هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلۡغَٰشِيَةِ
Shin labarin mai lulluvewa da (tsoro) ya zo maka?
وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٍ خَٰشِعَةٌ
Wasu fuskoki a wannan ranar qasqantattu ne
عَامِلَةٞ نَّاصِبَةٞ
Masu aiki ne (tuquru)[1] masu shan wahala
1- Watau a wutar Jahannama.
تَصۡلَىٰ نَارًا حَامِيَةٗ
Za su shiga wuta mai tsananin quna
تُسۡقَىٰ مِنۡ عَيۡنٍ ءَانِيَةٖ
Za a shayar da su daga idon ruwa mai tsananin zafi
لَّيۡسَ لَهُمۡ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٖ
Ba su da wani abinci sai na qayar tsidau
لَّا يُسۡمِنُ وَلَا يُغۡنِي مِن جُوعٖ
Ba ya sa qiba kuma ba ya maganin yunwa
وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ نَّاعِمَةٞ
Waxansu fuskokin kuwa a wannan ranar ni’imtattu ne
لِّسَعۡيِهَا رَاضِيَةٞ
Masu gamsuwa ne da (sakamakon) ayyukansu
فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٖ
(Suna) cikin Aljanna maxaukakiya[1]
1- Watau xaukaka ta daraja da xaukaka ta muhalli, domin gidajen Aljanna benaye ne wasu kan wasu.
لَّا تَسۡمَعُ فِيهَا لَٰغِيَةٗ
Ba a jin zancen banza a cikinta
فِيهَا عَيۡنٞ جَارِيَةٞ
A cikinta akwai marmaro mai gudana
فِيهَا سُرُرٞ مَّرۡفُوعَةٞ
A cikinta akwai gadaje maxaukaka
وَأَكۡوَابٞ مَّوۡضُوعَةٞ
Da kofuna a ajijjiye
وَنَمَارِقُ مَصۡفُوفَةٞ
Da matasan kai a jejjere
وَزَرَابِيُّ مَبۡثُوثَةٌ
Da dardumai a shisshimfixe
أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى ٱلۡإِبِلِ كَيۡفَ خُلِقَتۡ
Shin ba sa duban raqumi yadda aka halicce shi?
وَإِلَى ٱلسَّمَآءِ كَيۡفَ رُفِعَتۡ
Da kuma sama yadda aka xaga ta?
وَإِلَى ٱلۡجِبَالِ كَيۡفَ نُصِبَتۡ
Da kuma duwatsu yadda aka kakkafa su?
وَإِلَى ٱلۡأَرۡضِ كَيۡفَ سُطِحَتۡ
Da kuma qasa yadda aka shimfixa ta?
فَذَكِّرۡ إِنَّمَآ أَنتَ مُذَكِّرٞ
To ka yi wa’azi, lalle kai mai wa’azi ne kawai
لَّسۡتَ عَلَيۡهِم بِمُصَيۡطِرٍ
Kai ba mai tilasta su ba ne
إِلَّا مَن تَوَلَّىٰ وَكَفَرَ
Sai dai wanda ya ba da baya ya kuma kafirce
فَيُعَذِّبُهُ ٱللَّهُ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَكۡبَرَ
To Allah zai azabtar da shi azaba mafi girma[1]
1- Watau wutar Jahannama inda zai dawwama a cikinta har abada.
إِنَّ إِلَيۡنَآ إِيَابَهُمۡ
Lalle zuwa gare Mu ne makomarsu take
ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا حِسَابَهُم
Sannan kuma a kanmu ne hisabinsu yake