Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 61

وَإِذَا جَآءُوكُمۡ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا وَقَد دَّخَلُواْ بِٱلۡكُفۡرِ وَهُمۡ قَدۡ خَرَجُواْ بِهِۦۚ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا كَانُواْ يَكۡتُمُونَ

Kuma idan suka zo muku, sai su ce: “Mun yi imani”, alhali kuwa haqiqa sun shigo da kafirci ne, kuma haqiqa sun fita da shi ne. Allah kuwa Shi ne Mafi sanin abin da suka kasance suna voyewa



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 62

وَتَرَىٰ كَثِيرٗا مِّنۡهُمۡ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِ وَأَكۡلِهِمُ ٱلسُّحۡتَۚ لَبِئۡسَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Kuma za ka ga yawancinsu suna yin gaggawa wajen aikin savo da qetare iyaka da kuma cin haramun. Lalle tir da abin da suka kasance suna aikatawa



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 63

لَوۡلَا يَنۡهَىٰهُمُ ٱلرَّبَّـٰنِيُّونَ وَٱلۡأَحۡبَارُ عَن قَوۡلِهِمُ ٱلۡإِثۡمَ وَأَكۡلِهِمُ ٱلسُّحۡتَۚ لَبِئۡسَ مَا كَانُواْ يَصۡنَعُونَ

Me ya hana malamansu na Allah da masanansu ba su kwave su daga yin maganar savo da cin haram ba? Tir da abin da suka kasance suna aikatawa



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 64

وَقَالَتِ ٱلۡيَهُودُ يَدُ ٱللَّهِ مَغۡلُولَةٌۚ غُلَّتۡ أَيۡدِيهِمۡ وَلُعِنُواْ بِمَا قَالُواْۘ بَلۡ يَدَاهُ مَبۡسُوطَتَانِ يُنفِقُ كَيۡفَ يَشَآءُۚ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُم مَّآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ طُغۡيَٰنٗا وَكُفۡرٗاۚ وَأَلۡقَيۡنَا بَيۡنَهُمُ ٱلۡعَدَٰوَةَ وَٱلۡبَغۡضَآءَ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ كُلَّمَآ أَوۡقَدُواْ نَارٗا لِّلۡحَرۡبِ أَطۡفَأَهَا ٱللَّهُۚ وَيَسۡعَوۡنَ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَسَادٗاۚ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

Kuma Yahudawa suka ce: “Hannun Allah a ququnce yake.”[1] To an ququnce hannayensu, kuma an la’ance su sakamakon abin da suka faxa. Kuma ba haka ba ne. Hannayensa a shimfixe suke; Yana ciyarwa yadda Ya ga dama. Kuma abin da aka saukar maka daga wajen Ubangijinka lalle yana daxa wa yawancinsu shisshigi da kafirci. Kuma Mun jefa gaba da qiyayya a tsakankaninsu har zuwa ranar tashin alqiyama. Duk lokacin da suka yi yunqurin rura wutar yaqi, sai Allah Ya bice ta; kuma suna masu tafiya a bayan qasa suna aikata varna. Allah kuwa ba Ya son mavarnata


1- watau suna nufin ba ya kyauta. Allah () ya tsarkaka daga wannan mummunar magana tasu.


Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 65

وَلَوۡ أَنَّ أَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ ءَامَنُواْ وَٱتَّقَوۡاْ لَكَفَّرۡنَا عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَلَأَدۡخَلۡنَٰهُمۡ جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ

Kuma in da a ce waxanda aka bai wa Littafi sun yi imani, kuma sun kiyaye dokokin Allah, to lalle da Mun kankare musu zunubansu, kuma lalle da Mun shigar da su gidajen Aljanna na ni’ima



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 66

وَلَوۡ أَنَّهُمۡ أَقَامُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِم مِّن رَّبِّهِمۡ لَأَكَلُواْ مِن فَوۡقِهِمۡ وَمِن تَحۡتِ أَرۡجُلِهِمۚ مِّنۡهُمۡ أُمَّةٞ مُّقۡتَصِدَةٞۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ سَآءَ مَا يَعۡمَلُونَ

Kuma da a ce sun tsaya a kan aiki da Attaura da Linjila da kuma abin da aka saukar musu daga Ubangijinsu, lalle da sun ci daga samansu da kuma qarqashin qafafunsu. Daga cikinsu akwai wata al’umma madaidaiciya, (amma) kuma mafi yawa daga cikinsu, irin abin da suke aikatawa ya munana (matuqa)



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 67

۞يَـٰٓأَيُّهَا ٱلرَّسُولُ بَلِّغۡ مَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَۖ وَإِن لَّمۡ تَفۡعَلۡ فَمَا بَلَّغۡتَ رِسَالَتَهُۥۚ وَٱللَّهُ يَعۡصِمُكَ مِنَ ٱلنَّاسِۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Ya kai wannan Manzo, ka isar da abin da aka saukar maka daga Ubangijinka; idan kuwa ba ka yi ba, to ba ka isar da saqonsa ba. Allah kuwa Shi ne Yake kare ka daga (sharrin) mutane. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutanen da suke kafirai



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 68

قُلۡ يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَسۡتُمۡ عَلَىٰ شَيۡءٍ حَتَّىٰ تُقِيمُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكُم مِّن رَّبِّكُمۡۗ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُم مَّآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ طُغۡيَٰنٗا وَكُفۡرٗاۖ فَلَا تَأۡسَ عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Ka ce: “Ya ku Ma’abota Littafi, ba kwa kan wani abu (na addinin gaskiya), har sai kun tsaya a kan yin aiki da Attaura da Linjila da kuma abin da aka saukar muku daga wajen Ubangijinku.” Kuma abin da ake saukar maka daga Ubangijinka tabbas yana qara wa yawancinsu shisshigi da kafirci. Don haka kada ka yi baqin ciki dangane da (abin da yake samun) mutane kafirai



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 69

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلصَّـٰبِـُٔونَ وَٱلنَّصَٰرَىٰ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Lalle waxanda suka yi imani da waxanda suke Yahudawa da Sabi’awa da Nasara, duk wanda ya yi imani da Allah da ranar qarshe, kuma ya yi aiki nagari, to babu jin tsoro a tattare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 70

لَقَدۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ وَأَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهِمۡ رُسُلٗاۖ كُلَّمَا جَآءَهُمۡ رَسُولُۢ بِمَا لَا تَهۡوَىٰٓ أَنفُسُهُمۡ فَرِيقٗا كَذَّبُواْ وَفَرِيقٗا يَقۡتُلُونَ

Lalle haqiqa Mun xauki alqawari daga Bani-Isra’ila, kuma Muka aika musu da manzanni. Duk sa’adda wani manzo ya zo musu da abin da zukatansu ba sa so, sai su qaryata waxansu kuma su riqa kashe waxansu



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 71

وَحَسِبُوٓاْ أَلَّا تَكُونَ فِتۡنَةٞ فَعَمُواْ وَصَمُّواْ ثُمَّ تَابَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ ثُمَّ عَمُواْ وَصَمُّواْ كَثِيرٞ مِّنۡهُمۡۚ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِمَا يَعۡمَلُونَ

Kuma sun zaci cewa, babu wata fitina da za ta auku, sai suka makance kuma suka kurumce, sannan Allah Ya karvi tubansu, sannan kuma da yawa daga cikinsu suka sake makancewa da kurumcewa. Allah kuma Mai ganin abin da suke aikatawa ne



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 72

لَقَدۡ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ مَرۡيَمَۖ وَقَالَ ٱلۡمَسِيحُ يَٰبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبَّكُمۡۖ إِنَّهُۥ مَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدۡ حَرَّمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ ٱلۡجَنَّةَ وَمَأۡوَىٰهُ ٱلنَّارُۖ وَمَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِنۡ أَنصَارٖ

Lalle haqiqa waxanda suka ce: “Lalle Allah Shi ne Almasihu xan Maryamu” sun kafirta. Shi kuwa Almasihu cewa ya yi: “Ya ku Bani-Isra’ila, ku bauta wa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku. Lalle yadda al’amarin yake, duk wanda ya yi shirka da Allah, to haqiqa Allah Ya haramta masa shiga Aljanna, kuma makomarsa ita ce wuta, kuma azzalumai ba su da wasu mataimaka.”



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 73

لَّقَدۡ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ ثَالِثُ ثَلَٰثَةٖۘ وَمَا مِنۡ إِلَٰهٍ إِلَّآ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۚ وَإِن لَّمۡ يَنتَهُواْ عَمَّا يَقُولُونَ لَيَمَسَّنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ

Lalle haqiqa waxannan da suka ce: “Lalle Allah Shi ne na cikon (alloli) uku,”[1] sun kafirta. Babu kuwa wani abin bautawa na gaskiya, sai abin bauta Xaya tal. Idan ba su bar abin da suke faxa xin nan ba, lalle azaba mai raxaxi za ta shafi waxanda suka kafirta daga cikinsu


1- Ana nufin aqidar Nasara da suke cewa, abu uku ne suka haxu suka zama Allah, watau Isa da mahaifiyarsa Maryamu da kuma Allah.


Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 74

أَفَلَا يَتُوبُونَ إِلَى ٱللَّهِ وَيَسۡتَغۡفِرُونَهُۥۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Shin yanzu ba za su tuba zuwa ga Allah ba, kuma su nemi gafararsa? Allah kuwa Mai gafara ne, Mai jin qai



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 75

مَّا ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ مَرۡيَمَ إِلَّا رَسُولٞ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِ ٱلرُّسُلُ وَأُمُّهُۥ صِدِّيقَةٞۖ كَانَا يَأۡكُلَانِ ٱلطَّعَامَۗ ٱنظُرۡ كَيۡفَ نُبَيِّنُ لَهُمُ ٱلۡأٓيَٰتِ ثُمَّ ٱنظُرۡ أَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ

Shi fa Almasihu xan Maryamu bai zamo ba face Manzo, wanda haqiqa manzanni sun shuxe kafinsa. Mahaifiyarsa kuma Siddiqa ce; shi da ita sun kasance suna cin abinci. Duba ka ga yadda Muke bayyana musu ayoyi, sannan ka sake dubawa, ta yaya ake kautar da su?



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 76

قُلۡ أَتَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَمۡلِكُ لَكُمۡ ضَرّٗا وَلَا نَفۡعٗاۚ وَٱللَّهُ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Ka ce: “Shin yanzu kwa riqa bauta wa wani ba Allah ba, wanda ba ya mallakar cutarwa ko amfanarwa a gare ku; Shi kuwa Allah Shi ne Mai ji, kuma Masani?”



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 77

قُلۡ يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَا تَغۡلُواْ فِي دِينِكُمۡ غَيۡرَ ٱلۡحَقِّ وَلَا تَتَّبِعُوٓاْ أَهۡوَآءَ قَوۡمٖ قَدۡ ضَلُّواْ مِن قَبۡلُ وَأَضَلُّواْ كَثِيرٗا وَضَلُّواْ عَن سَوَآءِ ٱلسَّبِيلِ

Ka ce: “Ya ku ma’abota Littafi, kada ku zurfafa a ckin lamarin addiniku (ku qara) abin da ba gaskiya ba, kuma kada ku bi soye-soyen zukatan waxansu mutanen da suka riga suka vata tun a da can, kuma sun vatar da mutane da yawa, kuma sun vace daga madaidaiciyar hanya.”



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 78

لُعِنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۢ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ عَلَىٰ لِسَانِ دَاوُۥدَ وَعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعۡتَدُونَ

An la’anci waxanda suka kafirta daga cikin Bani-Isra’ila a bisa harshen Dawuda da kuma Isa xan Maryamu. Hakan kuwa saboda abin da suka riqa yi ne na savo, kuma sun kasance suna qetare iyaka



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 79

كَانُواْ لَا يَتَنَاهَوۡنَ عَن مُّنكَرٖ فَعَلُوهُۚ لَبِئۡسَ مَا كَانُواْ يَفۡعَلُونَ

Sun kasance ba sa hana junansu wani mummunan aikin da suka yi. Lalle tir da irin abin da suka kasance suna aikatawa



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 80

تَرَىٰ كَثِيرٗا مِّنۡهُمۡ يَتَوَلَّوۡنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ لَبِئۡسَ مَا قَدَّمَتۡ لَهُمۡ أَنفُسُهُمۡ أَن سَخِطَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ وَفِي ٱلۡعَذَابِ هُمۡ خَٰلِدُونَ

Za ka ga yawancinsu suna nuna qauna ga waxanda suka kafirta. Lalle tir da irin abin da kawunansu suka gabatar, don kuwa Allah Ya yi fushi da su, kuma su masu dawwama ne cikin azaba



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 81

وَلَوۡ كَانُواْ يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلنَّبِيِّ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مَا ٱتَّخَذُوهُمۡ أَوۡلِيَآءَ وَلَٰكِنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُمۡ فَٰسِقُونَ

Kuma da sun kasance suna imani da Allah da Annabi da abin da aka saukar masa, da ba su riqe su a matsayin masoya ba, sai dai kuma yawancinsu fasiqai ne



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 82

۞لَتَجِدَنَّ أَشَدَّ ٱلنَّاسِ عَدَٰوَةٗ لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱلۡيَهُودَ وَٱلَّذِينَ أَشۡرَكُواْۖ وَلَتَجِدَنَّ أَقۡرَبَهُم مَّوَدَّةٗ لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّا نَصَٰرَىٰۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّ مِنۡهُمۡ قِسِّيسِينَ وَرُهۡبَانٗا وَأَنَّهُمۡ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ

Tabbas lalle za ka samu cewa, mutanen da suka fi tsananin gaba da waxanda suka yi imani, su ne Yahudawa da waxanda suke mushirikai. Kuma tabbas lalle za ka sami waxanda suka fi kusanci wajen nuna qauna ga waxanda suka yi imani, su ne waxanda suka ce: “Lalle mu Nasara ne.” Wannan kuwa saboda a cikinsu akwai malamai da masu yawan ibada, don kuma lalle su ba sa yin girman kai



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 83

وَإِذَا سَمِعُواْ مَآ أُنزِلَ إِلَى ٱلرَّسُولِ تَرَىٰٓ أَعۡيُنَهُمۡ تَفِيضُ مِنَ ٱلدَّمۡعِ مِمَّا عَرَفُواْ مِنَ ٱلۡحَقِّۖ يَقُولُونَ رَبَّنَآ ءَامَنَّا فَٱكۡتُبۡنَا مَعَ ٱلشَّـٰهِدِينَ

Kuma idan sun ji abin da aka saukar wa wannan Manzo, za ka ga idanunsu suna zubar da hawaye, saboda abin da suka gane na gaskiya; suna cewa: “Ya Ubangijinmu, mun yi imani, don haka Ka rubuta mu cikin masu shaidawa



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 84

وَمَا لَنَا لَا نُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَمَا جَآءَنَا مِنَ ٱلۡحَقِّ وَنَطۡمَعُ أَن يُدۡخِلَنَا رَبُّنَا مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلصَّـٰلِحِينَ

“Kuma me muke da shi da ba za mu yi imani da Allah da abin da ya zo mana na gaskiya ba, muna kuwa sa rai Ubangijinmu Ya shigar da mu cikin salihan bayi?”



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 85

فَأَثَٰبَهُمُ ٱللَّهُ بِمَا قَالُواْ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Sai Allah Ya saka musu saboda abin da suka faxa, da gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dauwama a cikinsu, kuma wannan shi ne sakamakon masu kyautatawa



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 86

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَحِيمِ

Waxanda kuwa suka kafirta, kuma suka qaryata ayoyinmu, waxannan su ne ‘yan wuta



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 87

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُحَرِّمُواْ طَيِّبَٰتِ مَآ أَحَلَّ ٱللَّهُ لَكُمۡ وَلَا تَعۡتَدُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُعۡتَدِينَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku haramta kyawawan abubuwan da Allah Ya halatta muku, kuma kada ku qetare iyaka. Lalle Allah ba Ya son masu qetare iyaka



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 88

وَكُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ حَلَٰلٗا طَيِّبٗاۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِيٓ أَنتُم بِهِۦ مُؤۡمِنُونَ

Kuma ku ci daga abin da Allah Ya arzuta ku da shi, wanda yake halal, mai daxi. Kuma ku kiyaye dokokin Allah Wanda kuke yin imani da Shi



Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 89

لَا يُؤَاخِذُكُمُ ٱللَّهُ بِٱللَّغۡوِ فِيٓ أَيۡمَٰنِكُمۡ وَلَٰكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا عَقَّدتُّمُ ٱلۡأَيۡمَٰنَۖ فَكَفَّـٰرَتُهُۥٓ إِطۡعَامُ عَشَرَةِ مَسَٰكِينَ مِنۡ أَوۡسَطِ مَا تُطۡعِمُونَ أَهۡلِيكُمۡ أَوۡ كِسۡوَتُهُمۡ أَوۡ تَحۡرِيرُ رَقَبَةٖۖ فَمَن لَّمۡ يَجِدۡ فَصِيَامُ ثَلَٰثَةِ أَيَّامٖۚ ذَٰلِكَ كَفَّـٰرَةُ أَيۡمَٰنِكُمۡ إِذَا حَلَفۡتُمۡۚ وَٱحۡفَظُوٓاْ أَيۡمَٰنَكُمۡۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Allah ba zai kama ku da yasassun rantse-rantsenku ba[1], sai dai Yana kama ku ne da laifin abin da kuka qudurce na rantsuwa[2]; to kaffararsa ita ce ciyar da miskinai goma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyalinku ko kuma tufatar da su ko ‘yantar da bawa; wanda kuwa bai sami iko ba, to sai ya yi azumin kwana uku. Wannan shi ne kaffarar rantsuwarku, in kun yi rantsuwa. Kuma ku kiyaye rantse-rantsenku. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa don ku zamo masu godiya


1- Yasasshiyar rantsuwa ita ce rantsuwar da mutum yake yi ba da niyya ba.


2- Watau yana kama mutum da rantsuwar da ya qudurci niyya a kanta.


Sura: Suratul Ma’ida

Aya : 90

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡخَمۡرُ وَٱلۡمَيۡسِرُ وَٱلۡأَنصَابُ وَٱلۡأَزۡلَٰمُ رِجۡسٞ مِّنۡ عَمَلِ ٱلشَّيۡطَٰنِ فَٱجۡتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, ita dai giya da caca da gumaka da kibau na neman sa’a[1], ba komai ba ne face qazanta daga aikin Shaixan, don haka ku nisance su domin ku sami rabauta.[2]


1- A jahiliyya balarabe idan zai yi tafiya ko zai yi wani aiki, sai ya xauko wasu kibiyoyi uku, xaya an rubuta ‘aikata’, xaya kuma ‘kada ka aikata’, ta uku kuma ba a rubuta komai a kanta ba, sai ya karkaxa su sannan ya zavi xaya don ya gane sa’arsa ko rashinta.


2- Da wannan ayar Allah () ya haramta wa Musulmi shan giya da kasuwancinta.