طه
Xa Ha[1]
1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.
مَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡقُرۡءَانَ لِتَشۡقَىٰٓ
Ba Mu saukar maka da Alqur’ani don ka wahala ba
إِلَّا تَذۡكِرَةٗ لِّمَن يَخۡشَىٰ
Sai don wa’azi ga wanda zai ji tsoron (haxuwa da Allah)
تَنزِيلٗا مِّمَّنۡ خَلَقَ ٱلۡأَرۡضَ وَٱلسَّمَٰوَٰتِ ٱلۡعُلَى
Saukakke ne daga wanda Ya halicci qasa da sammai masu xaukaka
ٱلرَّحۡمَٰنُ عَلَى ٱلۡعَرۡشِ ٱسۡتَوَىٰ
(Allah) Mai rahama, Ya daidaita a kan Al’arshi[1]
1- Duba Suratul A’arafi, aya ta 54, hashiya ta 126.
لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا وَمَا تَحۡتَ ٱلثَّرَىٰ
Abin da yake sammai da qasa, da abin da yake tsakaninsu da kuma abin da yake qarqashin qasa, (duka) nasa ne
وَإِن تَجۡهَرۡ بِٱلۡقَوۡلِ فَإِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلسِّرَّ وَأَخۡفَى
Idan kuma ka xaga murya da furuci to lalle Shi Yana sane da sirri da abin da ya fi (sirri) vuya
ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ لَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰ
Allah (Shi ne wanda) babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi; Yana da sunaye mafiya kyau
وَهَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ
Shin kuwa labarin Musa ya zo maka?
إِذۡ رَءَا نَارٗا فَقَالَ لِأَهۡلِهِ ٱمۡكُثُوٓاْ إِنِّيٓ ءَانَسۡتُ نَارٗا لَّعَلِّيٓ ءَاتِيكُم مِّنۡهَا بِقَبَسٍ أَوۡ أَجِدُ عَلَى ٱلنَّارِ هُدٗى
Lokacin da ya gano wuta sai ya ce da iyalinsa: “Ku zauna (a nan), lalle ni fa na hangi wuta, (zan je) ko na zo muku da garwashinta ko kuma in sami mai nuna mini (hanya) a wurin wutar.”
فَلَمَّآ أَتَىٰهَا نُودِيَ يَٰمُوسَىٰٓ
To lokacin da ya zo wurinta (wato wutar), sai aka kira shi (cewa): “Ya Musa
إِنِّيٓ أَنَا۠ رَبُّكَ فَٱخۡلَعۡ نَعۡلَيۡكَ إِنَّكَ بِٱلۡوَادِ ٱلۡمُقَدَّسِ طُوٗى
“Lalle Ni, Ni ne fa Ubangijinka, sai ka tuve takalmanka; lalle kana a tsarkakakken kwarin Xuwa ne
وَأَنَا ٱخۡتَرۡتُكَ فَٱسۡتَمِعۡ لِمَا يُوحَىٰٓ
“Kuma Ni Na zave ka (da manzanci), sai ka ji abin da za a yiwo ma wahayi (da shi)
إِنَّنِيٓ أَنَا ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدۡنِي وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِذِكۡرِيٓ
“Lalle Ni, Ni ne Allah, babu wani abin bauta sai Ni, to ka bauta mini, kuma ka tsai da salla don tuna Ni
إِنَّ ٱلسَّاعَةَ ءَاتِيَةٌ أَكَادُ أُخۡفِيهَا لِتُجۡزَىٰ كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا تَسۡعَىٰ
“Lalle alqiyama za ta zo, ina nufin voye ta ne don a saka wa kowanne rai da irin abin da yake aikatawa
فَلَا يَصُدَّنَّكَ عَنۡهَا مَن لَّا يُؤۡمِنُ بِهَا وَٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ فَتَرۡدَىٰ
“To kada wanda bai yi imani da ita ba ya kuma bi son ransa ya hana ka gaskata ta, sai ka hallaka
وَمَا تِلۡكَ بِيَمِينِكَ يَٰمُوسَىٰ
“Mene ne kuma wancan yake a hannun damanka ya Musa?”
قَالَ هِيَ عَصَايَ أَتَوَكَّؤُاْ عَلَيۡهَا وَأَهُشُّ بِهَا عَلَىٰ غَنَمِي وَلِيَ فِيهَا مَـَٔارِبُ أُخۡرَىٰ
(Musa) ya ce: “Ai sandata ce da nake jingina a kanta, ina kuma kaxo wa dabbobina ganye da ita, ina kuma da sauran wasu buqatu game da ita.”
قَالَ أَلۡقِهَا يَٰمُوسَىٰ
(Allah) Ya ce: “Jefar da ita ya Musa.”
فَأَلۡقَىٰهَا فَإِذَا هِيَ حَيَّةٞ تَسۡعَىٰ
Sai ya jefar da ita, sai ga ta ta zama macijiya tana ta sauri
قَالَ خُذۡهَا وَلَا تَخَفۡۖ سَنُعِيدُهَا سِيرَتَهَا ٱلۡأُولَىٰ
Ya ce: “Kama ta, kuma kada ka ji tsoro; za Mu mai da ita kamar yadda take a da
وَٱضۡمُمۡ يَدَكَ إِلَىٰ جَنَاحِكَ تَخۡرُجۡ بَيۡضَآءَ مِنۡ غَيۡرِ سُوٓءٍ ءَايَةً أُخۡرَىٰ
“Kuma ka haxa hannunka da kwivinka zai fito fari sal ba tare da wata cuta ba; (wannan) wata ayar ce daban
لِنُرِيَكَ مِنۡ ءَايَٰتِنَا ٱلۡكُبۡرَى
“Domin Mu nuna maka irin manya-manyan ayoyinmu
ٱذۡهَبۡ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ
“Ka tafi wurin Fir’auna don kuwa lalle ya qetare iyaka.”
قَالَ رَبِّ ٱشۡرَحۡ لِي صَدۡرِي
(Musa) ya ce: “Ubangijina Ka buxe mini qirjina[1]
1- Watau ya cire masa in’ina da take damun sa.
وَيَسِّرۡ لِيٓ أَمۡرِي
“Kuma Ka sauqaqa mini lamarina
وَٱحۡلُلۡ عُقۡدَةٗ مِّن لِّسَانِي
“Ka kuma warware qullin da yake a harshena
يَفۡقَهُواْ قَوۡلِي
“(Don) su fahimci maganata
وَٱجۡعَل لِّي وَزِيرٗا مِّنۡ أَهۡلِي
“Kuma Ka sanya mini waziri daga dangina
هَٰرُونَ أَخِي
“(Watau) xau’uwana Haruna