Sura: Suratun Nur

Aya : 61

لَّيۡسَ عَلَى ٱلۡأَعۡمَىٰ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡأَعۡرَجِ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡمَرِيضِ حَرَجٞ وَلَا عَلَىٰٓ أَنفُسِكُمۡ أَن تَأۡكُلُواْ مِنۢ بُيُوتِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ ءَابَآئِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ أُمَّهَٰتِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ إِخۡوَٰنِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ أَخَوَٰتِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ أَعۡمَٰمِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ عَمَّـٰتِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ أَخۡوَٰلِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ خَٰلَٰتِكُمۡ أَوۡ مَا مَلَكۡتُم مَّفَاتِحَهُۥٓ أَوۡ صَدِيقِكُمۡۚ لَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَن تَأۡكُلُواْ جَمِيعًا أَوۡ أَشۡتَاتٗاۚ فَإِذَا دَخَلۡتُم بُيُوتٗا فَسَلِّمُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِكُمۡ تَحِيَّةٗ مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِ مُبَٰرَكَةٗ طَيِّبَةٗۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ

Babu wani laifi a kan makaho, babu kuma wani laifi a kan gurgu, kuma babu wani laifi a kan marar lafiya ko kuma a kanku, kan ku ci a gidajenku ko a gidajen iyayenku maza ko a gidajen iyayenku mata ko a gidajen ‘yan’uwanku maza ko a gidajen ‘yan’uwanku mata ko a gidajen baffanninku ko a gidajen gwaggwanninku ko kuma a gidajen kawunnanku ko kuma a gidajen yagwalgwalanku, ko kuma abin da kuka mallaki mabuxansa, ko kuma na abokinku. Babu wani laifi a kanku ku ci tare ko kuma daban-daban, sannan idan za ku shiga gidaje sai ku yi wa junanku sallama, (wannan) gaisuwa ce daga wurin Allah mai albarka tsattsarka. Kamar haka Allah Yake bayyana muku ayoyi don ku hankalta



Sura: Suratun Nur

Aya : 62

إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَإِذَا كَانُواْ مَعَهُۥ عَلَىٰٓ أَمۡرٖ جَامِعٖ لَّمۡ يَذۡهَبُواْ حَتَّىٰ يَسۡتَـٔۡذِنُوهُۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَسۡتَـٔۡذِنُونَكَ أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۚ فَإِذَا ٱسۡتَـٔۡذَنُوكَ لِبَعۡضِ شَأۡنِهِمۡ فَأۡذَن لِّمَن شِئۡتَ مِنۡهُمۡ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُمُ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Muminai na haqiqa (su ne) waxanda suka yi imani da Allah da Manzonsa, idan kuma suka kasance tare da shi bisa wani al’amari na jama’a, to ba za su tafi ba har sai sun nemi izininsa. Lalle waxanda suke neman izininka waxannan (su ne) waxanda suka yi imani da Allah da Manzonsa. To idan sun nemi izininka saboda wani sha’aninsu, sai ka yi izini ga wanda ka ga dama daga cikinsu, kuma ka nema musu gafarar Allah. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai rahama



Sura: Suratun Nur

Aya : 63

لَّا تَجۡعَلُواْ دُعَآءَ ٱلرَّسُولِ بَيۡنَكُمۡ كَدُعَآءِ بَعۡضِكُم بَعۡضٗاۚ قَدۡ يَعۡلَمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ يَتَسَلَّلُونَ مِنكُمۡ لِوَاذٗاۚ فَلۡيَحۡذَرِ ٱلَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنۡ أَمۡرِهِۦٓ أَن تُصِيبَهُمۡ فِتۡنَةٌ أَوۡ يُصِيبَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ

Kada ku mayar da kiran Manzo a tsakaninku kamar kiran junanku ga juna[1]. Haqiqa Allah Yana sane da waxanda suke zare jiki daga cikinku a voye. To lalle waxanda suke sava wa umarninsa su ji tsoron kada wata fitina ta shafe su ko kuma wata azaba mai raxaxi ta same su


1- Watau xayansu ya riqa cewa: “Ya Muhammadu” ko “Ya Muhammadu xan Abdullahi” ko “Ya xan Abdullahi”. Sai dai su ce: “Ya Manzon Allah” ko “Ya Annabin Allah”.


Sura: Suratun Nur

Aya : 64

أَلَآ إِنَّ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ قَدۡ يَعۡلَمُ مَآ أَنتُمۡ عَلَيۡهِ وَيَوۡمَ يُرۡجَعُونَ إِلَيۡهِ فَيُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُواْۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمُۢ

Ku saurara, lalle abin da yake sammai da qasa na Allah ne; haqiqa Yana sane da abin da ku kuke kansa, da kuma ranar da za a komar da su zuwa gare Shi, sannan Ya ba su labarin abin da suka aikata. Allah Masanin komai ne