سوره: Suratus Shams

آيه : 1

وَٱلشَّمۡسِ وَضُحَىٰهَا

Na rantse da rana da walaharta



سوره: Suratus Shams

آيه : 2

وَٱلۡقَمَرِ إِذَا تَلَىٰهَا

Da kuma wata idan ya bi ta (wato ranar)[1]


1- Watau ya biyo bayan faxuwar rana.


سوره: Suratus Shams

آيه : 3

وَٱلنَّهَارِ إِذَا جَلَّىٰهَا

Da kuma wuni idan ya bayyana ta



سوره: Suratus Shams

آيه : 4

وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَغۡشَىٰهَا

Da kuma dare idan ya lulluve ta



سوره: Suratus Shams

آيه : 5

وَٱلسَّمَآءِ وَمَا بَنَىٰهَا

Da kuma sama da gininta



سوره: Suratus Shams

آيه : 6

وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا طَحَىٰهَا

Da kuma qasa da shimfixarta



سوره: Suratus Shams

آيه : 7

وَنَفۡسٖ وَمَا سَوَّىٰهَا

Da kuma rai da daidaitarsa



سوره: Suratus Shams

آيه : 8

فَأَلۡهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقۡوَىٰهَا

Sai Ya kimsa masa (gane) lalacewarsa da taqawarsa



سوره: Suratus Shams

آيه : 9

قَدۡ أَفۡلَحَ مَن زَكَّىٰهَا

Haqiqa wanda ya tsarkake shi (ran) ya rabauta



سوره: Suratus Shams

آيه : 10

وَقَدۡ خَابَ مَن دَسَّىٰهَا

Haqiqa kuma wanda ya binne shi da savo ya tave



سوره: Suratus Shams

آيه : 11

كَذَّبَتۡ ثَمُودُ بِطَغۡوَىٰهَآ

Samudawa sun qaryata saboda xagawarsu



سوره: Suratus Shams

آيه : 12

إِذِ ٱنۢبَعَثَ أَشۡقَىٰهَا

Yayin da mafi tsagerancinsu ya zabura



سوره: Suratus Shams

آيه : 13

فَقَالَ لَهُمۡ رَسُولُ ٱللَّهِ نَاقَةَ ٱللَّهِ وَسُقۡيَٰهَا

Sai Manzon Allah[1] ya ce da su: “Ku bar taguwar Allah da (ranar) shanta.”


1- Watau Annabi Salihu ().


سوره: Suratus Shams

آيه : 14

فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمۡدَمَ عَلَيۡهِمۡ رَبُّهُم بِذَنۢبِهِمۡ فَسَوَّىٰهَا

Sai suka qaryata shi sannan suka soke ta, sai Ubangijinsu Ya kama su da azaba saboda zunubinsu, sai Ya daidaita ta (watau qabilar wajen azaba)



سوره: Suratus Shams

آيه : 15

وَلَا يَخَافُ عُقۡبَٰهَا

Kuma ba Ya tsoron abin da zai biyo bayanta[1]


1- Watau ba ya jin tsoron wani abu da hallaka su za ta haifar nan gaba.