إِنَّآ أَنزَلۡنَٰهُ فِي لَيۡلَةِ ٱلۡقَدۡرِ
Lalle Mu Muka saukar da shi (Alqur’ani) a daren Lailatul-Qadari[1] (dare mai daraja)
1- Watau lokacin da aka fara saukar da jumullarsa a sama ta kusa, kamar yadda a cikin watan Ramadana ne ake fara saukar da shi ga Manzon Allah () a kogon Hira.
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا لَيۡلَةُ ٱلۡقَدۡرِ
Mene ne ya sanar da kai mece ce Lailatul-Qadari?
لَيۡلَةُ ٱلۡقَدۡرِ خَيۡرٞ مِّنۡ أَلۡفِ شَهۡرٖ
(Daren) Lailatul-Qadari ya fi wata dubu alheri
تَنَزَّلُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ فِيهَا بِإِذۡنِ رَبِّهِم مِّن كُلِّ أَمۡرٖ
Mala’iku da Jibrilu suna ta saukowa da dukkanin al’amura a cikinsa da izinin Ubangijinsu
سَلَٰمٌ هِيَ حَتَّىٰ مَطۡلَعِ ٱلۡفَجۡرِ
Aminci ne shi (daren dukkansa) har zuwa hudowar alfijir