ثُمَّ ٱلۡجَحِيمَ صَلُّوهُ
Sannan ku shigar da shi (wutar) Jahimu
Tarayya :
ثُمَّ فِي سِلۡسِلَةٖ ذَرۡعُهَا سَبۡعُونَ ذِرَاعٗا فَٱسۡلُكُوهُ
Sannan ku sa shi cikin sarqa mai tsawo kamu saba’in
إِنَّهُۥ كَانَ لَا يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ ٱلۡعَظِيمِ
Lalle shi ya kasance ba ya imani da Allah Mai girma
وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلۡمِسۡكِينِ
Ba ya kuma kwaxaitarwa bisa ciyar da mabuqaci
فَلَيۡسَ لَهُ ٱلۡيَوۡمَ هَٰهُنَا حَمِيمٞ
To a yau ba shi da wani masoyi a nan
وَلَا طَعَامٌ إِلَّا مِنۡ غِسۡلِينٖ
Kuma ba shi da wani abinci sai na mugunyar ‘yan wuta
لَّا يَأۡكُلُهُۥٓ إِلَّا ٱلۡخَٰطِـُٔونَ
Ba mai cin ta sai masu laifukan ganganci
فَلَآ أُقۡسِمُ بِمَا تُبۡصِرُونَ
Ina yin rantsuwa da abin da kuke gani
وَمَا لَا تُبۡصِرُونَ
Da kuma abin da ba kwa gani
إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولٖ كَرِيمٖ
Lalle shi (Alqur’ani) tabbas zance ne na wani manzo mai girma
وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَاعِرٖۚ قَلِيلٗا مَّا تُؤۡمِنُونَ
Shi kuwa ba zancen mawaqi ba ne. Kaxan ne qwarai kuke yin imani
وَلَا بِقَوۡلِ كَاهِنٖۚ قَلِيلٗا مَّا تَذَكَّرُونَ
Ba kuma zance ne na boka ba. Kaxan ne qwarai kuke wa’azantuwa
تَنزِيلٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Shi saukakke ne daga Ubangijin halittu
وَلَوۡ تَقَوَّلَ عَلَيۡنَا بَعۡضَ ٱلۡأَقَاوِيلِ
Kuma da ya qaga Mana wasu maganganu
لَأَخَذۡنَا مِنۡهُ بِٱلۡيَمِينِ
Tabbas da Mun kama shi da qarfi
ثُمَّ لَقَطَعۡنَا مِنۡهُ ٱلۡوَتِينَ
Sannan da Mun yanke masa jijiyar zuciyarsa
فَمَا مِنكُم مِّنۡ أَحَدٍ عَنۡهُ حَٰجِزِينَ
Sannan kuma ba wani xaya daga cikinku da zai kare shi
وَإِنَّهُۥ لَتَذۡكِرَةٞ لِّلۡمُتَّقِينَ
Lalle shi (Alqur’ani) wa’azi ne ga masu kiyaye dokokin Allah
وَإِنَّا لَنَعۡلَمُ أَنَّ مِنكُم مُّكَذِّبِينَ
Lalle kuma Mu Muna sane da cewa a cikinku akwai masu qaryatawa
وَإِنَّهُۥ لَحَسۡرَةٌ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ
Kuma lalle shi tabbas nadama ce ga kafirai
وَإِنَّهُۥ لَحَقُّ ٱلۡيَقِينِ
Kuma lalle shi tabbas gaskiya ce ta sakankancewa
فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ
Saboda haka ka yi tasbihi da sunan Ubangijinka Mai girma