Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 151

أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ حَقّٗاۚ وَأَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٗا مُّهِينٗا

Waxannan su ne kafirai na haqiqa. Kuma Mun yi wa kafirai tanadin wata azaba mai wulaqantarwa



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 152

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ وَلَمۡ يُفَرِّقُواْ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّنۡهُمۡ أُوْلَـٰٓئِكَ سَوۡفَ يُؤۡتِيهِمۡ أُجُورَهُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Waxanda suka yi imani da Allah da manzanninsa, kuma ba su nuna bambanci tsakanin xaya daga cikinsu ba, waxannan (Allah) zai ba su ladansu. Allah kuma Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai yawan rahama



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 153

يَسۡـَٔلُكَ أَهۡلُ ٱلۡكِتَٰبِ أَن تُنَزِّلَ عَلَيۡهِمۡ كِتَٰبٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِۚ فَقَدۡ سَأَلُواْ مُوسَىٰٓ أَكۡبَرَ مِن ذَٰلِكَ فَقَالُوٓاْ أَرِنَا ٱللَّهَ جَهۡرَةٗ فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّـٰعِقَةُ بِظُلۡمِهِمۡۚ ثُمَّ ٱتَّخَذُواْ ٱلۡعِجۡلَ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ فَعَفَوۡنَا عَن ذَٰلِكَۚ وَءَاتَيۡنَا مُوسَىٰ سُلۡطَٰنٗا مُّبِينٗا

Ma’abota Littafi (Yahudawa da Nasara) suna tambayar ka cewa, ka saukar musu da wani cikakken littafi daga sama. To haqiqa da ma can sun tambayi Musa abin da ya fi wannan girma, da suka ce: “Ka nuna mana Allah a fili,” sai tsawa ta far musu a sanadiyyar zaluncinsu. Sannan kuma suka riqi xan maraqi abin bauta bayan hujjoji sun zo musu, sai Muka yi (musu) afuwa a kan haka. Kuma Muka bai wa Musa hujja bayyananniya



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 154

وَرَفَعۡنَا فَوۡقَهُمُ ٱلطُّورَ بِمِيثَٰقِهِمۡ وَقُلۡنَا لَهُمُ ٱدۡخُلُواْ ٱلۡبَابَ سُجَّدٗا وَقُلۡنَا لَهُمۡ لَا تَعۡدُواْ فِي ٱلسَّبۡتِ وَأَخَذۡنَا مِنۡهُم مِّيثَٰقًا غَلِيظٗا

Kuma Muka xaga dutsen Xuri a kansu don su karvi alqawarinsu, kuma Muka ce da su: “Ku shiga qofar (garin) a sunkuye.” Kuma Muka ce da su: “Kada ku qetare iyaka (ta kamun kifi) a ranar Asabar,” kuma Muka yi alqawari mai qarfi da su



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 155

فَبِمَا نَقۡضِهِم مِّيثَٰقَهُمۡ وَكُفۡرِهِم بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَقَتۡلِهِمُ ٱلۡأَنۢبِيَآءَ بِغَيۡرِ حَقّٖ وَقَوۡلِهِمۡ قُلُوبُنَا غُلۡفُۢۚ بَلۡ طَبَعَ ٱللَّهُ عَلَيۡهَا بِكُفۡرِهِمۡ فَلَا يُؤۡمِنُونَ إِلَّا قَلِيلٗا

To saboda warware alqawarinsu da kafircewarsu ga ayoyin Allah da kuma kashe wasu annabawan ba tare da wani laifi ba da kuma faxinsu cewa: “Zukatanmu a rufe suke.”A’a, ba haka ne ba, Allah ne Ya rufe su saboda kafircinsu, don haka ba za su yi imani ba sai xan kaxan



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 156

وَبِكُفۡرِهِمۡ وَقَوۡلِهِمۡ عَلَىٰ مَرۡيَمَ بُهۡتَٰنًا عَظِيمٗا

Kuma saboda kafircinsu da kuma wata babbar qarya da suka yi wa Maryamu[1]


1- Watau tuhumar da Yahudawa suka yi mata da cewa, wai zina ta yi ta haifi Annabi Isa ().


Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 157

وَقَوۡلِهِمۡ إِنَّا قَتَلۡنَا ٱلۡمَسِيحَ عِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ رَسُولَ ٱللَّهِ وَمَا قَتَلُوهُ وَمَا صَلَبُوهُ وَلَٰكِن شُبِّهَ لَهُمۡۚ وَإِنَّ ٱلَّذِينَ ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِ لَفِي شَكّٖ مِّنۡهُۚ مَا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٍ إِلَّا ٱتِّبَاعَ ٱلظَّنِّۚ وَمَا قَتَلُوهُ يَقِينَۢا

Da kuma faxarsu cewa: “Lalle mu mun kashe Almasihu Isa xan Maryamu Manzon Allah,” alhalin kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su gicciye shi ba, sai dai an kamanta musu (wani da shi ne)[1]. Kuma lalle waxanda suka yi savani game da shi (Annabi Isa) suna cikin shakka game da (kashe) shi, ba su da wani ilimi face bin zato. Kuma a haqiqanin gaskiya ba su kashe shi ba


1- Watau suka zaci shi ne Annabi Isa (), suka kama shi suka kashe.


Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 158

بَل رَّفَعَهُ ٱللَّهُ إِلَيۡهِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمٗا

Ba haka ba ne, Allah ya xaga shi zuwa gare Shi ne. kuma Allah Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 159

وَإِن مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ إِلَّا لَيُؤۡمِنَنَّ بِهِۦ قَبۡلَ مَوۡتِهِۦۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يَكُونُ عَلَيۡهِمۡ شَهِيدٗا

Kuma babu wani daga Ma’abota Littafi face sai ya yi imani da shi kafin mutuwarsa[1]; kuma a ranar tashin alqiyama zai zama mai ba da shaida a kansu


1- Watau lokacin da Annabi Isa () zai sauko qasa a qarshen zamani duk wani Bayahude ba Banasare sai ya yi imani da shi kafin mutuwar Annabi Isa ().


Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 160

فَبِظُلۡمٖ مِّنَ ٱلَّذِينَ هَادُواْ حَرَّمۡنَا عَلَيۡهِمۡ طَيِّبَٰتٍ أُحِلَّتۡ لَهُمۡ وَبِصَدِّهِمۡ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ كَثِيرٗا

To saboda zaluncin waxanda suka zama Yahudawa, Muka haramta musu daxaxan abubuwan da aka halatta musu, kuma saboda suna yawan hana mutane bin hanyar Allah



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 161

وَأَخۡذِهِمُ ٱلرِّبَوٰاْ وَقَدۡ نُهُواْ عَنۡهُ وَأَكۡلِهِمۡ أَمۡوَٰلَ ٱلنَّاسِ بِٱلۡبَٰطِلِۚ وَأَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ مِنۡهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا

Da kuma cin riba da suke yi, tare da cewa an hana su cin ta, da kuma yadda suke cin dukiyar mutane ta hanyar cuta, Mun kuwa yi tanadin azaba mai raxaxi ga kafirai daga cikinsu



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 162

لَّـٰكِنِ ٱلرَّـٰسِخُونَ فِي ٱلۡعِلۡمِ مِنۡهُمۡ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ يُؤۡمِنُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَۚ وَٱلۡمُقِيمِينَ ٱلصَّلَوٰةَۚ وَٱلۡمُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ أُوْلَـٰٓئِكَ سَنُؤۡتِيهِمۡ أَجۡرًا عَظِيمًا

Amma masu zurfin ilimi daga cikinsu da muminai, suna imani da abin da aka saukar maka da abin da aka saukar gabaninka; musamman ma masu tsayar da salla, da kuma masu bayar da zakka, kuma masu imani da Allah da ranar qarshe. Waxannan ba da jimawa ba za Mu ba su lada mai girma



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 163

۞إِنَّآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ كَمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ نُوحٖ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ مِنۢ بَعۡدِهِۦۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَعِيسَىٰ وَأَيُّوبَ وَيُونُسَ وَهَٰرُونَ وَسُلَيۡمَٰنَۚ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا

Lalle Mun yi maka wahayi irin wahayin da Muka yi wa Nuhu da kuma annabawan da suka biyo bayansa, kuma Mun yi wahayi ga Ibrahimu da Isma’ila da Ishaqa da Ya’aqubu da kuma jikokin (Ya’aqubu) da Isa da Ayyuba da Yunusa da Haruna da Sulaimanu; kuma Muka bai wa Dawuda littafin Zabura



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 164

وَرُسُلٗا قَدۡ قَصَصۡنَٰهُمۡ عَلَيۡكَ مِن قَبۡلُ وَرُسُلٗا لَّمۡ نَقۡصُصۡهُمۡ عَلَيۡكَۚ وَكَلَّمَ ٱللَّهُ مُوسَىٰ تَكۡلِيمٗا

(Muka) kuma aiko manzanni waxanda Muka ba ka labarinsu tun da farko, da waxansu manzannin daban da ba Mu ba ka labarinsu ba; kuma Allah Ya yi magana da Musa kai-tsaye



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 165

رُّسُلٗا مُّبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى ٱللَّهِ حُجَّةُۢ بَعۡدَ ٱلرُّسُلِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمٗا

Manzanni ne masu albishir kuma masu gargaxi, domin kada mutane su sami wata hujja a wurin Allah bayan aiko manzannin. Kuma Allah Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 166

لَّـٰكِنِ ٱللَّهُ يَشۡهَدُ بِمَآ أَنزَلَ إِلَيۡكَۖ أَنزَلَهُۥ بِعِلۡمِهِۦۖ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَشۡهَدُونَۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدًا

Amma Allah Yana shaida game da abin da Ya saukar maka; Ya saukar da shi ne da iliminsa; haka mala’iku ma suna shaidawa. Kuma Allah Ya isa Mai shaida



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 167

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ قَدۡ ضَلُّواْ ضَلَٰلَۢا بَعِيدًا

Lalle waxanda suka kafirta, kuma suka kange mutane daga hanyar Allah, haqiqa sun vace vata mai nisa



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 168

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَظَلَمُواْ لَمۡ يَكُنِ ٱللَّهُ لِيَغۡفِرَ لَهُمۡ وَلَا لِيَهۡدِيَهُمۡ طَرِيقًا

Lalle waxanda suka kafirta, kuma suka yi zalunci, Allah ba zai tava yi musu gafara ba, ba kuma zai shiryar da su wata hanya ta gari ba



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 169

إِلَّا طَرِيقَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٗا

Sai dai hanyar wutar Jahannama, suna masu dawwama a cikinta har abada. Yin hakan kuwa ya kasance abu ne mai sauqi a wajen Allah



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 170

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَكُمُ ٱلرَّسُولُ بِٱلۡحَقِّ مِن رَّبِّكُمۡ فَـَٔامِنُواْ خَيۡرٗا لَّكُمۡۚ وَإِن تَكۡفُرُواْ فَإِنَّ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا

Ya ku mutane, haqiqa Manzo ya zo muku da gaskiya daga wajen Ubangijinku, don haka ku yi imani shi ya fi alheri a gare ku. Idan kuwa kuka kafirce, to lalle abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa duk na Allah ne. kuma Allah Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai hikima



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 171

يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَا تَغۡلُواْ فِي دِينِكُمۡ وَلَا تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّۚ إِنَّمَا ٱلۡمَسِيحُ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ رَسُولُ ٱللَّهِ وَكَلِمَتُهُۥٓ أَلۡقَىٰهَآ إِلَىٰ مَرۡيَمَ وَرُوحٞ مِّنۡهُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦۖ وَلَا تَقُولُواْ ثَلَٰثَةٌۚ ٱنتَهُواْ خَيۡرٗا لَّكُمۡۚ إِنَّمَا ٱللَّهُ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ سُبۡحَٰنَهُۥٓ أَن يَكُونَ لَهُۥ وَلَدٞۘ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلٗا

Ya ku Ma’abota Littafi, kada ku wuce iyaka cikin addininku[1], kuma kada ku faxi wata magana game da Allah sai ta gaskiya. Almasihu Isa xan Maryamu Manzon Allah ne, kuma kalmarsa ce da ya jefa wa Maryamu, kuma Ruhi ne daga gare Shi; don haka ku yi imani da Allah da manzanninsa, kuma kada ku riqa cewa su uku ne. Ku daina shi ya fi alheri a gare ku. Allah Shi ne kaxai abin bauta da gaskiya, Xaya ne; Ya tsarkaka a ce Yana da xa. Kuma abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa nasa ne, kuma Allah Ya isa Abin dogaro


1- Watau kada su wuce iyaka wajen kuzuzuta lamarin Annabi Isa () har ta kai su ga cewa xan Allah ne.


Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 172

لَّن يَسۡتَنكِفَ ٱلۡمَسِيحُ أَن يَكُونَ عَبۡدٗا لِّلَّهِ وَلَا ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ ٱلۡمُقَرَّبُونَۚ وَمَن يَسۡتَنكِفۡ عَنۡ عِبَادَتِهِۦ وَيَسۡتَكۡبِرۡ فَسَيَحۡشُرُهُمۡ إِلَيۡهِ جَمِيعٗا

Almasihu ba zai tava qyamar ya zama bawan Allah ba, hakanan su ma mala’iku makusanta. Duk wanda yake qyamar bautar Allah, kuma suke girman kai, to zai tattara su gaba xaya zuwa gare Shi



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 173

فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فَيُوَفِّيهِمۡ أُجُورَهُمۡ وَيَزِيدُهُم مِّن فَضۡلِهِۦۖ وَأَمَّا ٱلَّذِينَ ٱسۡتَنكَفُواْ وَٱسۡتَكۡبَرُواْ فَيُعَذِّبُهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا وَلَا يَجِدُونَ لَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرٗا

To amma waxanda suka yi imani, kuma suka yi ayyuka nagari, to zai cika musu ladansu, kuma Ya qara musu daga falalarsa. Amma waxanda suka qyamaci bautar Allah kuwa, suka kuma yi girman kai, to zai azabtar da su azaba mai raxaxi, kuma ba za su tava samun wani masoyi ko mataimaki ba Allah ba



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 174

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَكُم بُرۡهَٰنٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكُمۡ نُورٗا مُّبِينٗا

Ya ku mutane, haqiqa hujja ta zo muku daga Ubangijinku, kuma Mun saukar muku wani haske mabayyani[1]


1- Watau Alqur’ani mai girma.


Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 175

فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَٱعۡتَصَمُواْ بِهِۦ فَسَيُدۡخِلُهُمۡ فِي رَحۡمَةٖ مِّنۡهُ وَفَضۡلٖ وَيَهۡدِيهِمۡ إِلَيۡهِ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا

To amma waxanda suka yi imani da Allah kuma suka yi garkuwa da Shi, to zai shigar da su cikin wata rahama tasa da kuma wata falala, kuma Ya shiryar da su tafarki madaidaici zuwa gare Shi



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 176

يَسۡتَفۡتُونَكَ قُلِ ٱللَّهُ يُفۡتِيكُمۡ فِي ٱلۡكَلَٰلَةِۚ إِنِ ٱمۡرُؤٌاْ هَلَكَ لَيۡسَ لَهُۥ وَلَدٞ وَلَهُۥٓ أُخۡتٞ فَلَهَا نِصۡفُ مَا تَرَكَۚ وَهُوَ يَرِثُهَآ إِن لَّمۡ يَكُن لَّهَا وَلَدٞۚ فَإِن كَانَتَا ٱثۡنَتَيۡنِ فَلَهُمَا ٱلثُّلُثَانِ مِمَّا تَرَكَۚ وَإِن كَانُوٓاْ إِخۡوَةٗ رِّجَالٗا وَنِسَآءٗ فَلِلذَّكَرِ مِثۡلُ حَظِّ ٱلۡأُنثَيَيۡنِۗ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ أَن تَضِلُّواْۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمُۢ

Suna neman ka yi musu fatawa, ka ce: “Allah ne zai yi muku fatawa game da kalala. Idan mutum ya mutu ba shi da xa ko ‘ya, amma yana da ‘yar’uwa mace, to za a ba ta rabin abin da ya bari. Shi kuwa zai gaje (dukiyar) ta gaba xaya idan ya kasance ba ta da xa ko ‘ya. Amma idan suka kasance mata ne su biyu, to suna da biyu bisa uku na abin da ya bari. Idan kuwa sun kasance ‘yan’uwa masu yawa maza da mata, to duk namiji xaya yana da rabon mata biyu.” Allah Yana bayyana muku wannan ne don kar ku vace. Kuma Allah Masanin komai ne