Sura: Suratul Baqara

Aya : 271

إِن تُبۡدُواْ ٱلصَّدَقَٰتِ فَنِعِمَّا هِيَۖ وَإِن تُخۡفُوهَا وَتُؤۡتُوهَا ٱلۡفُقَرَآءَ فَهُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡۚ وَيُكَفِّرُ عَنكُم مِّن سَيِّـَٔاتِكُمۡۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

In da za ku bayyanar da sadakoki a fili, to madalla da hakan, kuma idan kuka voye sadaqar, kuma kuka ba da ita ga talakawa, to hakan shi ya fi alheri a gare ku, kuma zai kankare muku kurakurenku, kuma Allah Masanin abin da kuke aikatawa ne



Sura: Suratul Baqara

Aya : 272

۞لَّيۡسَ عَلَيۡكَ هُدَىٰهُمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَهۡدِي مَن يَشَآءُۗ وَمَا تُنفِقُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَلِأَنفُسِكُمۡۚ وَمَا تُنفِقُونَ إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ ٱللَّهِۚ وَمَا تُنفِقُواْ مِنۡ خَيۡرٖ يُوَفَّ إِلَيۡكُمۡ وَأَنتُمۡ لَا تُظۡلَمُونَ

Shiryar da su ba a kanka yake ba, sai dai Allah ne Yake shiryar da wanda Ya ga dama, kuma duk abin da kuka ciyar na alheri, to domin kawunanku ne, kuma ba za ku ciyar ba sai don neman yardar Allah; kuma duk abin da kuka ciyar na alheri, za a cika muku ladansa, alhali kuma ba za a zalunce ku ba



Sura: Suratul Baqara

Aya : 273

لِلۡفُقَرَآءِ ٱلَّذِينَ أُحۡصِرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ لَا يَسۡتَطِيعُونَ ضَرۡبٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ يَحۡسَبُهُمُ ٱلۡجَاهِلُ أَغۡنِيَآءَ مِنَ ٱلتَّعَفُّفِ تَعۡرِفُهُم بِسِيمَٰهُمۡ لَا يَسۡـَٔلُونَ ٱلنَّاسَ إِلۡحَافٗاۗ وَمَا تُنفِقُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٌ

Ga mabuqata waxanda aka tsare saboda Allah, ba su da ikon yawatawa a bayan qasa, har wanda ya jahilci halinsu yana zato su mawadata ne saboda kame kai; za ka gane su ne da alamominsu, ba sa naciyar roqar mutane, kuma duk abin da kuka ciyar na alheri, to Allah Yana sane da shi



Sura: Suratul Baqara

Aya : 274

ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُم بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ فَلَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Waxanda suke ciyar da dukiyoyinsu dare da rana a voye da kuma a sarari, to suna da ladansu a wajen Ubangijinsu, kuma babu tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba



Sura: Suratul Baqara

Aya : 275

ٱلَّذِينَ يَأۡكُلُونَ ٱلرِّبَوٰاْ لَا يَقُومُونَ إِلَّا كَمَا يَقُومُ ٱلَّذِي يَتَخَبَّطُهُ ٱلشَّيۡطَٰنُ مِنَ ٱلۡمَسِّۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَالُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡبَيۡعُ مِثۡلُ ٱلرِّبَوٰاْۗ وَأَحَلَّ ٱللَّهُ ٱلۡبَيۡعَ وَحَرَّمَ ٱلرِّبَوٰاْۚ فَمَن جَآءَهُۥ مَوۡعِظَةٞ مِّن رَّبِّهِۦ فَٱنتَهَىٰ فَلَهُۥ مَا سَلَفَ وَأَمۡرُهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِۖ وَمَنۡ عَادَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Waxanda suke cin riba ba za su tashi ba (daga qaburburansu) sai kamar tashin mutumin da Shaixan yake bige shi da hauka. Hakan zai faru ne don sun ce: “Lalle kasuwanci kamar riba yake.” Kuma Allah Ya halatta kasuwanci, kuma Ya haramta riba. To duk wanda wa’azi ya zo masa daga wurin Ubangijinsa, sai ya daina, to abin da ya wuce a baya ya zama nasa, kuma al’amarinsa yana wurin Allah; wanda kuma ya sake komawa daga baya, to waxannan su ne ma’abota wuta, suna masu dawwama a cikinta



Sura: Suratul Baqara

Aya : 276

يَمۡحَقُ ٱللَّهُ ٱلرِّبَوٰاْ وَيُرۡبِي ٱلصَّدَقَٰتِۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ كَفَّارٍ أَثِيمٍ

Allah Yana shafe albarkar riba, Yana kuma havaka sadaqa. Kuma Allah ba Ya son dukkan wani mai yawan kafircewa, mai yawan savo



Sura: Suratul Baqara

Aya : 277

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ لَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Lalle waxanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka nagari kuma suka tsayar da salla, kuma suka bayar da zakka, to suna da ladansu a wajen Ubangijinsu, kuma babu jin tsoro a gare su, kuma ba za su yi baqin ciki ba



Sura: Suratul Baqara

Aya : 278

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَذَرُواْ مَا بَقِيَ مِنَ ٱلرِّبَوٰٓاْ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku rabu da abin da ya yi ragowa na riba in har kun kasance muminai



Sura: Suratul Baqara

Aya : 279

فَإِن لَّمۡ تَفۡعَلُواْ فَأۡذَنُواْ بِحَرۡبٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۖ وَإِن تُبۡتُمۡ فَلَكُمۡ رُءُوسُ أَمۡوَٰلِكُمۡ لَا تَظۡلِمُونَ وَلَا تُظۡلَمُونَ

Idan kuwa ba ku aikata haka ba, to ku saurari wani yaqi daga Allah da Manzonsa; idan kuwa kun tuba, to uwar kuxin taku ce, ba za ku yi zalunci ba, ku ma kuma ba za a zalunce ku ba



Sura: Suratul Baqara

Aya : 280

وَإِن كَانَ ذُو عُسۡرَةٖ فَنَظِرَةٌ إِلَىٰ مَيۡسَرَةٖۚ وَأَن تَصَدَّقُواْ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Kuma idan (mai cin bashin) ya kasance ma’abocin matsi, to sai a yi masa jinkiri zuwa lokacin da zai sami sauqi, kuma in da za ku yi sadaqa shi ya fi alheri a gare ku in kun kasance kuna da masaniya



Sura: Suratul Baqara

Aya : 281

وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا تُرۡجَعُونَ فِيهِ إِلَى ٱللَّهِۖ ثُمَّ تُوَفَّىٰ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Kuma ku kiyayi wani yini da za a mayar da ku zuwa ga Allah a cikinsa, sannan kowane rai za a cika masa abin da ya aiwatar na aiki, kuma su ba za a zalunce su ba



Sura: Suratul Baqara

Aya : 282

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا تَدَايَنتُم بِدَيۡنٍ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى فَٱكۡتُبُوهُۚ وَلۡيَكۡتُب بَّيۡنَكُمۡ كَاتِبُۢ بِٱلۡعَدۡلِۚ وَلَا يَأۡبَ كَاتِبٌ أَن يَكۡتُبَ كَمَا عَلَّمَهُ ٱللَّهُۚ فَلۡيَكۡتُبۡ وَلۡيُمۡلِلِ ٱلَّذِي عَلَيۡهِ ٱلۡحَقُّ وَلۡيَتَّقِ ٱللَّهَ رَبَّهُۥ وَلَا يَبۡخَسۡ مِنۡهُ شَيۡـٔٗاۚ فَإِن كَانَ ٱلَّذِي عَلَيۡهِ ٱلۡحَقُّ سَفِيهًا أَوۡ ضَعِيفًا أَوۡ لَا يَسۡتَطِيعُ أَن يُمِلَّ هُوَ فَلۡيُمۡلِلۡ وَلِيُّهُۥ بِٱلۡعَدۡلِۚ وَٱسۡتَشۡهِدُواْ شَهِيدَيۡنِ مِن رِّجَالِكُمۡۖ فَإِن لَّمۡ يَكُونَا رَجُلَيۡنِ فَرَجُلٞ وَٱمۡرَأَتَانِ مِمَّن تَرۡضَوۡنَ مِنَ ٱلشُّهَدَآءِ أَن تَضِلَّ إِحۡدَىٰهُمَا فَتُذَكِّرَ إِحۡدَىٰهُمَا ٱلۡأُخۡرَىٰۚ وَلَا يَأۡبَ ٱلشُّهَدَآءُ إِذَا مَا دُعُواْۚ وَلَا تَسۡـَٔمُوٓاْ أَن تَكۡتُبُوهُ صَغِيرًا أَوۡ كَبِيرًا إِلَىٰٓ أَجَلِهِۦۚ ذَٰلِكُمۡ أَقۡسَطُ عِندَ ٱللَّهِ وَأَقۡوَمُ لِلشَّهَٰدَةِ وَأَدۡنَىٰٓ أَلَّا تَرۡتَابُوٓاْ إِلَّآ أَن تَكُونَ تِجَٰرَةً حَاضِرَةٗ تُدِيرُونَهَا بَيۡنَكُمۡ فَلَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَلَّا تَكۡتُبُوهَاۗ وَأَشۡهِدُوٓاْ إِذَا تَبَايَعۡتُمۡۚ وَلَا يُضَآرَّ كَاتِبٞ وَلَا شَهِيدٞۚ وَإِن تَفۡعَلُواْ فَإِنَّهُۥ فُسُوقُۢ بِكُمۡۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ وَيُعَلِّمُكُمُ ٱللَّهُۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka ba wa junanku bashi zuwa wani lokaci sananne, to ku rubuta shi, kuma a sami wani marubuci da zai rubuta a tsakaninku da adalci, kuma marubucin kar ya qi rubutawa kamar yadda Allah ya sanar da shi. Don haka ya rubuta, kuma shi wanda haqqi yake kansa sai ya yi shifta gare shi, kuma ya ji tsoron Allah Ubangijinsa, kuma kada ya tauye wani abu a cikinsa. To idan wanda haqqi yake kansa ya kasance wawa ne ko mai rauni ko ba shi da ikon ya yi shifta shi da kansa, to sai majivincin lamarinsa ya yi shifta (a madadinsa) da adalci. Kuma ku kafa shaidu biyu cikin mazajenku; kuma idan ba su kasance mazaje biyu ba, to sai a nemi namiji xaya da mata biyu daga shaidun da kuka yarda da su, saboda idan xaya daga cikinsu ta manta sai xayar ta tuna mata, kuma kada shaidun su qi zuwa idan an kiraye su, kuma kada ku qosa, ku rubuta shi, kaxan ne ko da yawa, zuwa cikar wa’adinsa. Abin da aka ambata mukun nan shi ne ya fi zama adalci a wajen Allah, kuma ya fi daidaita shaida, kuma shi ya fi kusata ku ta yadda ba za ku yi shakka ba, sai dai idan ya kasance ciniki ne hannu da hannu da kuke gudanar da shi tsakaninku; to babu laifi a kanku idan ba ku rubuta shi ba. Kuma ku kafa shaida idan kun yi hulxa ta ciniki, kuma kada marubuci ya yi cuta, haka shi ma mai shaida (kada ya yi cuta)[1]. Idan kuwa har kuka aikata haka, to lalle wannan fasiqanci ne a gare ku. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma Allah Yana sanar da ku (dokokinsa). Kuma Allah Masanin komai ne


1- Hakanan ayar tana nufin cewa, su ma kuma kada a cutar da su.


Sura: Suratul Baqara

Aya : 283

۞وَإِن كُنتُمۡ عَلَىٰ سَفَرٖ وَلَمۡ تَجِدُواْ كَاتِبٗا فَرِهَٰنٞ مَّقۡبُوضَةٞۖ فَإِنۡ أَمِنَ بَعۡضُكُم بَعۡضٗا فَلۡيُؤَدِّ ٱلَّذِي ٱؤۡتُمِنَ أَمَٰنَتَهُۥ وَلۡيَتَّقِ ٱللَّهَ رَبَّهُۥۗ وَلَا تَكۡتُمُواْ ٱلشَّهَٰدَةَۚ وَمَن يَكۡتُمۡهَا فَإِنَّهُۥٓ ءَاثِمٞ قَلۡبُهُۥۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ عَلِيمٞ

Kuma idan kun kasance a halin tafiya, kuma ba ku sami marubuci ba, to sai a ba da jingina da za a karva, kuma idan sashinku ya amince wa sashi, to shi wanda aka amincewan ya bayar da amanarsa, kuma ya kiyayi Allah Ubangijinsa. Kuma kada ku voye shaida; duk wanda ya voye ta kuwa, to lalle shi zuciyarsa a cike take da savo. Kuma Allah Masanin abin da kuke aikatawa ne



Sura: Suratul Baqara

Aya : 284

لِّلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَإِن تُبۡدُواْ مَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ أَوۡ تُخۡفُوهُ يُحَاسِبۡكُم بِهِ ٱللَّهُۖ فَيَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa na Allah ne. Kuma in har kuka bayyana abin da yake cikin zukatanku ko kuka voye shi, Allah zai yi muku hisabi a kansa, sai Ya yi gafara ga wanda Ya ga dama, Ya kuma yi azaba ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai



Sura: Suratul Baqara

Aya : 285

ءَامَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مِن رَّبِّهِۦ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَمَلَـٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّن رُّسُلِهِۦۚ وَقَالُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَاۖ غُفۡرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيۡكَ ٱلۡمَصِيرُ

Manzon ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa, muminai ma haka, kowanne ya yi imani da Allah da mala’ikunsa da littattafansa da manzanninsa, (suna cewa) : “Ba ma nuna bambanci tsakanin xaya daga cikin manzanninsa.” Kuma suka ce: “Mun ji kuma mun bi ; muna neman gafararka ya Ubangijinmu, kuma zuwa gare Ka ne makoma take



Sura: Suratul Baqara

Aya : 286

لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۚ لَهَا مَا كَسَبَتۡ وَعَلَيۡهَا مَا ٱكۡتَسَبَتۡۗ رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذۡنَآ إِن نَّسِينَآ أَوۡ أَخۡطَأۡنَاۚ رَبَّنَا وَلَا تَحۡمِلۡ عَلَيۡنَآ إِصۡرٗا كَمَا حَمَلۡتَهُۥ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِنَاۚ رَبَّنَا وَلَا تُحَمِّلۡنَا مَا لَا طَاقَةَ لَنَا بِهِۦۖ وَٱعۡفُ عَنَّا وَٱغۡفِرۡ لَنَا وَٱرۡحَمۡنَآۚ أَنتَ مَوۡلَىٰنَا فَٱنصُرۡنَا عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Allah ba Ya kallafa wa rai sai abin da zai iya. Abin da ya aikata (na alheri) nasa ne, hakanan sakamakon abin da ya aikata (na sharri) shi ma nasa ne. Ya Ubangijinmu, kada Ka riqe mu da laifi idan mun yi mantuwa ko mun yi kuskure. Ya Ubangijinmu, kada kuma Ka xora mana wani nauyi irin wanda ka xora wa waxanda suke gabaninmu. Ya Ubangijinmu, kada kuma Ka xora mana abin da ba mu da iko a kansa, kuma Ka yi mana afuwa, kuma Ka yi mana gafara, kuma Ka ji qan mu; Kai ne Majivincin lamarinmu, don haka Ka taimake mu a kan mutane kafirai