Sura: Suratun Namli

Aya : 61

أَمَّن جَعَلَ ٱلۡأَرۡضَ قَرَارٗا وَجَعَلَ خِلَٰلَهَآ أَنۡهَٰرٗا وَجَعَلَ لَهَا رَوَٰسِيَ وَجَعَلَ بَيۡنَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ حَاجِزًاۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Ko kuwa wane ne ya sanya qasa wurin zama, ya kuma sanya qoramu a tsattsakinta, kuma ya sanya mata turaku, kana kuma ya sanya shamaki tsakanin kogunan nan biyu (na ruwan daxi da na ruwan zartsi)? Shin akwai wani abin bauta da gaskiya tare da Allah? A’a, yawancinsu dai ba sa ganewa



Sura: Suratun Namli

Aya : 62

أَمَّن يُجِيبُ ٱلۡمُضۡطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَيَكۡشِفُ ٱلسُّوٓءَ وَيَجۡعَلُكُمۡ خُلَفَآءَ ٱلۡأَرۡضِۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ قَلِيلٗا مَّا تَذَكَّرُونَ

Ko kuwa wane ne yake amsa wa wanda yake cikin matsuwa lokacin da ya roqe shi, yake kuma yaye duk wani bala’i, yake kuma sanya ku halifofi a bayan qasa[1]? Shin akwai wani abin bauta da gaskiya tare da Allah? Kaxan ne qwarai kuke wa’azantuwa


1- Wasu su shuxe wasu su zo su gaje su, tsareku bayan tsareku.


Sura: Suratun Namli

Aya : 63

أَمَّن يَهۡدِيكُمۡ فِي ظُلُمَٰتِ ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِ وَمَن يُرۡسِلُ ٱلرِّيَٰحَ بُشۡرَۢا بَيۡنَ يَدَيۡ رَحۡمَتِهِۦٓۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ تَعَٰلَى ٱللَّهُ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

Ko kuwa wane ne yake shiryar da ku a cikin duffan tudu da na kogi, kuma wane ne yake sako iska tana mai bushara gabanin (saukar) rahamarsa? Shin akwai wani abin bauta da gaskiya tare da Allah? Allah Ya xaukaka daga abin da suke tara (Shi da shi)



Sura: Suratun Namli

Aya : 64

أَمَّن يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ وَمَن يَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ قُلۡ هَاتُواْ بُرۡهَٰنَكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Ko kuwa wane ne yake qagar halitta sannan ya dawo da ita (bayan mutuwa), kuma wane ne yake arzuta ku ta sama da qasa? Shin akwai wani abin bauta da gaskiya tare da Allah?” Ka ce (da su): “Ku kawo dalilinku idan kun kasance masu gaskiya.”



Sura: Suratun Namli

Aya : 65

قُل لَّا يَعۡلَمُ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ ٱلۡغَيۡبَ إِلَّا ٱللَّهُۚ وَمَا يَشۡعُرُونَ أَيَّانَ يُبۡعَثُونَ

Ka ce (da su): “Duk wanda yake cikin sammai da qasa in ba Allah ba ba wanda ya san gaibu. Su kuma ba su san lokacin da za a tashe su ba.”



Sura: Suratun Namli

Aya : 66

بَلِ ٱدَّـٰرَكَ عِلۡمُهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِۚ بَلۡ هُمۡ فِي شَكّٖ مِّنۡهَاۖ بَلۡ هُم مِّنۡهَا عَمُونَ

A’a, iliminsu game da ranar lahira ya bibiyi na junansu[1] ne. Ba ma wannan kaxai ba, hakanan suna cikin kokwanto ne game da ita. Ban da hakan ma, su dai makafi ne game da ita


1- Watau sun sami iliminsu game da lahira daga iyayensu, su ma daga nasu iyayen, watau abin da ya shahara a wajensu na qaryata ranar alqiyama.


Sura: Suratun Namli

Aya : 67

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَءِذَا كُنَّا تُرَٰبٗا وَءَابَآؤُنَآ أَئِنَّا لَمُخۡرَجُونَ

Waxanda suka kafirta, kuma suka ce: “Yanzu bayan mun zama qasa mu da iyayenmu, ashe lalle za a (sake) fito da mu?



Sura: Suratun Namli

Aya : 68

لَقَدۡ وُعِدۡنَا هَٰذَا نَحۡنُ وَءَابَآؤُنَا مِن قَبۡلُ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ

“Haqiqa an yi mana alqawarin wannan mu da iyayenmu tun a da can, wannan ba komai ba ne face tatsuniyoyin mutanen farko.”



Sura: Suratun Namli

Aya : 69

قُلۡ سِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُجۡرِمِينَ

Ka ce (da su): “Ku yi tafiya a bayan qasa za ku ga yadda qarshen kafurai ya kasance.”



Sura: Suratun Namli

Aya : 70

وَلَا تَحۡزَنۡ عَلَيۡهِمۡ وَلَا تَكُن فِي ضَيۡقٖ مِّمَّا يَمۡكُرُونَ

Kuma kada ranka ya vaci game da su, kada kuma ka zama cikin quncin zuciya game da makircin da suke qullawa



Sura: Suratun Namli

Aya : 71

وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡوَعۡدُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Suna kuma cewa: “Yaushe ne lokacin wannan wa’adin idan kun kasance masu gaskiya?”



Sura: Suratun Namli

Aya : 72

قُلۡ عَسَىٰٓ أَن يَكُونَ رَدِفَ لَكُم بَعۡضُ ٱلَّذِي تَسۡتَعۡجِلُونَ

Ka ce (da su): “Lalle sashin abin da kuke gaggauto da zuwansa (na azaba) ya kusanto.”



Sura: Suratun Namli

Aya : 73

وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَشۡكُرُونَ

Kuma lalle Ubangijinka Mai falala ne ga mutane, sai dai kuma yawancinsu ba sa godewa



Sura: Suratun Namli

Aya : 74

وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَعۡلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمۡ وَمَا يُعۡلِنُونَ

Lalle kuma Ubangijinka tabbas Yana sane da abin da zukatansu suke voyewa, da kuma abin da suke bayyanawa



Sura: Suratun Namli

Aya : 75

وَمَا مِنۡ غَآئِبَةٖ فِي ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ إِلَّا فِي كِتَٰبٖ مُّبِينٍ

Kuma babu wani abu da yake voye a cikin sammai da qasa face yana cikin littafi mabayyani (watau Lauhul-Mahafuzu)



Sura: Suratun Namli

Aya : 76

إِنَّ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ يَقُصُّ عَلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ أَكۡثَرَ ٱلَّذِي هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

Lalle wannan Alqur’anin yana labarta wa Banu-Isra’ila mafi yawan abin da suke savani a kansa



Sura: Suratun Namli

Aya : 77

وَإِنَّهُۥ لَهُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ

Lalle kuma shi (Alqur’ani) tabbas shiriya ne kuma rahama ce ga muminai



Sura: Suratun Namli

Aya : 78

إِنَّ رَبَّكَ يَقۡضِي بَيۡنَهُم بِحُكۡمِهِۦۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡعَلِيمُ

Lalle Ubangijinka zai yi shari’a a tsakaninsu da hukuncinsa. Shi kuwa Mabuwayi ne, Masani



Sura: Suratun Namli

Aya : 79

فَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۖ إِنَّكَ عَلَى ٱلۡحَقِّ ٱلۡمُبِينِ

To ka dogara ga Allah; lalle kai kana kan gaskiya mabayyaniya



Sura: Suratun Namli

Aya : 80

إِنَّكَ لَا تُسۡمِعُ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَلَا تُسۡمِعُ ٱلصُّمَّ ٱلدُّعَآءَ إِذَا وَلَّوۡاْ مُدۡبِرِينَ

Lalle kai ba ka iya jiyar da matattu, ba kuma ka iya jiyar da kurame kira lokacin da suka juya suna masu ba da baya



Sura: Suratun Namli

Aya : 81

وَمَآ أَنتَ بِهَٰدِي ٱلۡعُمۡيِ عَن ضَلَٰلَتِهِمۡۖ إِن تُسۡمِعُ إِلَّا مَن يُؤۡمِنُ بِـَٔايَٰتِنَا فَهُم مُّسۡلِمُونَ

Kuma sannan kai ba za ka iya shiryar da makafi daga vatansu ba; ba wanda kake iya jiyarwa sai wanda ya yi imani da ayoyinmu, to waxannan su ne Musulmi



Sura: Suratun Namli

Aya : 82

۞وَإِذَا وَقَعَ ٱلۡقَوۡلُ عَلَيۡهِمۡ أَخۡرَجۡنَا لَهُمۡ دَآبَّةٗ مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ تُكَلِّمُهُمۡ أَنَّ ٱلنَّاسَ كَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا لَا يُوقِنُونَ

Kuma idan lokacin da aka alqawarta musu ya cika, to za Mu fito musu da wata dabba daga qasa[1] da za ta riqa faxa musu cewa: “Lalle mutane sun zamanto ba sa sakankancewa da ayoyinmu.”


1- Wannan xaya ce daga cikin manyan alamomin alqiyama, watau fitowar wata dabba mai magana da mutane.


Sura: Suratun Namli

Aya : 83

وَيَوۡمَ نَحۡشُرُ مِن كُلِّ أُمَّةٖ فَوۡجٗا مِّمَّن يُكَذِّبُ بِـَٔايَٰتِنَا فَهُمۡ يُوزَعُونَ

Kuma ka tuna ranar da za Mu tattara jama’a na kowacce al’umma, daga cikin waxanda suke qaryata ayoyinmu ana koro su na farko da na qarshe



Sura: Suratun Namli

Aya : 84

حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءُو قَالَ أَكَذَّبۡتُم بِـَٔايَٰتِي وَلَمۡ تُحِيطُواْ بِهَا عِلۡمًا أَمَّاذَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Har yayin da suka zo (sannan Allah) Ya ce da su: “Yanzu ku kuka qaryata ayoyina, alhali kuwa ba ku tantance da saninsu ba? Ko kuwa me kuka zamanto kuna aikatawa ne (a duniya)?”



Sura: Suratun Namli

Aya : 85

وَوَقَعَ ٱلۡقَوۡلُ عَلَيۡهِم بِمَا ظَلَمُواْ فَهُمۡ لَا يَنطِقُونَ

Kuma abin da aka alqawarta musu na azaba ya tabbata a kansu saboda kafircinsu, to su ba za su iya furta komai ba



Sura: Suratun Namli

Aya : 86

أَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّا جَعَلۡنَا ٱلَّيۡلَ لِيَسۡكُنُواْ فِيهِ وَٱلنَّهَارَ مُبۡصِرًاۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Yanzu ba sa gani cewa Mu Muka samar da dare don su nutsu a cikinsa, da kuma rana mai haskakawa (don su yi harka)? Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke yin imani



Sura: Suratun Namli

Aya : 87

وَيَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِ فَفَزِعَ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا مَن شَآءَ ٱللَّهُۚ وَكُلٌّ أَتَوۡهُ دَٰخِرِينَ

(Ka tuna) kuma ranar da za a busa qaho sai duk mahaluqin da yake cikin sammai da qasa ya firgita, sai dai wanda Allah Ya toge. Kuma gaba xayansu za su zo masa suna masu miqa wuya



Sura: Suratun Namli

Aya : 88

وَتَرَى ٱلۡجِبَالَ تَحۡسَبُهَا جَامِدَةٗ وَهِيَ تَمُرُّ مَرَّ ٱلسَّحَابِۚ صُنۡعَ ٱللَّهِ ٱلَّذِيٓ أَتۡقَنَ كُلَّ شَيۡءٍۚ إِنَّهُۥ خَبِيرُۢ بِمَا تَفۡعَلُونَ

Kuma za ka ga duwatsu ka zaci a tsaye suke cak, alhali kuwa su suna tafiya ne irin tafiyar gizagizai. Aikin Allah kenan wanda Ya kyautata halittar kowane irin abu. Lalle Shi Masanin abin da kuke aikatawa ne



Sura: Suratun Namli

Aya : 89

مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيۡرٞ مِّنۡهَا وَهُم مِّن فَزَعٖ يَوۡمَئِذٍ ءَامِنُونَ

Duk waxanda suka zo da kyakkyawan (aiki), to suna da (lada) fiye da shi, kuma su amintattu ne daga firgitar wannan ranar



Sura: Suratun Namli

Aya : 90

وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَكُبَّتۡ وُجُوهُهُمۡ فِي ٱلنَّارِ هَلۡ تُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Waxanda kuwa suka zo da mummunan (aiki), to an kifar da fuskokinsu cikin wuta, to ba za a saka muku ba sai da irin abin da kuka zamanto kuna aikatawa