سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمُزَّمِّلُ

Ya kai wannan mai lulluva[1]!


1- Shi ne Manzon Allah () bayan an saukar masa da wahayin farko a kogon Hira, ya dawo gida a tsorace ya lulluva da tufafinsa.


سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 2

قُمِ ٱلَّيۡلَ إِلَّا قَلِيلٗا

Ka yi tsaiwar dare sai xan kaxan (daga cikinsa)



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 3

نِّصۡفَهُۥٓ أَوِ ٱنقُصۡ مِنۡهُ قَلِيلًا

Rabinsa ko kuma ka rage kaxan daga gare shi



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 4

أَوۡ زِدۡ عَلَيۡهِ وَرَتِّلِ ٱلۡقُرۡءَانَ تَرۡتِيلًا

Ko ka qara a kansa, ka kuma karanta Alqur’ani daki-daki



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 5

إِنَّا سَنُلۡقِي عَلَيۡكَ قَوۡلٗا ثَقِيلًا

Lalle Mu da sannu za Mu saukar maka da zance mai nauyi[1]


1- Watau Alqur’ani da zai yiwo masa wahayinsa.


سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 6

إِنَّ نَاشِئَةَ ٱلَّيۡلِ هِيَ أَشَدُّ وَطۡـٔٗا وَأَقۡوَمُ قِيلًا

Lalle tsayuwar dare ita ta fi tsananin dacewa (game da nutsuwa), ta kuma fi daidaitar magana[1]


1- Watau sallar dare ta fi dacewa da nutsuwar zuciya da taimakawa wajen fahimtar zance daidai.


سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 7

إِنَّ لَكَ فِي ٱلنَّهَارِ سَبۡحٗا طَوِيلٗا

Lalle da rana kana da harkoki masu yawa



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 8

وَٱذۡكُرِ ٱسۡمَ رَبِّكَ وَتَبَتَّلۡ إِلَيۡهِ تَبۡتِيلٗا

Ka kuma ambaci sunan Ubangijinka kuma ka yanke alaqarka da komai don bautarsa



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 9

رَّبُّ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ فَٱتَّخِذۡهُ وَكِيلٗا

(Shi ne) Ubangijin mahudar rana da mafaxar rana, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi, saboda haka ka riqe Shi Abin dogara



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 10

وَٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَٱهۡجُرۡهُمۡ هَجۡرٗا جَمِيلٗا

Kuma ka yi haquri a kan abin da suke faxa, kuma ka qaurace musu kyakkyawar qauracewa[1]


1- Watau qauracewar da babu cutarwa a cikinta.


سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 11

وَذَرۡنِي وَٱلۡمُكَذِّبِينَ أُوْلِي ٱلنَّعۡمَةِ وَمَهِّلۡهُمۡ قَلِيلًا

Ka kuma bar ni da masu qaryatawa ma’abota ni’ima, ka kuma xan saurara musu



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 12

إِنَّ لَدَيۡنَآ أَنكَالٗا وَجَحِيمٗا

Lalle a wurinmu akwai maruruwa da kuma (wutar) Jahimu



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 13

وَطَعَامٗا ذَا غُصَّةٖ وَعَذَابًا أَلِيمٗا

Da kuma abinci mai shaqewa da kuma azaba mai raxaxi



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 14

يَوۡمَ تَرۡجُفُ ٱلۡأَرۡضُ وَٱلۡجِبَالُ وَكَانَتِ ٱلۡجِبَالُ كَثِيبٗا مَّهِيلًا

A ranar da qasa da duwatsu za su girgiza, duwatsun kuma su kasance rairayi tilis



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 15

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡكُمۡ رَسُولٗا شَٰهِدًا عَلَيۡكُمۡ كَمَآ أَرۡسَلۡنَآ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ رَسُولٗا

Lalle Mu Muka aiko muku da Manzo yana mai shaida a kanku kamar yadda Muka aiko wani manzo zuwa ga Fir’auna



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 16

فَعَصَىٰ فِرۡعَوۡنُ ٱلرَّسُولَ فَأَخَذۡنَٰهُ أَخۡذٗا وَبِيلٗا

Sai Fir’auna ya sava wa Manzon, sai Muka kama shi kamu mai tsanani



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 17

فَكَيۡفَ تَتَّقُونَ إِن كَفَرۡتُمۡ يَوۡمٗا يَجۡعَلُ ٱلۡوِلۡدَٰنَ شِيبًا

Ta yaya idan kuka kafirta za ku iya kare kanku daga ranar da za ta mayar da yara qanana su zama masu furfura?



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 18

ٱلسَّمَآءُ مُنفَطِرُۢ بِهِۦۚ كَانَ وَعۡدُهُۥ مَفۡعُولًا

Sama za ta kece saboda ita (ranar). Alqawarinsa ya kasance abin aikatawa ne



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 19

إِنَّ هَٰذِهِۦ تَذۡكِرَةٞۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ سَبِيلًا

Lalle wannan wa’azi ne, saboda haka duk wanda ya ga dama sai ya kama hanya zuwa ga Ubangijinsa



سوره: Suratul Muzzammil

آيه : 20

۞إِنَّ رَبَّكَ يَعۡلَمُ أَنَّكَ تَقُومُ أَدۡنَىٰ مِن ثُلُثَيِ ٱلَّيۡلِ وَنِصۡفَهُۥ وَثُلُثَهُۥ وَطَآئِفَةٞ مِّنَ ٱلَّذِينَ مَعَكَۚ وَٱللَّهُ يُقَدِّرُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَۚ عَلِمَ أَن لَّن تُحۡصُوهُ فَتَابَ عَلَيۡكُمۡۖ فَٱقۡرَءُواْ مَا تَيَسَّرَ مِنَ ٱلۡقُرۡءَانِۚ عَلِمَ أَن سَيَكُونُ مِنكُم مَّرۡضَىٰ وَءَاخَرُونَ يَضۡرِبُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَبۡتَغُونَ مِن فَضۡلِ ٱللَّهِ وَءَاخَرُونَ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ فَٱقۡرَءُواْ مَا تَيَسَّرَ مِنۡهُۚ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَقۡرِضُواْ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗاۚ وَمَا تُقَدِّمُواْ لِأَنفُسِكُم مِّنۡ خَيۡرٖ تَجِدُوهُ عِندَ ٱللَّهِ هُوَ خَيۡرٗا وَأَعۡظَمَ أَجۡرٗاۚ وَٱسۡتَغۡفِرُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمُۢ

Lalle Ubangijinka Yana sane da cewa kai kana tsayawa qasa da kashi biyu cikin uku na dare, da kuma rabinsa, da kuma xaya bisa ukunsa, kai da wata jama’ar da take tare da kai. Allah ne kuma Yake qaddara dare da rana. Ya san kuma cewa, ba za ku iya qididdige (sa’o’insa) ba, don haka sai Ya yafe muku; to sai ku karanta abin da ya sauqaqa daga Alqur’ani. Ya san cewa daga cikinku akwai waxanda za su kasance marasa lafiya, waxansu kuma suna tafiya a bayan qasa don fatauci suna neman falala daga Allah, waxansu kuma suna yin yaqi saboda Allah; to sai ku karanta abin da ya sauqaqa daga gare shi (Alqur’ani). Ku kuma tsayar da salla, ku kuma ba da zakka, kuma ku bai wa Allah rance kyakkyawa[1]. Kuma abin da kuka gabatar wa kanku na wani alheri, to za ku same shi wurin Allah, shi ya fi alheri ya kuma fi girman lada. Ku kuma nemi gafarar Allah; lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai


1- Watau su ciyar da dukiyoyinsu don Allah wuraren da suka dace.