Sura: Suratu Saba’i

Aya : 31

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَن نُّؤۡمِنَ بِهَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ وَلَا بِٱلَّذِي بَيۡنَ يَدَيۡهِۗ وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذِ ٱلظَّـٰلِمُونَ مَوۡقُوفُونَ عِندَ رَبِّهِمۡ يَرۡجِعُ بَعۡضُهُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٍ ٱلۡقَوۡلَ يَقُولُ ٱلَّذِينَ ٱسۡتُضۡعِفُواْ لِلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُواْ لَوۡلَآ أَنتُمۡ لَكُنَّا مُؤۡمِنِينَ

Kuma kafirai suka ce: “Ba za mu yi imani da wannan Alqur’ani ba, haka ma da wanda yake gabaninsa (na saukakkun littattafai).” Da kuwa za ka ga lokacin da za a tsai da azzalumai wajen Ubangijinsu suna mayar wa da juna magana, masu rauninsu (mabiya) suna ce wa masu girman kai (watau shugabanninsu): “Ba don ku ba da mun zamanto muminai.”



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 32

قَالَ ٱلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُواْ لِلَّذِينَ ٱسۡتُضۡعِفُوٓاْ أَنَحۡنُ صَدَدۡنَٰكُمۡ عَنِ ٱلۡهُدَىٰ بَعۡدَ إِذۡ جَآءَكُمۖ بَلۡ كُنتُم مُّجۡرِمِينَ

Masu girman kan suka ce wa raunanan: “Yanzu mu muka hana ku ku shiriya bayan ta zo muku? Ba haka ba ne, kun dai kasance masu laifi ne.”



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 33

وَقَالَ ٱلَّذِينَ ٱسۡتُضۡعِفُواْ لِلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُواْ بَلۡ مَكۡرُ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ إِذۡ تَأۡمُرُونَنَآ أَن نَّكۡفُرَ بِٱللَّهِ وَنَجۡعَلَ لَهُۥٓ أَندَادٗاۚ وَأَسَرُّواْ ٱلنَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَۚ وَجَعَلۡنَا ٱلۡأَغۡلَٰلَ فِيٓ أَعۡنَاقِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۖ هَلۡ يُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Raunanan kuma suka ce da manyan masu girman kan: “Ba haka ba ne, makircin dare da na rana ne (da kuke qulla mana ya hana mu shiriya), yayin da kuke umartar mu da mu kafirce wa Allah, mu kuma sanya masa abokan tarayya.” Suka kuma bayyana nadama lokacin da suka ga azaba, kuma Muka sanya ququmi a wuyan waxanda suka kafirta, ba kuwa za a saka musu da komai ba sai da irin abin da suka kasance suna aikatawa



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 34

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا فِي قَرۡيَةٖ مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُتۡرَفُوهَآ إِنَّا بِمَآ أُرۡسِلۡتُم بِهِۦ كَٰفِرُونَ

Ba Mu tava aiko wani mai gargaxi cikin wata alqarya ba sai mawadatan cikinta sun ce: “Mu dai masu kafirce wa abin da aka aiko ku da shi ne.”



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 35

وَقَالُواْ نَحۡنُ أَكۡثَرُ أَمۡوَٰلٗا وَأَوۡلَٰدٗا وَمَا نَحۡنُ بِمُعَذَّبِينَ

Suka kuma ce: “Mu muka fi kowa yawan dukiya da ‘ya’ya, kuma mu ba waxanda za a azabtar ba ne.”



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 36

قُلۡ إِنَّ رَبِّي يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

Ka ce: “Lalle Ubangijina Yana shimfixa arziki ga wanda Ya ga dama, Ya kuma quntata, sai dai kuma yawancin mutane ba su san (haka) ba.”



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 37

وَمَآ أَمۡوَٰلُكُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُكُم بِٱلَّتِي تُقَرِّبُكُمۡ عِندَنَا زُلۡفَىٰٓ إِلَّا مَنۡ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَأُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ جَزَآءُ ٱلضِّعۡفِ بِمَا عَمِلُواْ وَهُمۡ فِي ٱلۡغُرُفَٰتِ ءَامِنُونَ

Kuma ba dukiyoyinku da ‘ya’yanku ne za su kusantar da ku gare Mu ba, sai wanda ya yi imani ya kuma yi aiki nagari, to waxannan suna da sakamako ninkin-baninki saboda abin da suka aikata, suna kuma amintattu cikin benaye



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 38

وَٱلَّذِينَ يَسۡعَوۡنَ فِيٓ ءَايَٰتِنَا مُعَٰجِزِينَ أُوْلَـٰٓئِكَ فِي ٱلۡعَذَابِ مُحۡضَرُونَ

Waxanda kuwa suke yin qoqari na vata ayoyinmu, don su nuna gazawarmu, waxannan cikin azaba za a halartar da su



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 39

قُلۡ إِنَّ رَبِّي يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦ وَيَقۡدِرُ لَهُۥۚ وَمَآ أَنفَقۡتُم مِّن شَيۡءٖ فَهُوَ يُخۡلِفُهُۥۖ وَهُوَ خَيۡرُ ٱلرَّـٰزِقِينَ

Ka ce: “Lalle Ubangijna Yana shimfixa arziki ga wanda ya ga dama cikin bayinsa, Yana kuma quntata masa. Kuma duk abin da kuka ciyar (don Allah), to Shi ne zai ba ku madadinsa, Shi ne kuwa Fiyayyen masu arzutawa.”



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 40

وَيَوۡمَ يَحۡشُرُهُمۡ جَمِيعٗا ثُمَّ يَقُولُ لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ أَهَـٰٓؤُلَآءِ إِيَّاكُمۡ كَانُواْ يَعۡبُدُونَ

Kuma (ka tuna) ranar da zai tattaro su gaba xaya sannan Ya ce da mala’iku: “Ashe yanzu ku ne waxannan suka kasance suna bauta wa?”



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 41

قَالُواْ سُبۡحَٰنَكَ أَنتَ وَلِيُّنَا مِن دُونِهِمۖ بَلۡ كَانُواْ يَعۡبُدُونَ ٱلۡجِنَّۖ أَكۡثَرُهُم بِهِم مُّؤۡمِنُونَ

Suka ce: “Tsarki ya tabbata a gare Ka, Kai ne Majivincinmu ba su ba.” Ba haka ba ne, sun kasance suna bauta wa aljannu ne; mafiya yawansu masu yin imani da su ne



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 42

فَٱلۡيَوۡمَ لَا يَمۡلِكُ بَعۡضُكُمۡ لِبَعۡضٖ نَّفۡعٗا وَلَا ضَرّٗا وَنَقُولُ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ ذُوقُواْ عَذَابَ ٱلنَّارِ ٱلَّتِي كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ

(Sai Allah Ya ce): “To yau shashinku ba zai mallaki amfani ga wani sashi ba ko cutarwa,” za kuma Mu ce da waxanda suka kafirta: “Ku xanxani azabar wutar da kuka kasance kuna qaryata ta.”



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 43

وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُنَا بَيِّنَٰتٖ قَالُواْ مَا هَٰذَآ إِلَّا رَجُلٞ يُرِيدُ أَن يَصُدَّكُمۡ عَمَّا كَانَ يَعۡبُدُ ءَابَآؤُكُمۡ وَقَالُواْ مَا هَٰذَآ إِلَّآ إِفۡكٞ مُّفۡتَرٗىۚ وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمۡ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ

Idan kuma ana karanta musu ayoyinmu mabayyana sai su ce: “Wannan ai ba wani ba ne sai wani mutum da yake nufin ya hana ku (bauta wa) abin da iyayenku suka kasance suna bauta wa.” Suka kuma ce: “Wannan ai ba wani abu ba ne in ban da qarya da aka qirqira.” Waxanda kuma suka kafirta suka ce game da gaskiya yayin da ta zo musu: “Wannan ba wani abu ba ne sai sihiri mabayyani.”



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 44

وَمَآ ءَاتَيۡنَٰهُم مِّن كُتُبٖ يَدۡرُسُونَهَاۖ وَمَآ أَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهِمۡ قَبۡلَكَ مِن نَّذِيرٖ

Kuma ba Mu kawo musu wasu littattafai da suke karantawa ba, kuma ba Mu aiko musu da wani mai gargaxi ba gabaninka



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 45

وَكَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ وَمَا بَلَغُواْ مِعۡشَارَ مَآ ءَاتَيۡنَٰهُمۡ فَكَذَّبُواْ رُسُلِيۖ فَكَيۡفَ كَانَ نَكِيرِ

Kuma waxanda suka gabace su sun qaryata (annabawa; kafiran Makka) kuwa ba su kai ushurin abin da Muka ba su ba, to su ma sun qaryata manzannina; to yaya tsawatarwata ta kasance (gare su)?



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 46

۞قُلۡ إِنَّمَآ أَعِظُكُم بِوَٰحِدَةٍۖ أَن تَقُومُواْ لِلَّهِ مَثۡنَىٰ وَفُرَٰدَىٰ ثُمَّ تَتَفَكَّرُواْۚ مَا بِصَاحِبِكُم مِّن جِنَّةٍۚ إِنۡ هُوَ إِلَّا نَذِيرٞ لَّكُم بَيۡنَ يَدَيۡ عَذَابٖ شَدِيدٖ

Ka ce: “Ni dai kawai ina yi muku wa’azi ne da abu xaya; cewa ku tsaya don Allah; bibbiyu da kuma xai-xai, sannan ku yi tunani. Ba wata hauka tare da mutuminku, shi ba wani ne ba, sai mai yi muku gargaxin azaba mai tsanani da take gabanku.”



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 47

قُلۡ مَا سَأَلۡتُكُم مِّنۡ أَجۡرٖ فَهُوَ لَكُمۡۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٞ

Ka ce: “Abin da na tambaye ku na wani lada to naku ne[1]; ladana yana wajen Allah kawai; kuma Shi Mai shaida ne a kan komai.”


1- Watau ko da kuwa a ce ya nemi su bayar da wani lada a kan hakan, to ladan nasu ne, ba nasa ba ne, shi sakamakonsa yana wajen Allah shi kaxai.


Sura: Suratu Saba’i

Aya : 48

قُلۡ إِنَّ رَبِّي يَقۡذِفُ بِٱلۡحَقِّ عَلَّـٰمُ ٱلۡغُيُوبِ

Ka ce: “Lalle Ubangijina Yana jefo gaskiya (sai ta rushe qarya), Masanin gaibu ne.”



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 49

قُلۡ جَآءَ ٱلۡحَقُّ وَمَا يُبۡدِئُ ٱلۡبَٰطِلُ وَمَا يُعِيدُ

Ka ce: “Gaskiya ta zo qarya kuma ba za ta sake faruwa ba, ba kuma za ta dawo ba.”



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 50

قُلۡ إِن ضَلَلۡتُ فَإِنَّمَآ أَضِلُّ عَلَىٰ نَفۡسِيۖ وَإِنِ ٱهۡتَدَيۡتُ فَبِمَا يُوحِيٓ إِلَيَّ رَبِّيٓۚ إِنَّهُۥ سَمِيعٞ قَرِيبٞ

Ka ce: “Idan na vata to na vata ne a kan kaina; idan kuwa na shiriya to (na shiriya ne) da abin da Ubangijina Yake yi min wahayinsa. Lalle Shi Mai ji ne, Makusanci.”



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 51

وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ فَزِعُواْ فَلَا فَوۡتَ وَأُخِذُواْ مِن مَّكَانٖ قَرِيبٖ

Da kuwa za ka ga sanda (kafirai) za su firgita, (da ganin azaba), sannan ba wata makuvuta, kuma aka damqo su daga makusancin wuri



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 52

وَقَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِهِۦ وَأَنَّىٰ لَهُمُ ٱلتَّنَاوُشُ مِن مَّكَانِۭ بَعِيدٖ

Suka kuma ce: “Mun yi imani da shi,” yaya kuwa za su iya kamo (wannan imani) daga wuri mai nisa (wato duniya)?



Sura: Suratu Saba’i

Aya : 53

وَقَدۡ كَفَرُواْ بِهِۦ مِن قَبۡلُۖ وَيَقۡذِفُونَ بِٱلۡغَيۡبِ مِن مَّكَانِۭ بَعِيدٖ

Alhalin kuma haqiqa sun riga sun kafirta da shi a da can, kuma suna jifa (da zato) ta wani wuri mai nisa[1]


1- Watau sun riqa jifan Manzon Allah () da zace-zace iri-iri da shaci-faxi, wani lokaci su kira shi mai sihiri, wani lokaci su ce masa boka, ko su kira shi mawaqi.


Sura: Suratu Saba’i

Aya : 54

وَحِيلَ بَيۡنَهُمۡ وَبَيۡنَ مَا يَشۡتَهُونَ كَمَا فُعِلَ بِأَشۡيَاعِهِم مِّن قَبۡلُۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ فِي شَكّٖ مُّرِيبِۭ

Aka kuma kange tsakaninsu da abin da suke sha’awa (na jin daxin rayuwa ko komawa duniya) kamar yadda aka yi da ire-irensu tun da can. Lalle su sun kasance cikin shakka mai cike da kokwanto