وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلۡبُرُوجِ
Na rantse da sama ma’abociyar manziloli[1]
1- Watau manziloli na rana da wata da taurari.
وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡمَوۡعُودِ
Da ranar da aka yi alqawarin zuwanta[1]
1- Watau ranar alqiyama.
وَشَاهِدٖ وَمَشۡهُودٖ
Da mai shaida[1] da kuma abin yi wa shaida
1- Watau kamar Annabi da zai ba da shaida game da al’ummarsa.
قُتِلَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡأُخۡدُودِ
An la’anci ma’abota rami (na azabtar da muminai)[1]
1- Wani azzalumin sarki ne da aka yi a Najrana ta qasar Yaman kafin aiko Annabi () wanda aka haqa masa rami aka hura wuta, ya riqa jefa muminai a cikinsa yana qona su da ransu.
ٱلنَّارِ ذَاتِ ٱلۡوَقُودِ
Na wuta mai ruruwa
إِذۡ هُمۡ عَلَيۡهَا قُعُودٞ
Yayin da suke zaune a gefenta
وَهُمۡ عَلَىٰ مَا يَفۡعَلُونَ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ شُهُودٞ
Alhali su suna kallon abin da suke aikata wa muminai
وَمَا نَقَمُواْ مِنۡهُمۡ إِلَّآ أَن يُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ
Babu kuwa abin da suke tuhumar su da shi sai don kawai sun yi imani da Allah Mabuwayi, Sha-yabo
ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ
Wanda Yake da mulkin sammai da qasa. Allah kuma Mai ganin komai ne
إِنَّ ٱلَّذِينَ فَتَنُواْ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ ثُمَّ لَمۡ يَتُوبُواْ فَلَهُمۡ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمۡ عَذَابُ ٱلۡحَرِيقِ
Lalle waxanda suka azabtar da muminai maza da muminai mata sannan ba su tuba ba, to suna da azabar Jahannama, suna kuma da azabar quna
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَهُمۡ جَنَّـٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡكَبِيرُ
Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari suna da gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu. Wannan kuwa shi ne babban rabo
إِنَّ بَطۡشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ
Lalle damqar Ubangijinka tabbas mai tsanani ce
إِنَّهُۥ هُوَ يُبۡدِئُ وَيُعِيدُ
Lalle Shi ne Yake farar (da komai) Yake kuma dawo (da shi)
وَهُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلۡوَدُودُ
Shi ne kuma Mai gafara, Mai qaunar (bayinsa na qwarai)
ذُو ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡمَجِيدُ
Ma’abocin Al’arshi Mai girma
فَعَّالٞ لِّمَا يُرِيدُ
Mai aikata abin da Yake nufi
هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلۡجُنُودِ
Shin labarin rundunoni ya zo maka?
فِرۡعَوۡنَ وَثَمُودَ
(Su ne) Fir’auna da Samudawa
بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي تَكۡذِيبٖ
A’a, su dai waxanda suka kafirta suna cikin qaryatawa ne
وَٱللَّهُ مِن وَرَآئِهِم مُّحِيطُۢ
Allah kuwa Yana kewaye da su (da iliminsa)
بَلۡ هُوَ قُرۡءَانٞ مَّجِيدٞ
A’a, shi dai Alqur’ani ne mai girma
فِي لَوۡحٖ مَّحۡفُوظِۭ
A cikin Lauhul-Mahafuzu