Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 61

أُوْلَـٰٓئِكَ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِ وَهُمۡ لَهَا سَٰبِقُونَ

Waxannan su ne suke gaggawa ga ayyukan alheri, suna kuma masu rige-rige gare su



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 62

وَلَا نُكَلِّفُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۚ وَلَدَيۡنَا كِتَٰبٞ يَنطِقُ بِٱلۡحَقِّ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Ba Ma kuwa xora wa kowane rai wani abu sai wanda zai iya. Kuma a wurinmu akwai littafi da yake furuci da gaskiya, kuma su ba za a zalunce su ba



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 63

بَلۡ قُلُوبُهُمۡ فِي غَمۡرَةٖ مِّنۡ هَٰذَا وَلَهُمۡ أَعۡمَٰلٞ مِّن دُونِ ذَٰلِكَ هُمۡ لَهَا عَٰمِلُونَ

A’a, ba haka ba ne, zukatansu dai suna cikin gafala daga wannan (littafi mai furta gaskiya), suna kuma da wasu ayyukan ban da waxannan waxanda suke aikatawa



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 64

حَتَّىٰٓ إِذَآ أَخَذۡنَا مُتۡرَفِيهِم بِٱلۡعَذَابِ إِذَا هُمۡ يَجۡـَٔرُونَ

Har yayin da Muka kama mawadatansu da azaba sai ga su suna kururuwa



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 65

لَا تَجۡـَٔرُواْ ٱلۡيَوۡمَۖ إِنَّكُم مِّنَّا لَا تُنصَرُونَ

(Sai a ce da su): “Kada ku yi kururuwa a yau; lalle ku ba za a kare ku ba daga gare Mu



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 66

قَدۡ كَانَتۡ ءَايَٰتِي تُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ فَكُنتُمۡ عَلَىٰٓ أَعۡقَٰبِكُمۡ تَنكِصُونَ

“Haqiqa ayoyina sun kasance ana karanta muku su, sai kuka zamanto kuna komawa da baya



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 67

مُسۡتَكۡبِرِينَ بِهِۦ سَٰمِرٗا تَهۡجُرُونَ

“Kuna masu girman kai (na qin imani) a wurinsa (Xakin Ka’aba), kuna masu hira, kuna vata (Alqur’ani).”



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 68

أَفَلَمۡ يَدَّبَّرُواْ ٱلۡقَوۡلَ أَمۡ جَآءَهُم مَّا لَمۡ يَأۡتِ ءَابَآءَهُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ

Me ya sa ne ba su yi zuzzurfan tunani ba game da Alqur’ani, ko kuwa wani abu ne ya zo musu da bai zo wa iyayensu na farko ba?



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 69

أَمۡ لَمۡ يَعۡرِفُواْ رَسُولَهُمۡ فَهُمۡ لَهُۥ مُنكِرُونَ

Ko kuwa ba su san Manzonsu ba ne, don haka ba su tantance da shi ba?



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 70

أَمۡ يَقُولُونَ بِهِۦ جِنَّةُۢۚ بَلۡ جَآءَهُم بِٱلۡحَقِّ وَأَكۡثَرُهُمۡ لِلۡحَقِّ كَٰرِهُونَ

Ko kuwa cewa suke yi ya tavu? A’a, ya zo musu ne da gaskiya, sai dai yawancinsu masu qin gaskiya ne



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 71

وَلَوِ ٱتَّبَعَ ٱلۡحَقُّ أَهۡوَآءَهُمۡ لَفَسَدَتِ ٱلسَّمَٰوَٰتُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَن فِيهِنَّۚ بَلۡ أَتَيۡنَٰهُم بِذِكۡرِهِمۡ فَهُمۡ عَن ذِكۡرِهِم مُّعۡرِضُونَ

Da kuma Alqur’ani ya biye ma son ransu, to da lallai sammai da qasa da abin da yake cikinsu duka sun lalace. A’a, Mun dai zo musu ne da abin alfaharinsu, amma kuma suna masu bijire wa abin alfaharin nasu



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 72

أَمۡ تَسۡـَٔلُهُمۡ خَرۡجٗا فَخَرَاجُ رَبِّكَ خَيۡرٞۖ وَهُوَ خَيۡرُ ٱلرَّـٰزِقِينَ

Ko kuwa kana neman lada ne a wurinsu, to ladan Ubangijinka shi ya fi alheri; kuma Shi ne Fiyayyen masu arzutawa



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 73

وَإِنَّكَ لَتَدۡعُوهُمۡ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Kuma lalle kai tabbas kana kiran su ne zuwa ga hanya madaidaiciya



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 74

وَإِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ عَنِ ٱلصِّرَٰطِ لَنَٰكِبُونَ

Lalle kuma waxanda ba sa yin imani da lahira tabbas su masu bauxewa ne daga hanya



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 75

۞وَلَوۡ رَحِمۡنَٰهُمۡ وَكَشَفۡنَا مَا بِهِم مِّن ضُرّٖ لَّلَجُّواْ فِي طُغۡيَٰنِهِمۡ يَعۡمَهُونَ

Da kuwa Mun ji qan su Mun kuma yaye musu cutar da take tare da su (ta fari), to tabbas da sun zarce cikin shisshiginsu suna fagamniya



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 76

وَلَقَدۡ أَخَذۡنَٰهُم بِٱلۡعَذَابِ فَمَا ٱسۡتَكَانُواْ لِرَبِّهِمۡ وَمَا يَتَضَرَّعُونَ

Kuma haqiqa Mun kama su da azaba amma ba su miqa wuya ga Ubangijinsu ba, ba sa kuma qasqantar da kai



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 77

حَتَّىٰٓ إِذَا فَتَحۡنَا عَلَيۡهِم بَابٗا ذَا عَذَابٖ شَدِيدٍ إِذَا هُمۡ فِيهِ مُبۡلِسُونَ

Har dai yayin da Muka buxe musu qofa mai matsananciyar azaba sai ga su cikinta suna masu yanke qauna (daga kowace rahama)



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 78

وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَنشَأَ لَكُمُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَٱلۡأَفۡـِٔدَةَۚ قَلِيلٗا مَّا تَشۡكُرُونَ

Shi ne kuma (Allah) wanda Ya halitta muku ji da gani da kuma zukata. Kaxan qwarai kuke gode wa (masa)



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 79

وَهُوَ ٱلَّذِي ذَرَأَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَإِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ

Shi ne kuma wanda Ya halicce ku a bayan qasa, kuma zuwa gare Shi za a tattara ku



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 80

وَهُوَ ٱلَّذِي يُحۡيِۦ وَيُمِيتُ وَلَهُ ٱخۡتِلَٰفُ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

Kuma Shi ne Yake rayawa Yake kuma kashewa, kuma sassavawar dare da rana nasa ne. Me ya sa ba kwa hankalta ne?



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 81

بَلۡ قَالُواْ مِثۡلَ مَا قَالَ ٱلۡأَوَّلُونَ

A’a, sun dai faxi irin abin da (mutanen) farko suka faxa ne



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 82

قَالُوٓاْ أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ

(Wato) sun ce: “Yanzu wai idan mun mutu kuma mun zama turvaya da qasusuwa, anya za a kuwa tashe mu?



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 83

لَقَدۡ وُعِدۡنَا نَحۡنُ وَءَابَآؤُنَا هَٰذَا مِن قَبۡلُ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ

“Haqiqa mu da iyayenmu an yi mana alqawarin wannan tun tuni, wannan ba wani abu ba ne in ban da tatsuniyoyin mutan da.”



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 84

قُل لِّمَنِ ٱلۡأَرۡضُ وَمَن فِيهَآ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Ka ce (da su): “Qasa da abin da yake cikinta na Wane ne, idan kun kasance kun sani?”



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 85

سَيَقُولُونَ لِلَّهِۚ قُلۡ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ

Ai za ka ji sun ce: “Na Allah ne.” Ka ce (da su): “To me ya sa ba kwa wa’azantuwa ne?”



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 86

قُلۡ مَن رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ ٱلسَّبۡعِ وَرَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡعَظِيمِ

Ka ce (da su): “Wane ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al’arshi mai girma?”



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 87

سَيَقُولُونَ لِلَّهِۚ قُلۡ أَفَلَا تَتَّقُونَ

Ai za su ce: “Na Allah ne.” Ka ce (da su): “To me ya sa ba kwa taqawa?”



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 88

قُلۡ مَنۢ بِيَدِهِۦ مَلَكُوتُ كُلِّ شَيۡءٖ وَهُوَ يُجِيرُ وَلَا يُجَارُ عَلَيۡهِ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Ka ce (da su): “Wane ne mulkin komai yake a hannunsa, kuma Shi ne Yake kariya, (Shi) kuma ba a kare wani daga gare Shi, idan kun kasance kun sani?”



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 89

سَيَقُولُونَ لِلَّهِۚ قُلۡ فَأَنَّىٰ تُسۡحَرُونَ

Ai za su ce: “Na Allah ne.” Ka ce (da su): “To ta ina ne ake tafiyar muku da hankalinku?”



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 90

بَلۡ أَتَيۡنَٰهُم بِٱلۡحَقِّ وَإِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ

A’a, Mun dai zo musu ne da gaskiya, su kuwa lalle tabbas maqaryata ne