Sura: Suratul Hijr

Aya : 91

ٱلَّذِينَ جَعَلُواْ ٱلۡقُرۡءَانَ عِضِينَ

(Su ne) waxanda suka mai da Alqur’ani kashi-kashi[1]


1- Watau suka yi imani da wani vangare suka kafirce wa wani vangare.


Sura: Suratul Hijr

Aya : 92

فَوَرَبِّكَ لَنَسۡـَٔلَنَّهُمۡ أَجۡمَعِينَ

(Na rantse) da Ubangijinka tabbas za Mu tambaye su gaba xaya



Sura: Suratul Hijr

Aya : 93

عَمَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Game da abin da suka kasance suna aikatawa



Sura: Suratul Hijr

Aya : 94

فَٱصۡدَعۡ بِمَا تُؤۡمَرُ وَأَعۡرِضۡ عَنِ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

To ka tsage gaskiyar abin da aka umarce ka da shi, ka kuma kawar da kanka daga mushirikai



Sura: Suratul Hijr

Aya : 95

إِنَّا كَفَيۡنَٰكَ ٱلۡمُسۡتَهۡزِءِينَ

Lalle Mu Mun isar maka (sharrin) masu izgili



Sura: Suratul Hijr

Aya : 96

ٱلَّذِينَ يَجۡعَلُونَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۚ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ

(Su ne) waxanda suke sanya wani abin bauta tare da Allah. Ba ko da daxewa ba za su sani



Sura: Suratul Hijr

Aya : 97

وَلَقَدۡ نَعۡلَمُ أَنَّكَ يَضِيقُ صَدۡرُكَ بِمَا يَقُولُونَ

Haqiqa kuma Muna sane da cewa qirjinka yana qunci game da abin da suke faxa



Sura: Suratul Hijr

Aya : 98

فَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ وَكُن مِّنَ ٱلسَّـٰجِدِينَ

To sai ka yi tasbihi tare da godiyar Ubangijinka, ka kuma zamo cikin masu sujjada



Sura: Suratul Hijr

Aya : 99

وَٱعۡبُدۡ رَبَّكَ حَتَّىٰ يَأۡتِيَكَ ٱلۡيَقِينُ

Ka kuma bauta wa Ubangijinka har yaqini ya zo maka (wato mutuwa)