فَلَمَّا جَآءَ ءَالَ لُوطٍ ٱلۡمُرۡسَلُونَ
To lokacin da manzannin suka zo wa iyalin Luxu
قَالَ إِنَّكُمۡ قَوۡمٞ مُّنكَرُونَ
Ya ce: “Lalle ku wasu mutane ne da ba a san su ba.”
قَالُواْ بَلۡ جِئۡنَٰكَ بِمَا كَانُواْ فِيهِ يَمۡتَرُونَ
Suka ce: “A’a, mu mun zo maka ne da abin da (mutanenka) suke kokwanto game da shi
وَأَتَيۡنَٰكَ بِٱلۡحَقِّ وَإِنَّا لَصَٰدِقُونَ
“Mun kuma zo maka da dahir, lalle kuma tabbas mu masu gaskiya ne
فَأَسۡرِ بِأَهۡلِكَ بِقِطۡعٖ مِّنَ ٱلَّيۡلِ وَٱتَّبِعۡ أَدۡبَٰرَهُمۡ وَلَا يَلۡتَفِتۡ مِنكُمۡ أَحَدٞ وَٱمۡضُواْ حَيۡثُ تُؤۡمَرُونَ
“Sai ka tafi da iyalinka cikin wani yankin dare ka kuma riqa bin su a baya, kada kuwa xaya daga cikinku ya waiwaya, kuma ku tafi inda aka umarce ku.”
وَقَضَيۡنَآ إِلَيۡهِ ذَٰلِكَ ٱلۡأَمۡرَ أَنَّ دَابِرَ هَـٰٓؤُلَآءِ مَقۡطُوعٞ مُّصۡبِحِينَ
Muka kuwa sanar da shi abin da Muka qaddara na wannan al’amari cewa, qarshen waxannan zai yanke ne da asuba
وَجَآءَ أَهۡلُ ٱلۡمَدِينَةِ يَسۡتَبۡشِرُونَ
Mutanen garin kuma suka zo suna murna (da ganin baqin)
قَالَ إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ ضَيۡفِي فَلَا تَفۡضَحُونِ
Ya ce: “Lalle waxannan baqina ne, kada fa ku kunyata ni
وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَلَا تُخۡزُونِ
“Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kada ku tozarta ni[1].”
1- Annabi Luxu ya yi wannan maganar ne kafin ya san cewa waxannan baqi nasa mala’iku ne.
قَالُوٓاْ أَوَلَمۡ نَنۡهَكَ عَنِ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Suka ce: “Ashe ba mu hana ka (ka saukar da) mutane (baqi ba)?”
قَالَ هَـٰٓؤُلَآءِ بَنَاتِيٓ إِن كُنتُمۡ فَٰعِلِينَ
Ya ce: “Ga ‘ya’yana nan (ku aura)[1] idan kun kasance masu aikata (haka)
1- Yana nufin matan al’ummarsa.
لَعَمۡرُكَ إِنَّهُمۡ لَفِي سَكۡرَتِهِمۡ يَعۡمَهُونَ
“Na rantse da rayuwarka lalle su tabbas suna cikin mayensu suna ta ximuwa.”
فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّيۡحَةُ مُشۡرِقِينَ
Sai tsawa ta auka musu lokacin hudowar rana
فَجَعَلۡنَا عَٰلِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِمۡ حِجَارَةٗ مِّن سِجِّيلٍ
Sai Muka mayar da samanta ya koma qasa, Muka kuma yi musu ruwan duwatsu soyayyu
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّلۡمُتَوَسِّمِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga masu hangen nesa
وَإِنَّهَا لَبِسَبِيلٖ مُّقِيمٍ
Lalle kuma ita (alqaryar) tabbas tana kan wani gwadabe ne miqaqqe
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai izina ga muminai
وَإِن كَانَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡأَيۡكَةِ لَظَٰلِمِينَ
Lalle kuma mutanen (alqaryar) Mai duhuwa tabbas sun zamanto azzalumai
فَٱنتَقَمۡنَا مِنۡهُمۡ وَإِنَّهُمَا لَبِإِمَامٖ مُّبِينٖ
Sai Muka azabtar da su, lalle kuma su biyun suna kan wani gwadabe ne fitacce
وَلَقَدۡ كَذَّبَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡحِجۡرِ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Haqiqa kuma mutanen Hijiru (Samudawa) sun qaryata manzanni
وَءَاتَيۡنَٰهُمۡ ءَايَٰتِنَا فَكَانُواْ عَنۡهَا مُعۡرِضِينَ
Muka kuma kawo musu ayoyinmu, sai suka zamanto masu bijirewa daga gare su
وَكَانُواْ يَنۡحِتُونَ مِنَ ٱلۡجِبَالِ بُيُوتًا ءَامِنِينَ
Sun zamanto suna fafe duwatsu suna yin gidaje su zama cikin aminci
فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّيۡحَةُ مُصۡبِحِينَ
Sai tsawa ta auka musu da asuba
فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Sai abin da suka zamanto suna aikatawa bai amfane su ba
وَمَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۗ وَإِنَّ ٱلسَّاعَةَ لَأٓتِيَةٞۖ فَٱصۡفَحِ ٱلصَّفۡحَ ٱلۡجَمِيلَ
Ba Mu kuma halicci sammai da qasa ba sai da gaskiya. Kuma lalle alqiyama tabbas mai zuwa ce, sai ka yi afuwa kyakkyawar afuwa[1]
1- Watau afuwar da babu cutarwa a cikinta sai dai kyautatawa ga wanda ya munana.
إِنَّ رَبَّكَ هُوَ ٱلۡخَلَّـٰقُ ٱلۡعَلِيمُ
Lalle Ubangijinka Shi ne Mai halitta, Masani
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَٰكَ سَبۡعٗا مِّنَ ٱلۡمَثَانِي وَٱلۡقُرۡءَانَ ٱلۡعَظِيمَ
Haqiqa kuma Mun ba ka (ayoyi) bakwai waxanda ake ta nanatawa (wato Suratul Fatiha) da kuma Alqur’ani mai girma
لَا تَمُدَّنَّ عَيۡنَيۡكَ إِلَىٰ مَا مَتَّعۡنَا بِهِۦٓ أَزۡوَٰجٗا مِّنۡهُمۡ وَلَا تَحۡزَنۡ عَلَيۡهِمۡ وَٱخۡفِضۡ جَنَاحَكَ لِلۡمُؤۡمِنِينَ
Kada ka zura idanuwanka ga abubuwan jin daxi da Muka ba wa wasu dangogi daga cikinsu, kada kuma ka yi baqin ciki a kansu, kuma ka qasqantar da kanka ga muminai
وَقُلۡ إِنِّيٓ أَنَا ٱلنَّذِيرُ ٱلۡمُبِينُ
Ka kuma ce: “Lalle ni, ni ne mai gargaxi mabayyani»
كَمَآ أَنزَلۡنَا عَلَى ٱلۡمُقۡتَسِمِينَ
Kamar yadda Muka saukar wa masu rarrabawa (wato ma’abota littafi)