وَٱلۡمُرۡسَلَٰتِ عُرۡفٗا
Na rantse da iska mai bibiyar juna
Tarayya :
فَٱلۡعَٰصِفَٰتِ عَصۡفٗا
Da kuma iska mai tasowa da tsanani
وَٱلنَّـٰشِرَٰتِ نَشۡرٗا
Da iska mai watso ruwa watsowa
فَٱلۡفَٰرِقَٰتِ فَرۡقٗا
Da kuma (mala’iku) masu rarrabe qarya da gaskiya iya rarrabewa
فَٱلۡمُلۡقِيَٰتِ ذِكۡرًا
Sannan masu sauko da wahayi
عُذۡرًا أَوۡ نُذۡرًا
Don yanke hanzari ko don gargaxi
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَٰقِعٞ
Lalle abin da ake yi muku alqawari tabbas mai afkuwa ne
فَإِذَا ٱلنُّجُومُ طُمِسَتۡ
To idan taurari aka shafe haskensu
وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ فُرِجَتۡ
Idan kuma sama aka tsattsage ta
وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ نُسِفَتۡ
Idan kuma duwatsu aka sheqe su
وَإِذَا ٱلرُّسُلُ أُقِّتَتۡ
Idan kuma manzanni aka tattara su[1]
1- Watau don su ba da shaida cewa sun isar wa al’ummunnsu saqon Allah.
لِأَيِّ يَوۡمٍ أُجِّلَتۡ
Ga wacce rana ce aka qayyaje musu
لِيَوۡمِ ٱلۡفَصۡلِ
Ga rana ta yin hukunci[1]
1- Watau hukunci tsakanin bayi, a bayyana mai gaskiya da marar gaskiya da xan wuta da xan Aljanna.
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ
Me kuma ya sanar da kai ranar yin hukunci
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu qaryatawa
أَلَمۡ نُهۡلِكِ ٱلۡأَوَّلِينَ
Yanzu ba Mu hallakar da na farko ba?
ثُمَّ نُتۡبِعُهُمُ ٱلۡأٓخِرِينَ
Sannan Muka biyo su da na qarshe?
كَذَٰلِكَ نَفۡعَلُ بِٱلۡمُجۡرِمِينَ
Kamar haka Muke yi wa masu manyan laifuka
أَلَمۡ نَخۡلُقكُّم مِّن مَّآءٖ مَّهِينٖ
Yanzu ba Mu halicce ku daga wani wulaqantaccen ruwa ba?
فَجَعَلۡنَٰهُ فِي قَرَارٖ مَّكِينٍ
Sannan Muka sanya shi cikin matabbata mai aminci?
إِلَىٰ قَدَرٖ مَّعۡلُومٖ
Zuwa wani lokaci sananne?
فَقَدَرۡنَا فَنِعۡمَ ٱلۡقَٰدِرُونَ
Sannan Muka qaddara (komai ta yadda ya dace)? To madalla da Masu qaddarawa
أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ كِفَاتًا
Yanzu ba Mu sanya qasa (ta zama) matattara ba?
أَحۡيَآءٗ وَأَمۡوَٰتٗا
(Ga) rayayyu da matattu[1]?
1- Watau masu rai a cikin gidajensu a bayanta, matatu kuma a binne a cikin qaburburansu a qarqashinta.
وَجَعَلۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ شَٰمِخَٰتٖ وَأَسۡقَيۡنَٰكُم مَّآءٗ فُرَاتٗا
Muka kuma sanya kafaffun duwatsu dogaye a cikinta, Muka kuma shayar da ku ruwa mai daxi?
ٱنطَلِقُوٓاْ إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna qaryatawa
ٱنطَلِقُوٓاْ إِلَىٰ ظِلّٖ ذِي ثَلَٰثِ شُعَبٖ
Ku tafi zuwa wata inuwa mai rassa uku