إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba
Tarayya :
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi ne Mabuwayi, Mai jin qai
كَذَّبَتۡ عَادٌ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Adawa (ma) sun qaryata manzanni[1]
1- Domin qaryata Annabi Hudu () daidai yake da qaryata duk manzannin Allah, saboda saqo iri xaya suke xauke da shi.
إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ هُودٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Lokacin da xan’uwansu Hudu ya ce da su: “Yanzu ba kwa riqa kiyaye dokokin (Allah) ba?
إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ
“Lalle ni Manzo ne amintacce gare ku
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni
وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
“Kuma ba na tambayar ku wani lada game da shi (isar da manzancin); ladana yana wajen Ubangijin talikai kawai
أَتَبۡنُونَ بِكُلِّ رِيعٍ ءَايَةٗ تَعۡبَثُونَ
“Yanzu kwa riqa yin dogayen gine-gine a kan tuddai kuna sharholiya?
وَتَتَّخِذُونَ مَصَانِعَ لَعَلَّكُمۡ تَخۡلُدُونَ
“Kuma ku riqa gina ganuwoyi da maka-makan gidaje kamar za ku dawwama?
وَإِذَا بَطَشۡتُم بَطَشۡتُمۡ جَبَّارِينَ
“Idan kuma kuka yi damqa sai kukan yi damqa da tsanani
وَٱتَّقُواْ ٱلَّذِيٓ أَمَدَّكُم بِمَا تَعۡلَمُونَ
“Kuma ku kiyaye dokokin (Allah) wanda Ya ni’imta ku da abin da kuka sani
أَمَدَّكُم بِأَنۡعَٰمٖ وَبَنِينَ
“Ya ni’imta ku da dabbobin ni’ima da ‘ya’ya
وَجَنَّـٰتٖ وَعُيُونٍ
“Da kuma gonakai da idanuwan ruwa
إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ
“Lalle ni ina jiye muku tsoron azabar wani yini mai girma.”
قَالُواْ سَوَآءٌ عَلَيۡنَآ أَوَعَظۡتَ أَمۡ لَمۡ تَكُن مِّنَ ٱلۡوَٰعِظِينَ
Suka ce: “Mu duk xaya ne a wajenmu; ko ka yi wa’azi ko kuwa kada ka zamanto daga masu wa’azi
إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا خُلُقُ ٱلۡأَوَّلِينَ
“Wannan ba wani abu ba ne in ban da halayyar mutanen farko
وَمَا نَحۡنُ بِمُعَذَّبِينَ
“Mu kuma ba waxanda za a yi wa azaba ba ne.”
فَكَذَّبُوهُ فَأَهۡلَكۡنَٰهُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Sai suka qaryata shi, sannan Muka hallaka su. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba
كَذَّبَتۡ ثَمُودُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Samudawa sun qaryata manzanni[1]
1- Domin qaryata Annabi Salihu () daidai yake da qaryata duk manzannin Allah, saboda saqo iri xaya suke xauke da shi.
إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ صَٰلِحٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Lokacin da xan’uwansu Salihu ya ce da su: “Yanzu ba kwa yi taqawa ba?
أَتُتۡرَكُونَ فِي مَا هَٰهُنَآ ءَامِنِينَ
“Yanzu (zatonku) za a bar ku ne cikin abin da yake a nan (duniya) cikin kwanciyar hankali?
فِي جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٖ
“(Watau) a cikin gonaki da idandunan ruwa?
وَزُرُوعٖ وَنَخۡلٖ طَلۡعُهَا هَضِيمٞ
“Da shuke-shuke da dabinai masu taushin ‘ya’ya?
وَتَنۡحِتُونَ مِنَ ٱلۡجِبَالِ بُيُوتٗا فَٰرِهِينَ
“Kuma kuna fafe duwatsu kuna yin gidaje kuna masu nuna qwarewa?