ثُمَّ أَنشَأۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِمۡ قَرۡنًا ءَاخَرِينَ
Sannan kuma a bayansu Muka halicci wata al’umma daban
فَأَرۡسَلۡنَا فِيهِمۡ رَسُولٗا مِّنۡهُمۡ أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓۚ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Sai Muka aiko musu wani manzon daga cikinsu da cewa: “Ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta in ba Shi ba; me ya sa ne ba za ku yi taqawa ba?”
وَقَالَ ٱلۡمَلَأُ مِن قَوۡمِهِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِلِقَآءِ ٱلۡأٓخِرَةِ وَأَتۡرَفۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا مَا هَٰذَآ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ يَأۡكُلُ مِمَّا تَأۡكُلُونَ مِنۡهُ وَيَشۡرَبُ مِمَّا تَشۡرَبُونَ
Kuma manyan mutane daga cikin mutanensa waxanda suka kafirce suka kuma qaryata haxuwa da ranar lahira, Muka kuma wadata su a rayuwar duniya, suka ce: “Wannan ba kowa ba ne face mutum kamarku, yana cin irin abin da kuke ci, yana kuma shan irin abin da kuke sha
وَلَئِنۡ أَطَعۡتُم بَشَرٗا مِّثۡلَكُمۡ إِنَّكُمۡ إِذٗا لَّخَٰسِرُونَ
“Kuma tabbas in har kuka bi mutum kamarku, to lalle tabbas a sannan kun yi asara
أَيَعِدُكُمۡ أَنَّكُمۡ إِذَا مِتُّمۡ وَكُنتُمۡ تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَنَّكُم مُّخۡرَجُونَ
“Shin yanzu ya riqa yi muku alqawarin cewa idan kun mutu kun kuma zama turvaya da qasusuwa cewa lalle za a tashe ku?”
۞هَيۡهَاتَ هَيۡهَاتَ لِمَا تُوعَدُونَ
“Faufau-faufau game da abin da ake yi muku alqawarinsa!
إِنۡ هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا ٱلدُّنۡيَا نَمُوتُ وَنَحۡيَا وَمَا نَحۡنُ بِمَبۡعُوثِينَ
“Ba mu da wata (rayuwa) sai rayuwarmu ta duniya; mu mutu kuma mu rayu, ba kuwa za a tashe mu (daga qaburburanmu) ba
إِنۡ هُوَ إِلَّا رَجُلٌ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا وَمَا نَحۡنُ لَهُۥ بِمُؤۡمِنِينَ
“Shi ba kowa ba ne face mutum da ya qaga wa Allah qarya, mu kuwa ba za mu yi imani da shi ba.”
قَالَ رَبِّ ٱنصُرۡنِي بِمَا كَذَّبُونِ
Ya ce: “Ya Ubangijina, Ka taimake ni game da abin da suke qaryata ni a kansa.”
قَالَ عَمَّا قَلِيلٖ لَّيُصۡبِحُنَّ نَٰدِمِينَ
Ya ce: “Ba da daxewa ba tabbas za su wayi gari suna masu nadama.”
فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّيۡحَةُ بِٱلۡحَقِّ فَجَعَلۡنَٰهُمۡ غُثَآءٗۚ فَبُعۡدٗا لِّلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Sai tsawa ta far musu bisa cancanta, sai Muka mai da su dudduga. To nisanta (daga rahamar Allah) ta tabbata ga mutane azzalumai
ثُمَّ أَنشَأۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِمۡ قُرُونًا ءَاخَرِينَ
Sannan kuma a bayansu Muka halitta wasu al’ummun daban
مَا تَسۡبِقُ مِنۡ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ
Babu wata al’umma da take rigayar ajalinta, babu kuma wadda take jinkiri
ثُمَّ أَرۡسَلۡنَا رُسُلَنَا تَتۡرَاۖ كُلَّ مَا جَآءَ أُمَّةٗ رَّسُولُهَا كَذَّبُوهُۖ فَأَتۡبَعۡنَا بَعۡضَهُم بَعۡضٗا وَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَحَادِيثَۚ فَبُعۡدٗا لِّقَوۡمٖ لَّا يُؤۡمِنُونَ
Sannan Muka aiko manzanninmu suna biye da juna; duk sanda manzon (kowacce) al’umma ya zo musu sai su qaryata shi. Sai Muka hallaka su xaya bayan xaya, Muka kuma mai da su tarihi. To nisanta (daga rahamar Allah) ta tabbata ga mutanen da ba sa yin imani
ثُمَّ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ وَأَخَاهُ هَٰرُونَ بِـَٔايَٰتِنَا وَسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ
Sannan Muka aiko Musa da xan’uwansa Haruna da ayoyinmu da kuma hujja bayyananniya
إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمًا عَالِينَ
Zuwa ga Fir’auna da manyan (‘yan majalisarsa), sai suka yi girman kai kuma suka kasance mutane masu haike wa (jama’a da zalunci)
فَقَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ لِبَشَرَيۡنِ مِثۡلِنَا وَقَوۡمُهُمَا لَنَا عَٰبِدُونَ
Sai suka ce: “Yanzu ma ba da gaskiya da mutum biyu irinmu, alhali kuwa mutanensu masu yi mana bauta ne?”
فَكَذَّبُوهُمَا فَكَانُواْ مِنَ ٱلۡمُهۡلَكِينَ
Sai suka qaryata su (wato Musa da Haruna), sannan suka kasance daga waxanda aka hallaka
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ لَعَلَّهُمۡ يَهۡتَدُونَ
Haqiqa kuma Mun bai wa Musa Littafi (wato Attaura) don su shiriya
وَجَعَلۡنَا ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَأُمَّهُۥٓ ءَايَةٗ وَءَاوَيۡنَٰهُمَآ إِلَىٰ رَبۡوَةٖ ذَاتِ قَرَارٖ وَمَعِينٖ
Muka kuma sanya Xan Maryamu da mahaifiyarsa (don su zama) aya, Muka kuma zaunar da su a wata jigawa ta hutawa da kuma ruwa mai gudana
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلرُّسُلُ كُلُواْ مِنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَٱعۡمَلُواْ صَٰلِحًاۖ إِنِّي بِمَا تَعۡمَلُونَ عَلِيمٞ
Ya ku manzanni, ku ci daga halal, kuma ku yi aiki na gari; Lalle Ni ina sane da abin da kuke aikatawa
وَإِنَّ هَٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَأَنَا۠ رَبُّكُمۡ فَٱتَّقُونِ
Kuma lalle wannan addininku ne, addini guda xaya (wato Musulunci), kuma Ni ne Ubangijinku, sai ku kiyaye dokokina
فَتَقَطَّعُوٓاْ أَمۡرَهُم بَيۡنَهُمۡ زُبُرٗاۖ كُلُّ حِزۡبِۭ بِمَا لَدَيۡهِمۡ فَرِحُونَ
Sai suka sassava al’amarinsu a tsakaninsu (suka kasu) qungiya-qungiya; kowacce qungiya tana alfahari da nata
فَذَرۡهُمۡ فِي غَمۡرَتِهِمۡ حَتَّىٰ حِينٍ
Sai ka bar su cikin ximuwarsu har zuwa xan wani lokaci
أَيَحۡسَبُونَ أَنَّمَا نُمِدُّهُم بِهِۦ مِن مَّالٖ وَبَنِينَ
Yanzu suna tsammanin cewa abin da Muke ba su na dukiya da ‘ya’yaye (a duniya)
نُسَارِعُ لَهُمۡ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِۚ بَل لَّا يَشۡعُرُونَ
Muna gaggauto musu sakamakon alheri ne? Ba haka ba ne; su dai ba sa ganewa ne
إِنَّ ٱلَّذِينَ هُم مِّنۡ خَشۡيَةِ رَبِّهِم مُّشۡفِقُونَ
Lalle waxanda su suke cike da tsoron Ubangijinsu
وَٱلَّذِينَ هُم بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ يُؤۡمِنُونَ
Kuma waxanda suke imani da ayoyin Ubangijinsu
وَٱلَّذِينَ هُم بِرَبِّهِمۡ لَا يُشۡرِكُونَ
Kuma waxanda ba sa shirka da Ubangijinsu
وَٱلَّذِينَ يُؤۡتُونَ مَآ ءَاتَواْ وَّقُلُوبُهُمۡ وَجِلَةٌ أَنَّهُمۡ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ رَٰجِعُونَ
Kuma waxanda suke ba da abin da suka bayar (na ayyukan kirki), alhali kuwa zukatansu suna tsorace[1], don kuwa lalle su masu komawa ne zuwa ga Ubangijinsu
1- Watau suna cike da tsoron za a karva ko ba za a karva ba.