مَا ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ مِن وَلَدٖ وَمَا كَانَ مَعَهُۥ مِنۡ إِلَٰهٍۚ إِذٗا لَّذَهَبَ كُلُّ إِلَٰهِۭ بِمَا خَلَقَ وَلَعَلَا بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ
Allah bai riqi wani xa ba, kuma babu wani abin bauta tare da Shi. (Da ko haka ta faru) to da kowanne abin bauta ya kevanta da abin da ya halitta, da kuma wani ya yi rinjaye a kan wani. Allah Ya tsarkaka daga abin da suke sifanta (Shi da shi)
عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ فَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Shi ne Masanin voye da sarari, to Ya xaukaka daga abin da suke shirka (da Shi)
قُل رَّبِّ إِمَّا تُرِيَنِّي مَا يُوعَدُونَ
Ka ce: “Ubangijina, idan Ka nuna min abin da ake yi musu alqawari da shi (na azaba)
رَبِّ فَلَا تَجۡعَلۡنِي فِي ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ
“Ubangijina, kada Ka sanya ni cikin mutane azzalumai.”
وَإِنَّا عَلَىٰٓ أَن نُّرِيَكَ مَا نَعِدُهُمۡ لَقَٰدِرُونَ
Mu kuma lalle Masu iko ne a kan Mu nuna maka abin da Muke musu alkawari
ٱدۡفَعۡ بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ ٱلسَّيِّئَةَۚ نَحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَصِفُونَ
Ka ingije mummunan abu da wanda ya fi kyau. Mu ne Muka fi sanin abin da suke siffata (ka da shi)
وَقُل رَّبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنۡ هَمَزَٰتِ ٱلشَّيَٰطِينِ
Kuma ka ce: “Ubangijina, ina neman tsarinka daga waswasin shaixanu
وَأَعُوذُ بِكَ رَبِّ أَن يَحۡضُرُونِ
“Ina kuma neman tsarinka Ubangijina kar su zo min.”
حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَ أَحَدَهُمُ ٱلۡمَوۡتُ قَالَ رَبِّ ٱرۡجِعُونِ
Har sai idan da mutuwa ta zo wa xayansu zai ce: “Ubangijina, Ku mai da ni (duniya) mana
لَعَلِّيٓ أَعۡمَلُ صَٰلِحٗا فِيمَا تَرَكۡتُۚ كَلَّآۚ إِنَّهَا كَلِمَةٌ هُوَ قَآئِلُهَاۖ وَمِن وَرَآئِهِم بَرۡزَخٌ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ
“Don in yi aiki na gari game da abin da na bari (a rayuwata).” Ina! Lalle wannan kalma ce da yake faxin ta (da bakinsa). A gabansu kuwa akwai shamaki har zuwa ranar tashinsu
فَإِذَا نُفِخَ فِي ٱلصُّورِ فَلَآ أَنسَابَ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَئِذٖ وَلَا يَتَسَآءَلُونَ
Sannan idan aka busa qaho to fa babu wata dangantaka (mai amfani) a tsakaninsu a wannan ranar, kuma ba za su tambayi juna ba
فَمَن ثَقُلَتۡ مَوَٰزِينُهُۥ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
To waxanda ma’aunansu suka yi nauyi waxannan su ne masu babban rabo
وَمَنۡ خَفَّتۡ مَوَٰزِينُهُۥ فَأُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فِي جَهَنَّمَ خَٰلِدُونَ
Waxanda kuwa ma’aunansu suka yi sakayau waxannan su ne waxanda suka yi asarar kawunansu, suna masu dawwama a cikin (wutar) Jahannama
تَلۡفَحُ وُجُوهَهُمُ ٱلنَّارُ وَهُمۡ فِيهَا كَٰلِحُونَ
(Wutar) tana qona fuskokinsu alhali kuwa suna ciccije haqoransu a cikinta
أَلَمۡ تَكُنۡ ءَايَٰتِي تُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ فَكُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ
Yanzu ayoyina ba su zamanto ana karanta muku su ba, sai ya zamana kuna qaryata su?
قَالُواْ رَبَّنَا غَلَبَتۡ عَلَيۡنَا شِقۡوَتُنَا وَكُنَّا قَوۡمٗا ضَآلِّينَ
Suka ce: “Ya Ubangijinmu, tsiyarmu ce ta rinjaye mu, mun kuma zamo mutane vatattu
رَبَّنَآ أَخۡرِجۡنَا مِنۡهَا فَإِنۡ عُدۡنَا فَإِنَّا ظَٰلِمُونَ
“Ya Ubangijinmu, Ka fitar da mu daga cikinta, to idan muka sake, to lalle mu azzalumai ne.”
قَالَ ٱخۡسَـُٔواْ فِيهَا وَلَا تُكَلِّمُونِ
Ya ce: “Ku yi min shiru, kada kuwa ku qara yi min magana a cikinta
إِنَّهُۥ كَانَ فَرِيقٞ مِّنۡ عِبَادِي يَقُولُونَ رَبَّنَآ ءَامَنَّا فَٱغۡفِرۡ لَنَا وَٱرۡحَمۡنَا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلرَّـٰحِمِينَ
“Lalle yadda lamarin yake, wata qungiya daga bayina sun kasance suna cewa: “Ya Ubangijinmu, mun yi imani, sai Ka gafarta mana, kuma Ka ji qan mu, Kai ne kuwa Fiyayyen masu jin qai
فَٱتَّخَذۡتُمُوهُمۡ سِخۡرِيًّا حَتَّىٰٓ أَنسَوۡكُمۡ ذِكۡرِي وَكُنتُم مِّنۡهُمۡ تَضۡحَكُونَ
“Sai kuka xauke su ababen yi wa izgili, har suka mantar da ku ambatona kuka kuma kasance kuna yi musu dariya
إِنِّي جَزَيۡتُهُمُ ٱلۡيَوۡمَ بِمَا صَبَرُوٓاْ أَنَّهُمۡ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ
“Lalle Ni Na saka musu a yau saboda haqurinsu. Lalle kuma su ne marabauta.”
قَٰلَ كَمۡ لَبِثۡتُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ عَدَدَ سِنِينَ
Ya ce: “Zaman shekara nawa kuka yi a bayan qasa?”
قَالُواْ لَبِثۡنَا يَوۡمًا أَوۡ بَعۡضَ يَوۡمٖ فَسۡـَٔلِ ٱلۡعَآدِّينَ
Suka ce: “Mun zauna ne yini xaya ko rabin yini, sai Ka tambayi (mala’iku) masu lissafin (kwanaki)
قَٰلَ إِن لَّبِثۡتُمۡ إِلَّا قَلِيلٗاۖ لَّوۡ أَنَّكُمۡ كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Ya ce: “Ai ba ku zauna ba sai xan lokaci qanqani (dangane da zaman lahira), da a ce kun kasance kun san da haka.”
أَفَحَسِبۡتُمۡ أَنَّمَا خَلَقۡنَٰكُمۡ عَبَثٗا وَأَنَّكُمۡ إِلَيۡنَا لَا تُرۡجَعُونَ
(Allah Ya ce da su): “Ko kuna tsammani ne cewa Mun halicce ku ne ba manufa kuma ku ba za a dawo da ku gare Mu ba?”
فَتَعَٰلَى ٱللَّهُ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡحَقُّۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡكَرِيمِ
To Allah Sarki na gaskiya Ya xaukaka; babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, (Shi ne) Ubangijin Al’arshi mai girma
وَمَن يَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ لَا بُرۡهَٰنَ لَهُۥ بِهِۦ فَإِنَّمَا حِسَابُهُۥ عِندَ رَبِّهِۦٓۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلۡكَٰفِرُونَ
Duk wanda ya bauta wa wani abin bauta tare da Allah ba da wata hujja ba game da (wannan bautar), to sakamakonsa wajen Ubangijinsa kawai yake. Lalle su dai kafirai ba za su rabauta ba
وَقُل رَّبِّ ٱغۡفِرۡ وَٱرۡحَمۡ وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلرَّـٰحِمِينَ
Kuma ka ce: “Ya Ubangijina Ka gafarta (mana) kuma Ka ji qan mu, Kai ne kuwa Fiyayyen masu jin qai.”