zamana akwai wasu ababen bauta ba Allah ba a cikinsu (wato sammai da qasa), to da sun lalace. Sai dai tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al’arshi game da abin da suke siffata (Shi da shi)
لَا يُسۡـَٔلُ عَمَّا يَفۡعَلُ وَهُمۡ يُسۡـَٔلُونَ
Ba a tambayar Sa game da abin da yake aikatawa, su dai ne za a tambaye su
أَمِ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةٗۖ قُلۡ هَاتُواْ بُرۡهَٰنَكُمۡۖ هَٰذَا ذِكۡرُ مَن مَّعِيَ وَذِكۡرُ مَن قَبۡلِيۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ ٱلۡحَقَّۖ فَهُم مُّعۡرِضُونَ
Ko kuma sun riqi wasu ababen bauta ne ba Shi ba? Ka ce (da su): “To ku kawo dalilinku (a kan haka). Ga wa’azin waxanda suke tare dani (watau Alqur’ani), ga kuma wa’azin waxanda suka gabace ni (watau littattafan annabawa sai ku duba).” A’a, yawancinsu dai ba sa sanin gaskiya sannan kuma masu bijire (mata) ne
وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِيٓ إِلَيۡهِ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدُونِ
Kuma ba wani manzo da Muka aiko gabaninka face sai Mun yi masa wahayi cewa, babu wani abin bauta da gaskiya sai Ni; to sai ku bauta min[1]
1- Duk manzannin da Allah ya aiko sun zo ne da saqon a bauta wa Allah shi kaxai ba tare da shirka ba.
وَقَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَلَدٗاۗ سُبۡحَٰنَهُۥۚ بَلۡ عِبَادٞ مُّكۡرَمُونَ
Suka kuma ce wai Allah Ya riqi xa (daga cikin mala’iku)! Tsarki ya tabbata a gare Shi. A’a, su bayi dai ne ababen girmamawa
لَا يَسۡبِقُونَهُۥ بِٱلۡقَوۡلِ وَهُم بِأَمۡرِهِۦ يَعۡمَلُونَ
Ba sa rigayar Sa da magana, su kuma da umarninsa suke aiki
يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَلَا يَشۡفَعُونَ إِلَّا لِمَنِ ٱرۡتَضَىٰ وَهُم مِّنۡ خَشۡيَتِهِۦ مُشۡفِقُونَ
Yana sane da ayyukansu da suka gabatar da na nan gaba, ba kuma za su yi ceto ba sai ga wanda Ya yarda (daga bayinsa), suna kuwa masu kaffa-kaffa don tsoron Sa
۞وَمَن يَقُلۡ مِنۡهُمۡ إِنِّيٓ إِلَٰهٞ مِّن دُونِهِۦ فَذَٰلِكَ نَجۡزِيهِ جَهَنَّمَۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلظَّـٰلِمِينَ
Daga cikinsu kuwa duk wanda ya ce: “Ni abin bauta ne ba shi (Allah) ba,” to wannan za Mu saka masa da (wutar) Jahannama. Kamar haka kuwa Muke saka wa azzalumai
أَوَلَمۡ يَرَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَنَّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ كَانَتَا رَتۡقٗا فَفَتَقۡنَٰهُمَاۖ وَجَعَلۡنَا مِنَ ٱلۡمَآءِ كُلَّ شَيۡءٍ حَيٍّۚ أَفَلَا يُؤۡمِنُونَ
Yanzu waxanda suka kafirta ba sa ganin cewa a da can sammai da qasa a haxe suke, sannan Muka raba su[1]; Muka kuma halicci duk wani abu mai rai daga ruwa? To me ya sa ba za su yi imani ba?
1- Watau Allah () ya fara halittar sammai da qasa a manne da juna daga bisani ya raba tsakaninsu.