Sura: Suratul Baqara

Aya : 211

سَلۡ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ كَمۡ ءَاتَيۡنَٰهُم مِّنۡ ءَايَةِۭ بَيِّنَةٖۗ وَمَن يُبَدِّلۡ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُ فَإِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Ka tambayi Banu Isra’ila, sau nawa Muka ba su wata aya bayyananniya? Kuma duk wanda ya musanya ni’imar Allah bayan ta zo masa, to lalle Allah Mai tsananin uquba ne



Sura: Suratul Baqara

Aya : 212

زُيِّنَ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا وَيَسۡخَرُونَ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۘ وَٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ فَوۡقَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ وَٱللَّهُ يَرۡزُقُ مَن يَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٖ

An qawata wa kafirai rayuwar duniya, kuma suna yin izgili ga waxanda suka yi imani. Waxanda kuwa suka yi taqawa su ne a samansu a ranar alqiyama. Kuma Allah Yana arzurta wanda ya ga dama, ba tare da lissafi ba



Sura: Suratul Baqara

Aya : 213

كَانَ ٱلنَّاسُ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ فَبَعَثَ ٱللَّهُ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ لِيَحۡكُمَ بَيۡنَ ٱلنَّاسِ فِيمَا ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِۚ وَمَا ٱخۡتَلَفَ فِيهِ إِلَّا ٱلَّذِينَ أُوتُوهُ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ بَغۡيَۢا بَيۡنَهُمۡۖ فَهَدَى ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لِمَا ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِ مِنَ ٱلۡحَقِّ بِإِذۡنِهِۦۗ وَٱللَّهُ يَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٍ

Mutane sun kasance al’umma guda xaya, sai Allah Ya aiko da annabawa, suna masu albishir, kuma masu gargaxi, kuma Ya saukar da littafi tare da su da gaskiya, don ya yi hukunci tsakanin mutane cikin abin da suka yi savani a kansa. Kuma ba wasu ne suka yi savani a kansa ba sai waxanda aka ba wa shi, bayan hujjoji bayyanannu sun zo musu, don zalunci a tsakaninsu; sai Allah Ya shiryar da waxanda suka yi imani ga abin da (mutane) suka yi savani cikinsa na gaskiya da izininsa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga tafarki madaidaici



Sura: Suratul Baqara

Aya : 214

أَمۡ حَسِبۡتُمۡ أَن تَدۡخُلُواْ ٱلۡجَنَّةَ وَلَمَّا يَأۡتِكُم مَّثَلُ ٱلَّذِينَ خَلَوۡاْ مِن قَبۡلِكُمۖ مَّسَّتۡهُمُ ٱلۡبَأۡسَآءُ وَٱلضَّرَّآءُ وَزُلۡزِلُواْ حَتَّىٰ يَقُولَ ٱلرَّسُولُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ مَتَىٰ نَصۡرُ ٱللَّهِۗ أَلَآ إِنَّ نَصۡرَ ٱللَّهِ قَرِيبٞ

Shin kun yi tsammanin za ku shiga Aljanna ne, alhalin misalin irin abin da ya shafi waxanda suka shuxe gabaninku bai zo muku ba? Tsananin talauci da cuta sun shafe su; kuma an girgiza su sosai, har Manzo da waxanda suka yi imani tare da shi suka riqa cewa: “Yaushe ne nasarar Allah za ta zo?” Ku saurara, lalle nasarar Allah a kusa take



Sura: Suratul Baqara

Aya : 215

يَسۡـَٔلُونَكَ مَاذَا يُنفِقُونَۖ قُلۡ مَآ أَنفَقۡتُم مِّنۡ خَيۡرٖ فَلِلۡوَٰلِدَيۡنِ وَٱلۡأَقۡرَبِينَ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِۗ وَمَا تَفۡعَلُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٞ

Suna tambayar ka, me za su ciyar ne? Ka ce: “Duk abin da za ku ciyar na alheri, to ga mahaifa da dangi mafiya kusanci da marayu da miskinai da matafiyi. Kuma duk abin da kuka aikata na alheri, to lalle Allah Masani ne da shi.”



Sura: Suratul Baqara

Aya : 216

كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡقِتَالُ وَهُوَ كُرۡهٞ لَّكُمۡۖ وَعَسَىٰٓ أَن تَكۡرَهُواْ شَيۡـٔٗا وَهُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡۖ وَعَسَىٰٓ أَن تُحِبُّواْ شَيۡـٔٗا وَهُوَ شَرّٞ لَّكُمۡۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ

An wajabta muku yaqi (ku muminai), ga shi kuwa kuna qin sa, kuma zai iya yiwuwa ku qi wani abu alhalin shi alheri ne a gare ku, kuma zai iya yiwuwa ku so wani abu alhalin shi sharri ne a gare ku. Kuma Allah Shi yake da sani, ku ba ku sani ba



Sura: Suratul Baqara

Aya : 217

يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلشَّهۡرِ ٱلۡحَرَامِ قِتَالٖ فِيهِۖ قُلۡ قِتَالٞ فِيهِ كَبِيرٞۚ وَصَدٌّ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَكُفۡرُۢ بِهِۦ وَٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ وَإِخۡرَاجُ أَهۡلِهِۦ مِنۡهُ أَكۡبَرُ عِندَ ٱللَّهِۚ وَٱلۡفِتۡنَةُ أَكۡبَرُ مِنَ ٱلۡقَتۡلِۗ وَلَا يَزَالُونَ يُقَٰتِلُونَكُمۡ حَتَّىٰ يَرُدُّوكُمۡ عَن دِينِكُمۡ إِنِ ٱسۡتَطَٰعُواْۚ وَمَن يَرۡتَدِدۡ مِنكُمۡ عَن دِينِهِۦ فَيَمُتۡ وَهُوَ كَافِرٞ فَأُوْلَـٰٓئِكَ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Suna tambayar ka game da wata mai alfarma, yin yaqi a cikinsa. Ka ce: “Yaqi a cikinsa, babban laifi ne, amma hana (mutane) bin tafarkin Allah da kafirce masa da kuma (hana mutane shiga) Masallaci mai alfarma da fitar da mutanensa daga gare shi, su ne mafi girman laifi a wajen Allah. Kuma (laifin) fitina ya fi na kisa girma.”[1] Kuma (kafirai) ba za su gushe ba suna yaqar ku, har sai sun raba ku da addininku, idan da za su sami dama. Kuma duk wanda ya yi ridda daga cikinku, ya bar addininsa, kuma ya mutu yana kafiri, to waxannan ayyukansu sun lalace a duniya da lahira, kuma waxannan su ne ma’abota wuta, suna masu dawwama a cikinta


1- Wannan ayar ta sauka ne bayan da wata runduna ta Musulmi suka kashe wani kafiri mai suna Ibnul Hadhrami a watan Rajab ba su sani ba. Sai kafirai suka riqa aibata su da haka, sai Allah ya saukar da wannan ayar.


Sura: Suratul Baqara

Aya : 218

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ وَجَٰهَدُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أُوْلَـٰٓئِكَ يَرۡجُونَ رَحۡمَتَ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Lalle waxanda suka yi imani da kuma waxanda suka yi hijira, kuma suka yi jihadi don Allah, waxannan su ne suke fatan rahamar Allah; Allah kuwa Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin qai



Sura: Suratul Baqara

Aya : 219

۞يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡخَمۡرِ وَٱلۡمَيۡسِرِۖ قُلۡ فِيهِمَآ إِثۡمٞ كَبِيرٞ وَمَنَٰفِعُ لِلنَّاسِ وَإِثۡمُهُمَآ أَكۡبَرُ مِن نَّفۡعِهِمَاۗ وَيَسۡـَٔلُونَكَ مَاذَا يُنفِقُونَۖ قُلِ ٱلۡعَفۡوَۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّكُمۡ تَتَفَكَّرُونَ

Suna tambayar ka game da giya da caca. Ka ce: “A cikin lamarinsu akwai zunubi mai girma da kuma waxansu amfanunnuka ga mutane. Amma zunubinsu ya fi amfaninsu girma”[1] Kuma suna tambayar ka, me za su ciyar? Ka ce: “Abin da ya daxu a kan buqatunku.” Kamar haka ne Allah Yake muku bayanin ayoyi don ku yi tunani


1- Wannan matakin farko ne na tsawatarwa game da giya. Allah ya haramta giya gaba xaya a Suratul Ma’ida, aya ta 90-91


Sura: Suratul Baqara

Aya : 220

فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۗ وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡيَتَٰمَىٰۖ قُلۡ إِصۡلَاحٞ لَّهُمۡ خَيۡرٞۖ وَإِن تُخَالِطُوهُمۡ فَإِخۡوَٰنُكُمۡۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ ٱلۡمُفۡسِدَ مِنَ ٱلۡمُصۡلِحِۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَأَعۡنَتَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

Game da lamarin duniya da lahira. Kuma suna tambayar ka game da marayu. Ka ce : “Inganta musu dukiyarsu shi ne mafi alheri, kuma in kuka haxa cimakarku da tasu, to ai ‘yan’uwanku ne. Amma fa Allah Ya san mai son yin varna daga wanda yake son yin gyara. Kuma da Allah Ya ga dama da Ya quntata muku. Lalle Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.”



Sura: Suratul Baqara

Aya : 221

وَلَا تَنكِحُواْ ٱلۡمُشۡرِكَٰتِ حَتَّىٰ يُؤۡمِنَّۚ وَلَأَمَةٞ مُّؤۡمِنَةٌ خَيۡرٞ مِّن مُّشۡرِكَةٖ وَلَوۡ أَعۡجَبَتۡكُمۡۗ وَلَا تُنكِحُواْ ٱلۡمُشۡرِكِينَ حَتَّىٰ يُؤۡمِنُواْۚ وَلَعَبۡدٞ مُّؤۡمِنٌ خَيۡرٞ مِّن مُّشۡرِكٖ وَلَوۡ أَعۡجَبَكُمۡۗ أُوْلَـٰٓئِكَ يَدۡعُونَ إِلَى ٱلنَّارِۖ وَٱللَّهُ يَدۡعُوٓاْ إِلَى ٱلۡجَنَّةِ وَٱلۡمَغۡفِرَةِ بِإِذۡنِهِۦۖ وَيُبَيِّنُ ءَايَٰتِهِۦ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ

Kuma kada ku auri mata mushirikai har sai sun yi imani, kuma lalle baiwa mumina ta fi ‘ya mushirika alheri, ko da (mushirikar) ta burge ku. Kuma kada ku aurar wa mushirikai har sai sun yi imani; kuma lalle bawa mumini ya fi (xa) mushiriki alheri, ko da ya burge ku. Su waxancan (kafirai), suna kira ne zuwa ga wuta, Allah kuwa Yana kira ne zuwa ga Aljanna da gafara da izininsa, kuma Yana bayyana ayoyinsa ga mutane don su wa’azantu



Sura: Suratul Baqara

Aya : 222

وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡمَحِيضِۖ قُلۡ هُوَ أَذٗى فَٱعۡتَزِلُواْ ٱلنِّسَآءَ فِي ٱلۡمَحِيضِ وَلَا تَقۡرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطۡهُرۡنَۖ فَإِذَا تَطَهَّرۡنَ فَأۡتُوهُنَّ مِنۡ حَيۡثُ أَمَرَكُمُ ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلتَّوَّـٰبِينَ وَيُحِبُّ ٱلۡمُتَطَهِّرِينَ

Kuma suna tambayar ka game da jinin haila. Ka ce:  “Shi cuta ne, don haka ku qaurace wa mata a (kwanakin) haila, kuma kada ku kusance su har sai sun tsarkaka. To idan suka yi tsarki, sai ku zo musu ta inda Allah Ya umarce ku. Lalle Allah Yana son masu yawan tuba, kuma Yana son masu tsarki.”



Sura: Suratul Baqara

Aya : 223

نِسَآؤُكُمۡ حَرۡثٞ لَّكُمۡ فَأۡتُواْ حَرۡثَكُمۡ أَنَّىٰ شِئۡتُمۡۖ وَقَدِّمُواْ لِأَنفُسِكُمۡۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّكُم مُّلَٰقُوهُۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Matanku gonaki ne a gare ku, don haka ku zaike wa gonakinku ta inda kuka ga dama, kuma ku gabatar wa kawunanku (laduban da shari’a ta tanadar muku). Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku sani cewa, lalle ku masu saduwa ne da Shi. Kuma ka yi albishir ga muminai



Sura: Suratul Baqara

Aya : 224

وَلَا تَجۡعَلُواْ ٱللَّهَ عُرۡضَةٗ لِّأَيۡمَٰنِكُمۡ أَن تَبَرُّواْ وَتَتَّقُواْ وَتُصۡلِحُواْ بَيۡنَ ٱلنَّاسِۚ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Kuma kada ku mayar da Allah Ya zamanto kariya ga rantse-rantsenku don su hana ku aiki na xa’a ko na taqawa ko na sulhu tsakanin mutane. Kuma Allah Mai ji ne, Masani



Sura: Suratul Baqara

Aya : 225

لَّا يُؤَاخِذُكُمُ ٱللَّهُ بِٱللَّغۡوِ فِيٓ أَيۡمَٰنِكُمۡ وَلَٰكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا كَسَبَتۡ قُلُوبُكُمۡۗ وَٱللَّهُ غَفُورٌ حَلِيمٞ

Allah ba zai kama ku da yasasshen zance a cikin rantse-rantsenku ba, sai dai zai kama ku da abin da zukatanku suka qudurce. Kuma Allah Mai yawan gafara ne, Mai yawan haquri



Sura: Suratul Baqara

Aya : 226

لِّلَّذِينَ يُؤۡلُونَ مِن نِّسَآئِهِمۡ تَرَبُّصُ أَرۡبَعَةِ أَشۡهُرٖۖ فَإِن فَآءُو فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Waxanda suke rantsuwar ba za su sadu da matansu ba, za a yi musu jinkiri na wata huxu; to idan sun dawo, to lalle Allah Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin qai



Sura: Suratul Baqara

Aya : 227

وَإِنۡ عَزَمُواْ ٱلطَّلَٰقَ فَإِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Idan kuwa suka yi niyyar saki (a cikin zukatansu), to lalle Allah Mai ji ne, kuma Masani



Sura: Suratul Baqara

Aya : 228

وَٱلۡمُطَلَّقَٰتُ يَتَرَبَّصۡنَ بِأَنفُسِهِنَّ ثَلَٰثَةَ قُرُوٓءٖۚ وَلَا يَحِلُّ لَهُنَّ أَن يَكۡتُمۡنَ مَا خَلَقَ ٱللَّهُ فِيٓ أَرۡحَامِهِنَّ إِن كُنَّ يُؤۡمِنَّ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ وَبُعُولَتُهُنَّ أَحَقُّ بِرَدِّهِنَّ فِي ذَٰلِكَ إِنۡ أَرَادُوٓاْ إِصۡلَٰحٗاۚ وَلَهُنَّ مِثۡلُ ٱلَّذِي عَلَيۡهِنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ وَلِلرِّجَالِ عَلَيۡهِنَّ دَرَجَةٞۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ

Kuma mata waxanda aka saki za su dakatar da kawunansu (tsawon) qur’i[1] uku, kuma ba ya halatta a gare su su voye abin da Allah Ya halitta a cikin mahaifarsu, in sun kasance suna yin imani da Allah da ranar qarshe; kuma mazajensu su suka fi cancantar dawo da su a cikin wancan lokaci in sun yi nufin sulhu[2]; kuma su (mata) suna da haqqi kwatankwacin irin wanda yake kansu ta hanyar da aka sani, kuma mazaje suna da fifiko a kansu. Allah Kuma Mabuwayi ne, Mai hikima


1- Qur’i a Larabci yana nufin ‘haila’ ko ‘tsarki’, A ra’ayin manyan sahabbai, har da Halifofi huxu da wasu tabi’ai, sun ce, ana nufin ‘jinin haila’. Watau iddar wadda aka saki tana qare wa da xaukewar jinin al’adar ta ta uku bayan sakin.


2- Mijin da ya saki matarsa saki na farko, ko na biyu, zai iya dawo da ita matuqar suna son su ci gaba da zama da juna cikin mutuntawa da kyautatawa.


Sura: Suratul Baqara

Aya : 229

ٱلطَّلَٰقُ مَرَّتَانِۖ فَإِمۡسَاكُۢ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ تَسۡرِيحُۢ بِإِحۡسَٰنٖۗ وَلَا يَحِلُّ لَكُمۡ أَن تَأۡخُذُواْ مِمَّآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ شَيۡـًٔا إِلَّآ أَن يَخَافَآ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِۖ فَإِنۡ خِفۡتُمۡ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِمَا فِيمَا ٱفۡتَدَتۡ بِهِۦۗ تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِ فَلَا تَعۡتَدُوهَاۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ ٱللَّهِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Saki sau biyu ne (xaya bayan xaya), don haka ko dai ya riqe ta ta hanyar da aka sani, ko kuma ya sake ta tare da kyautatawa. Kuma bai halatta gare ku ba ku karvi wani abu daga cikin abin da kuka ba su, sai fa idan su (ma’aurata) biyu sun ji tsoron ba za su tsayar da dokokin Allah ba. To idan kuka ji tsoron ba za su tsayar da dokokin Allah ba, to babu laifi a gare su game da abin da ta fanshi kanta da shi[1]. Waxannan iyakokin Allah ne, kada ku qetare su, kuma duk wanda ya qetare iyakokin Allah, to waxannan su ne azzalumai


1- Idan mace ta ga ba za ta iya zama da mijinta ba, to babu laifi ta mayar masa abin da ya kashe, sai su rabu. Wannan shi ne: Khul’u.


Sura: Suratul Baqara

Aya : 230

فَإِن طَلَّقَهَا فَلَا تَحِلُّ لَهُۥ مِنۢ بَعۡدُ حَتَّىٰ تَنكِحَ زَوۡجًا غَيۡرَهُۥۗ فَإِن طَلَّقَهَا فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِمَآ أَن يَتَرَاجَعَآ إِن ظَنَّآ أَن يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِۗ وَتِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِ يُبَيِّنُهَا لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

To idan ya sake sakin ta, ba za ta halatta a gare shi ba bayan haka har sai ta auri wani mijin daban[1]. To idan ya sake ta, to babu laifi gare su su koma, idan sun yi zaton cewa za su tsayar da dokokin Allah. Waxannan dokokin Allah ne, Yake bayyana su ga mutanen da suke da sani


1- Watau aure sahihi, kuma mijin ya tare da ita. Idan daga baya ya sake ta ta kammala iddarta, to za ta iya koma wa wajen mijinta na farko, amma bayan an sake xaura musu aure.


Sura: Suratul Baqara

Aya : 231

وَإِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَبَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمۡسِكُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ سَرِّحُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٖۚ وَلَا تُمۡسِكُوهُنَّ ضِرَارٗا لِّتَعۡتَدُواْۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ فَقَدۡ ظَلَمَ نَفۡسَهُۥۚ وَلَا تَتَّخِذُوٓاْ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ هُزُوٗاۚ وَٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَمَآ أَنزَلَ عَلَيۡكُم مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَٱلۡحِكۡمَةِ يَعِظُكُم بِهِۦۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ

Kuma idan kuka saki mata, sai wa’adin iddarsu ya kusa, (idan kuna son su) sai ku riqe su ta hanyar da ta dace (a shari’ance) ko kuma ku qyale su ta hanyar da ta dace (a shari’ance); kuma kada ku riqe su da nufin cutarwa don ku qetare iyakar (Ubangiji). Duk wanda ya aikata haka kuwa, to haqiqa ya zalunci kansa. Kuma kada ku mayar da ayoyin Allah abin izgili, kuma ku tuna ni’imar Allah da Ya yi muku da abin da Ya saukar muku na Littafi da Hikima Yana yi muku wa’azi da shi. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku sani lalle Allah Masanin komai ne



Sura: Suratul Baqara

Aya : 232

وَإِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَبَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا تَعۡضُلُوهُنَّ أَن يَنكِحۡنَ أَزۡوَٰجَهُنَّ إِذَا تَرَٰضَوۡاْ بَيۡنَهُم بِٱلۡمَعۡرُوفِۗ ذَٰلِكَ يُوعَظُ بِهِۦ مَن كَانَ مِنكُمۡ يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۗ ذَٰلِكُمۡ أَزۡكَىٰ لَكُمۡ وَأَطۡهَرُۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ

Kuma idan kun saki mata sai suka cika wa’adin iddarsu, to (ku waliyyai) kada ku hana su su auri mazajensu (na da) idan sun yi yarjejeniya a tsakaninsu ta hanyar da ta dace (a shari’a). Wannan (abin da aka ambata) shi ne wanda ake yin wa’azi da shi ga wanda ya kasance daga cikinku, yana imani da Allah da ranar lahira. Wannan shi ne abin da ya fi alheri a gare ku kuma ya fi tsarki; kuma Allah Shi ne Yake da sani, ku ba ku sani ba



Sura: Suratul Baqara

Aya : 233

۞وَٱلۡوَٰلِدَٰتُ يُرۡضِعۡنَ أَوۡلَٰدَهُنَّ حَوۡلَيۡنِ كَامِلَيۡنِۖ لِمَنۡ أَرَادَ أَن يُتِمَّ ٱلرَّضَاعَةَۚ وَعَلَى ٱلۡمَوۡلُودِ لَهُۥ رِزۡقُهُنَّ وَكِسۡوَتُهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ لَا تُكَلَّفُ نَفۡسٌ إِلَّا وُسۡعَهَاۚ لَا تُضَآرَّ وَٰلِدَةُۢ بِوَلَدِهَا وَلَا مَوۡلُودٞ لَّهُۥ بِوَلَدِهِۦۚ وَعَلَى ٱلۡوَارِثِ مِثۡلُ ذَٰلِكَۗ فَإِنۡ أَرَادَا فِصَالًا عَن تَرَاضٖ مِّنۡهُمَا وَتَشَاوُرٖ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِمَاۗ وَإِنۡ أَرَدتُّمۡ أَن تَسۡتَرۡضِعُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُمۡ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ إِذَا سَلَّمۡتُم مَّآ ءَاتَيۡتُم بِٱلۡمَعۡرُوفِۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Kuma iyaye mata za su shayar da ‘ya’yansu tsawon shekara biyu cikakku, ga wanda ya yi nufin ya cika wa’adi na shayarwa. Kuma wajibi ne a kan wanda aka yi wa haihuwa ya ciyar da su (mata masu shayarwa) da yi musu tufafi ta hanyar da aka saba. Ba a xora wa wani rai sai abin da zai iya. Kar a cutar da uwa saboda xanta, haka kuma kar a cutar da uba saboda xansa. Kuma kwatankwacin irin wannan ya wajaba kan magajinsa. To idan su biyun sun yi nufin yaye bisa ga yarjejeniya da shawara da junansu, to babu laifi a kansu. Kuma idan kun yi nufin nema wa ‘ya’yanku mai shayarwa, to babu laifi a kanku idan kun bayar da abin da ya kamata ta yadda aka saba. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku sani cewa, lalle Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne



Sura: Suratul Baqara

Aya : 234

وَٱلَّذِينَ يُتَوَفَّوۡنَ مِنكُمۡ وَيَذَرُونَ أَزۡوَٰجٗا يَتَرَبَّصۡنَ بِأَنفُسِهِنَّ أَرۡبَعَةَ أَشۡهُرٖ وَعَشۡرٗاۖ فَإِذَا بَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا فَعَلۡنَ فِيٓ أَنفُسِهِنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

Kuma waxanda suke mutuwa daga cikinku, suna kuma barin mata na aure, (su matan) za su yi zaman jira na wata huxu da kwana goma. To idan sun cika wa’adinsu, babu laifi a kanku (waliyyansu) cikin duk abin da suka aikata game da kawunansu ta hanyar da aka saba (a shari’a). Kuma Allah Mai cikakken sani ne game da abin da kuke aikatawa



Sura: Suratul Baqara

Aya : 235

وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا عَرَّضۡتُم بِهِۦ مِنۡ خِطۡبَةِ ٱلنِّسَآءِ أَوۡ أَكۡنَنتُمۡ فِيٓ أَنفُسِكُمۡۚ عَلِمَ ٱللَّهُ أَنَّكُمۡ سَتَذۡكُرُونَهُنَّ وَلَٰكِن لَّا تُوَاعِدُوهُنَّ سِرًّا إِلَّآ أَن تَقُولُواْ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗاۚ وَلَا تَعۡزِمُواْ عُقۡدَةَ ٱلنِّكَاحِ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ ٱلۡكِتَٰبُ أَجَلَهُۥۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ فَٱحۡذَرُوهُۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٞ

Kuma babu laifi a kanku game da abin da kuka yi wa mata jirwaye da shi na neman aurensu ko kuma kuka voye a cikin zukatanku, Allah Ya san cewa ku za ku riqa maganarsu, sai dai kar ku yi alqawari da su (na aure) a asirce, sai dai in za ku faxi zance wanda yake sananne a (shari’a). Kuma kada ku qulla igiyar aure (da mata masu takaba) har sai faralin idda ya cika wa’adinsa. Kuma ku sani lalle Allah Ya san abin da yake cikin zukatanku, don haka ku kiyaye Shi. Kuma ku sani lalle Allah Mai yawan gafara ne, Mai haquri



Sura: Suratul Baqara

Aya : 236

لَّا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ إِن طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ مَا لَمۡ تَمَسُّوهُنَّ أَوۡ تَفۡرِضُواْ لَهُنَّ فَرِيضَةٗۚ وَمَتِّعُوهُنَّ عَلَى ٱلۡمُوسِعِ قَدَرُهُۥ وَعَلَى ٱلۡمُقۡتِرِ قَدَرُهُۥ مَتَٰعَۢا بِٱلۡمَعۡرُوفِۖ حَقًّا عَلَى ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Babu laifi (sadaqi) a kanku idan kun saki mata, matuqar ba ku riga kun sadu da su ko kuma kun yanka musu sadaki sananne ba. Sai ku yi musu kyauta (ta kwantar da hankali); mai yalwa daidai yalwarsa; talaka ma daidai qarfinsa. (Wannan) wata kyauta ce (da za a bayar) ta hanyar da aka saba; haqqi ne a kan masu kyautatawa[1]


1- Allah ya yi umarni ga mijin wanda ya saki matarsa kafin ya tare da ita, lalle ya yi mata wata kyauta ta kwantar da hankali gwargwadon qarfinsa.


Sura: Suratul Baqara

Aya : 237

وَإِن طَلَّقۡتُمُوهُنَّ مِن قَبۡلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ وَقَدۡ فَرَضۡتُمۡ لَهُنَّ فَرِيضَةٗ فَنِصۡفُ مَا فَرَضۡتُمۡ إِلَّآ أَن يَعۡفُونَ أَوۡ يَعۡفُوَاْ ٱلَّذِي بِيَدِهِۦ عُقۡدَةُ ٱلنِّكَاحِۚ وَأَن تَعۡفُوٓاْ أَقۡرَبُ لِلتَّقۡوَىٰۚ وَلَا تَنسَوُاْ ٱلۡفَضۡلَ بَيۡنَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٌ

Idan kuwa kun sake su ne tun kafin ku sadu da su, alhalin kuma kun yanka musu sadaki, to sai (ku bayar) da rabin abin da kuka yanka, sai fa in su matan sun yi afuwa ko kuma wanda a hannunsa igiyar aure take ya yi afuwa[1]; kuma ku yi afuwa shi ya fi kusa ga taqawa. Kuma kada ku manta da kyautatawar da take tsakaninku. Lalle Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne


1- Wanda igiyar aure take hannusa, shi ne mijin. Yana iya yafe wa, ya bar mata duk sadakin baki xaya.


Sura: Suratul Baqara

Aya : 238

حَٰفِظُواْ عَلَى ٱلصَّلَوَٰتِ وَٱلصَّلَوٰةِ ٱلۡوُسۡطَىٰ وَقُومُواْ لِلَّهِ قَٰنِتِينَ

Ku kiyaye salloli da kuma salla mafificiya, kuma ku tsaya domin Allah kuna masu nutsuwa



Sura: Suratul Baqara

Aya : 239

فَإِنۡ خِفۡتُمۡ فَرِجَالًا أَوۡ رُكۡبَانٗاۖ فَإِذَآ أَمِنتُمۡ فَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ كَمَا عَلَّمَكُم مَّا لَمۡ تَكُونُواْ تَعۡلَمُونَ

To idan kuna cikin halin tsoro, sai ku yi salla kuna tafe da qafafuwanku ko a kan ababan hawanku. To idan kun amintu, sai ku ambaci Allah kamar yadda Ya sanar da ku abin da ba ku kasance kun sani ba



Sura: Suratul Baqara

Aya : 240

وَٱلَّذِينَ يُتَوَفَّوۡنَ مِنكُمۡ وَيَذَرُونَ أَزۡوَٰجٗا وَصِيَّةٗ لِّأَزۡوَٰجِهِم مَّتَٰعًا إِلَى ٱلۡحَوۡلِ غَيۡرَ إِخۡرَاجٖۚ فَإِنۡ خَرَجۡنَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِي مَا فَعَلۡنَ فِيٓ أَنفُسِهِنَّ مِن مَّعۡرُوفٖۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

Kuma waxanda suke rasuwa daga cikinku suke barin matan aure, (to za su yi) wasiyya ga matansu cewa, a jiyar da su daxi har zuwa shekara, ba tare da an fitar da su ba; to idan su suka fita da kansu, to babu laifi a kanku dangane da abin da suka aikata wa kansu na abin da yake sananne a shari’a. Kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima[1]


1- Wasu malamai suna ganin wannan aya an shafe ta da aya ta 234. Wasu kuma suna ganin umarni ne ga mazaje su yi wasiyya ga magadansu a kan su qale matansu su zauna a gidajensu tsawon shekara xaya, Wannan kuwa ya kasance ne kafin Allah ya shar’anta rabon gado, a inda ya ambaci kason mace daga dukiyar mijinta.