وَيۡلٞ لِّكُلِّ هُمَزَةٖ لُّمَزَةٍ
Tsananin azaba ya tabbata ga duk wani mai yawan qyafice mai yawan suka[1]
1- Watau yawan qyafice ga mutane, yana kuma yawan sukan su da aibata su a bayan idanuwansu..
Tarayya :
ٱلَّذِي جَمَعَ مَالٗا وَعَدَّدَهُۥ
Wanda ya tara dukiya ya qididdige ta
يَحۡسَبُ أَنَّ مَالَهُۥٓ أَخۡلَدَهُۥ
Yana zaton cewa dukiyarsa za ta dawwamar da shi
كَلَّاۖ لَيُنۢبَذَنَّ فِي ٱلۡحُطَمَةِ
Faufau! Tabbas lalle sai an jefa shi cikin (wutar) ‘Huxama’[1]
1- Ita ce wuta mai kakkarya duk wani abu da aka jefa cikinta saboda tsananin zafinta da azabarta.
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡحُطَمَةُ
Me kuma ya sanar da kai irin girman ‘Huxama’?
نَارُ ٱللَّهِ ٱلۡمُوقَدَةُ
Wuta ce ta Allah abar hurawa
ٱلَّتِي تَطَّلِعُ عَلَى ٱلۡأَفۡـِٔدَةِ
Wadda take mamaye zukata
إِنَّهَا عَلَيۡهِم مُّؤۡصَدَةٞ
Lalle ita abar kullewa ce da su[1]
1- Watau za a kulle kafirai a cikin ruf babu fita.
فِي عَمَدٖ مُّمَدَّدَةِۭ
A cikin ginshiqai miqaqqu (da suka kewaye ta)