قَالُواْ رَبَّنَا مَن قَدَّمَ لَنَا هَٰذَا فَزِدۡهُ عَذَابٗا ضِعۡفٗا فِي ٱلنَّارِ
Sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, duk wanda ya kawo mana wannan (sakamakon) to Ka qara masa ninkin azaba a cikin wuta.”
وَقَالُواْ مَا لَنَا لَا نَرَىٰ رِجَالٗا كُنَّا نَعُدُّهُم مِّنَ ٱلۡأَشۡرَارِ
Suka kuma ce: “Me ya sa ne ba ma ganin wasu mazaje[1] da muka kasance muna lissafa su cikin ashararai?
1- Suna nufin muminai waxanda suka riqa yi wa izgili a duniya, suna musu kallon vatattu.
أَتَّخَذۡنَٰهُمۡ سِخۡرِيًّا أَمۡ زَاغَتۡ عَنۡهُمُ ٱلۡأَبۡصَٰرُ
“Shin mun xauke su ne ababen yi wa ba’a (a duniya), ko kuwa idanuwanmu ne suka bauxe ba sa hango su?”
إِنَّ ذَٰلِكَ لَحَقّٞ تَخَاصُمُ أَهۡلِ ٱلنَّارِ
“Shin mun xauke su ne ababen yi wa ba’a (a duniya), ko kuwa idanuwanmu ne suka bauxe ba sa hango su?”
قُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ مُنذِرٞۖ وَمَا مِنۡ إِلَٰهٍ إِلَّا ٱللَّهُ ٱلۡوَٰحِدُ ٱلۡقَهَّارُ
Ka ce: “Ni dai mai gargaxi ne kawai; kuma babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Allah Xaya, Mai rinjaye
رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡغَفَّـٰرُ
“Ubangijin sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu, Mabuwayi, Mai gafara.”
قُلۡ هُوَ نَبَؤٌاْ عَظِيمٌ
Ka ce: “Shi (wannan Alqur’ani) labari ne mai girma
أَنتُمۡ عَنۡهُ مُعۡرِضُونَ
“Da kuke bijire masa
مَا كَانَ لِيَ مِنۡ عِلۡمِۭ بِٱلۡمَلَإِ ٱلۡأَعۡلَىٰٓ إِذۡ يَخۡتَصِمُونَ
“Ban zama na san wani abu ba dangane da mala’iku masu daraja lokacin da suke yin muhawara (game da halittar Adamu)
إِن يُوحَىٰٓ إِلَيَّ إِلَّآ أَنَّمَآ أَنَا۠ نَذِيرٞ مُّبِينٌ
“Ba wani wahayi da aka yiwo min sai kawai cewa ni mai gargaxi ne mai bayyanawa.”
إِذۡ قَالَ رَبُّكَ لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ إِنِّي خَٰلِقُۢ بَشَرٗا مِّن طِينٖ
(Ka tuna) lokacin da Ubangijinka Ya ce da mala’iku: “Lalle Ni zan halicci wani mutum daga tavo
فَإِذَا سَوَّيۡتُهُۥ وَنَفَخۡتُ فِيهِ مِن رُّوحِي فَقَعُواْ لَهُۥ سَٰجِدِينَ
“To idan Na daidaita shi Na kuma busa masa ruhina, sai ku faxi kuna masu yi masa sujjada.”
فَسَجَدَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ كُلُّهُمۡ أَجۡمَعُونَ
Sai mala’iku dukkaninsu gaba xaya suka yi sujjada
إِلَّآ إِبۡلِيسَ ٱسۡتَكۡبَرَ وَكَانَ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Sai Iblisa da ya yi girman kai ya kuma zama cikin kafirai
قَالَ يَـٰٓإِبۡلِيسُ مَا مَنَعَكَ أَن تَسۡجُدَ لِمَا خَلَقۡتُ بِيَدَيَّۖ أَسۡتَكۡبَرۡتَ أَمۡ كُنتَ مِنَ ٱلۡعَالِينَ
(Allah) Ya ce: “Ya kai Iblisa, me ya hana ka yin sujjada ga abin da Na halitta da hannayena biyu? Ka yi girman kai ne, ko kuwa da man can ka kasance daga masu nuna isa?”
قَالَ أَنَا۠ خَيۡرٞ مِّنۡهُ خَلَقۡتَنِي مِن نَّارٖ وَخَلَقۡتَهُۥ مِن طِينٖ
Sai ya ce: “Ni ai na fi shi; (domin) Ka halicce ni ne daga wuta, (shi) kuma Ka halicce shi daga tavo.”
قَالَ فَٱخۡرُجۡ مِنۡهَا فَإِنَّكَ رَجِيمٞ
(Sai Allah) Ya ce (da shi): “To ka fice daga cikinta (wato Aljanna) saboda kai lalle korarre ne (daga rahama)
وَإِنَّ عَلَيۡكَ لَعۡنَتِيٓ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلدِّينِ
“Kuma lalle la’antata tabbas ta hau kanka har zuwa ranar alqiyama.”
قَالَ رَبِّ فَأَنظِرۡنِيٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ
(Sai Iblisa) ya ce: “Ya Ubangijina, Ka saurara min har zuwa ranar da za a tashe su.”
قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ ٱلۡمُنظَرِينَ
(Sai Allah) Ya ce: “To lalle kana cikin waxanda za a saurara wa
إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡوَقۡتِ ٱلۡمَعۡلُومِ
“Har zuwa ranar lokaci sananne.”
قَالَ فَبِعِزَّتِكَ لَأُغۡوِيَنَّهُمۡ أَجۡمَعِينَ
Sai ya ce: “To na rantse da girmanka tabbas zan vatar da su baki xaya
إِلَّا عِبَادَكَ مِنۡهُمُ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
“Sai dai bayinka waxanda aka tsarkake daga cikinsu.”
قَالَ فَٱلۡحَقُّ وَٱلۡحَقَّ أَقُولُ
(Allah) Ya ce: “Gaskiya (daga gare Ni take), kuma gaskiyar kawai Nake faxa!
لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنكَ وَمِمَّن تَبِعَكَ مِنۡهُمۡ أَجۡمَعِينَ
“Tabbas zan cika Jahannama da kai da kuma waxanda suka bi ka baki xaya.”
قُلۡ مَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٖ وَمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُتَكَلِّفِينَ
Ka faxa (musu): “Babu wani lada da nake tambayar ku game da shi, (wato isar da aike), kuma ni ba na cikin masu matsa wa kai (don in qago wani sabon saqo)
إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ لِّلۡعَٰلَمِينَ
“Shi ba wani abu ba ne in ban da tunatarwa ga talikai
وَلَتَعۡلَمُنَّ نَبَأَهُۥ بَعۡدَ حِينِۭ
“Kuma tabbas za ku san gaskiyar labarinsa (watau Alqur’ani) bayan wani xan lokaci.”