لِمِثۡلِ هَٰذَا فَلۡيَعۡمَلِ ٱلۡعَٰمِلُونَ
Don samun irin wannan lalle masu (kyakkyawan) aiki su yi aiki
Tarayya :
أَذَٰلِكَ خَيۡرٞ نُّزُلًا أَمۡ شَجَرَةُ ٱلزَّقُّومِ
Shin wannan liyafa ita ce ta fi alheri ko kuwa bishiyar Zaqqum?
إِنَّا جَعَلۡنَٰهَا فِتۡنَةٗ لِّلظَّـٰلِمِينَ
Lalle Mu Mun sanya ta don ta zama fitina ga azzalumai
إِنَّهَا شَجَرَةٞ تَخۡرُجُ فِيٓ أَصۡلِ ٱلۡجَحِيمِ
Lalle ita wata bishiya ce da take fitowa a tsakiyar wutar Jahima
طَلۡعُهَا كَأَنَّهُۥ رُءُوسُ ٱلشَّيَٰطِينِ
‘Ya’yanta kai ka ce kawunan shaixanu ne
فَإِنَّهُمۡ لَأٓكِلُونَ مِنۡهَا فَمَالِـُٔونَ مِنۡهَا ٱلۡبُطُونَ
To su lalle za su ci daga gare ta, za su kuma cika cikkuna da ita
ثُمَّ إِنَّ لَهُمۡ عَلَيۡهَا لَشَوۡبٗا مِّنۡ حَمِيمٖ
Sannan kuma suna da wani gauraye na tafasasshen ruwa a kanta
ثُمَّ إِنَّ مَرۡجِعَهُمۡ لَإِلَى ٱلۡجَحِيمِ
Sannan kuma lalle makomarsu wutar Jahima ce
إِنَّهُمۡ أَلۡفَوۡاْ ءَابَآءَهُمۡ ضَآلِّينَ
Lalle su sun sami iyayensu vatattu
فَهُمۡ عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِمۡ يُهۡرَعُونَ
Sai suka riqa gaggawar bin sawunsu
وَلَقَدۡ ضَلَّ قَبۡلَهُمۡ أَكۡثَرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Haqiqa kafin su mafi yawan mutanen farko sun vata
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا فِيهِم مُّنذِرِينَ
Kuma haqiqa Mun aiko masu gargaxi a cikinsu
فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُنذَرِينَ
To ka dubi yadda qarshen waxanda aka yi wa gargaxi ya kasance
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Sai dai bayin Allah waxanda aka tsarkake
وَلَقَدۡ نَادَىٰنَا نُوحٞ فَلَنِعۡمَ ٱلۡمُجِيبُونَ
Kuma haqiqa Nuhu ya roqe Mu, to madalla da Masu amsawa
وَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥ مِنَ ٱلۡكَرۡبِ ٱلۡعَظِيمِ
Muka kuma tserar da shi tare da iyalinsa daga baqin ciki mai girma
وَجَعَلۡنَا ذُرِّيَّتَهُۥ هُمُ ٱلۡبَاقِينَ
Muka kuma sanya zuriyarsa su ne suka wanzu
وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ
Muka kuma bar (kyakkyawan yabo) a gare shi ga ‘yan baya
سَلَٰمٌ عَلَىٰ نُوحٖ فِي ٱلۡعَٰلَمِينَ
Aminci ya tabbata ga Nuhu a cikin talikai
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Lalle Mu kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa
إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Lalle shi yana daga bayinmu muminai
ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ
Sannan Muka nutsar da sauran
۞وَإِنَّ مِن شِيعَتِهِۦ لَإِبۡرَٰهِيمَ
Lalle kuma Ibrahimu yana daga mabiya addininsa
إِذۡ جَآءَ رَبَّهُۥ بِقَلۡبٖ سَلِيمٍ
A yayin da ya zo wa Ubangijinsa da lafiyayyar zuciya
إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦ مَاذَا تَعۡبُدُونَ
Lokacin da ya ce da babansa da kuma mutanensa: “Me kuke bauta wa ne?
أَئِفۡكًا ءَالِهَةٗ دُونَ ٱللَّهِ تُرِيدُونَ
“Yanzu iyayen giji na qarya ba Allah ba kuke nufi?
فَمَا ظَنُّكُم بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
“To mene ne tsammaninku game da Ubangijin talikai?”
فَنَظَرَ نَظۡرَةٗ فِي ٱلنُّجُومِ
Sai ya yi duba a cikin taurari, duba na tunani
فَقَالَ إِنِّي سَقِيمٞ
Sannan ya ce: “Lalle ni fa ba ni da lafiya.”
فَتَوَلَّوۡاْ عَنۡهُ مُدۡبِرِينَ
Sai suka juya daga wurinsa suna masu ba da baya