سوره: Suratul Mulk

آيه : 1

تَبَٰرَكَ ٱلَّذِي بِيَدِهِ ٱلۡمُلۡكُ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Wanda mulki yake a hannunsa alhairansa sun yawaita, kuma Shi Mai iko ne a kan komai



سوره: Suratul Mulk

آيه : 2

ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡمَوۡتَ وَٱلۡحَيَوٰةَ لِيَبۡلُوَكُمۡ أَيُّكُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗاۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡغَفُورُ

Wanda Ya halicci mutuwa da rayuwa don Ya jarraba ku (Ya bayyana) wane ne a cikinku ya fi kyakkyawan aiki? Shi kuma Mabuwayi ne, Mai gafara



سوره: Suratul Mulk

آيه : 3

ٱلَّذِي خَلَقَ سَبۡعَ سَمَٰوَٰتٖ طِبَاقٗاۖ مَّا تَرَىٰ فِي خَلۡقِ ٱلرَّحۡمَٰنِ مِن تَفَٰوُتٖۖ فَٱرۡجِعِ ٱلۡبَصَرَ هَلۡ تَرَىٰ مِن فُطُورٖ

Wanda Ya halicci sammai bakwai hawa-hawa; ba za ka ga wata tangarxa cikin halittar (Allah) Mai rahama ba. Ka maimaita dubanka, shin za ka ga wata tsaga?



سوره: Suratul Mulk

آيه : 4

ثُمَّ ٱرۡجِعِ ٱلۡبَصَرَ كَرَّتَيۡنِ يَنقَلِبۡ إِلَيۡكَ ٱلۡبَصَرُ خَاسِئٗا وَهُوَ حَسِيرٞ

Sannan ka sake mayar da gani sau da yawa, ganin zai dawo maka a qasqance, shi kuma yana a dakushe (bai ga wata tsaga ba)



سوره: Suratul Mulk

آيه : 5

وَلَقَدۡ زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنۡيَا بِمَصَٰبِيحَ وَجَعَلۡنَٰهَا رُجُومٗا لِّلشَّيَٰطِينِۖ وَأَعۡتَدۡنَا لَهُمۡ عَذَابَ ٱلسَّعِيرِ

Kuma haqiqa Mun qawata saman duniya da taurari Muka sanya su kuma ababan jifan shaixanu[1]; Muka kuma tanadar musu azabar (wutar) Sa’ira


1- Watau jifar shaixanu masu qoqarin satar ji su qona su.


سوره: Suratul Mulk

آيه : 6

وَلِلَّذِينَ كَفَرُواْ بِرَبِّهِمۡ عَذَابُ جَهَنَّمَۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

Waxanda kuma suka kafirce wa Ubangijinsu suna da azabar Jahannama; makoma kuwa ta munana



سوره: Suratul Mulk

آيه : 7

إِذَآ أُلۡقُواْ فِيهَا سَمِعُواْ لَهَا شَهِيقٗا وَهِيَ تَفُورُ

Idan aka jefa su a cikinta sai su ji kururuwarta, tana tafarfasa



سوره: Suratul Mulk

آيه : 8

تَكَادُ تَمَيَّزُ مِنَ ٱلۡغَيۡظِۖ كُلَّمَآ أُلۡقِيَ فِيهَا فَوۡجٞ سَأَلَهُمۡ خَزَنَتُهَآ أَلَمۡ يَأۡتِكُمۡ نَذِيرٞ

Tana kusa da ta kekkece saboda tsananin fushi; duk sanda aka jefa wata tawaga a cikinta sai masu tsaron ta su tambaye su: “Shin mai gargaxi bai zo muku ba?”



سوره: Suratul Mulk

آيه : 9

قَالُواْ بَلَىٰ قَدۡ جَآءَنَا نَذِيرٞ فَكَذَّبۡنَا وَقُلۡنَا مَا نَزَّلَ ٱللَّهُ مِن شَيۡءٍ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا فِي ضَلَٰلٖ كَبِيرٖ

Sai su ce, “E, haka ne, haqiqa mai gargaxi ya zo mana, sai muka qaryata, muka kuma ce, Allah bai saukar da wani abu ba, ba kwa a kan komai sai vata mai girma.”



سوره: Suratul Mulk

آيه : 10

وَقَالُواْ لَوۡ كُنَّا نَسۡمَعُ أَوۡ نَعۡقِلُ مَا كُنَّا فِيٓ أَصۡحَٰبِ ٱلسَّعِيرِ

Suka kuma ce: “Da mun kasance muna fahimta ko kuma muna hankalta, to da ba mu kasance cikin ‘yan (wutar) Sa’ira ba.”



سوره: Suratul Mulk

آيه : 11

فَٱعۡتَرَفُواْ بِذَنۢبِهِمۡ فَسُحۡقٗا لِّأَصۡحَٰبِ ٱلسَّعِيرِ

Sai suka amsa laifinsu, sai (a ce da su): “Can dai da ‘yan (wutar) Sa’ira.”



سوره: Suratul Mulk

آيه : 12

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَخۡشَوۡنَ رَبَّهُم بِٱلۡغَيۡبِ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَأَجۡرٞ كَبِيرٞ

Lalle waxanda suke tsoron Ubangijinsu ba tare da suna ganin sa ba, suna da gafara da kuma lada mai girma



سوره: Suratul Mulk

آيه : 13

وَأَسِرُّواْ قَوۡلَكُمۡ أَوِ ٱجۡهَرُواْ بِهِۦٓۖ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

Da ku voye zancenku ko ku bayyana shi, lalle Shi Masanin abin da yake cikin zukata ne



سوره: Suratul Mulk

آيه : 14

أَلَا يَعۡلَمُ مَنۡ خَلَقَ وَهُوَ ٱللَّطِيفُ ٱلۡخَبِيرُ

Yanzu wanda ya yi halitta ba zai san ta ba? Shi ne kuma Mai tausasawa Masani



سوره: Suratul Mulk

آيه : 15

هُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ ذَلُولٗا فَٱمۡشُواْ فِي مَنَاكِبِهَا وَكُلُواْ مِن رِّزۡقِهِۦۖ وَإِلَيۡهِ ٱلنُّشُورُ

Shi ne wanda Ya sanya muku qasa horarriya[1], saboda haka ku yi tafiya a cikin sasanninta kuma ku ci daga arzikinta; makoma kuwa zuwa gare Shi take


1- Watau ta zamanto mai sauqin zama da rayuwa a kanta, ba tare da tana tangal-tangal da su ba.


سوره: Suratul Mulk

آيه : 16

ءَأَمِنتُم مَّن فِي ٱلسَّمَآءِ أَن يَخۡسِفَ بِكُمُ ٱلۡأَرۡضَ فَإِذَا هِيَ تَمُورُ

Yanzu kun amince cewa wanda Yake sama Ya kifar da qasa da ku, sai kawai ku gan ta tana ta tambal-tambal?



سوره: Suratul Mulk

آيه : 17

أَمۡ أَمِنتُم مَّن فِي ٱلسَّمَآءِ أَن يُرۡسِلَ عَلَيۡكُمۡ حَاصِبٗاۖ فَسَتَعۡلَمُونَ كَيۡفَ نَذِيرِ

Ko kuma kun amince cewa wanda Yake sama Ya aiko muku da guguwa mai tsakwankwani? To da sannu za ku san yadda (sakamakon) gargaxina zai zama



سوره: Suratul Mulk

آيه : 18

وَلَقَدۡ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ فَكَيۡفَ كَانَ نَكِيرِ

Haqiqa kuma waxanda suke gabaninku sun qaryata, to yaya (sakamakon) nuna qin amincewata ya zama?



سوره: Suratul Mulk

آيه : 19

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَى ٱلطَّيۡرِ فَوۡقَهُمۡ صَـٰٓفَّـٰتٖ وَيَقۡبِضۡنَۚ مَا يُمۡسِكُهُنَّ إِلَّا ٱلرَّحۡمَٰنُۚ إِنَّهُۥ بِكُلِّ شَيۡءِۭ بَصِيرٌ

Shin ba sa ganin tsuntsaye a samansu suna shimfixa (fikafikansu) suna kuma rufe su? Ba wanda yake riqe da su sai (Allah) Mai rahama. Lalle Shi Mai ganin komai ne



سوره: Suratul Mulk

آيه : 20

أَمَّنۡ هَٰذَا ٱلَّذِي هُوَ جُندٞ لَّكُمۡ يَنصُرُكُم مِّن دُونِ ٱلرَّحۡمَٰنِۚ إِنِ ٱلۡكَٰفِرُونَ إِلَّا فِي غُرُورٍ

Ko kuwa wace runduna ce kuke da ita da za ta taimaka muku ba (Allah) Mai rahama ba? Su dai kafirai ba sa kan komai sai ruxi



سوره: Suratul Mulk

آيه : 21

أَمَّنۡ هَٰذَا ٱلَّذِي يَرۡزُقُكُمۡ إِنۡ أَمۡسَكَ رِزۡقَهُۥۚ بَل لَّجُّواْ فِي عُتُوّٖ وَنُفُورٍ

Ko kuwa wane ne zai arzuta ku idan (Allah) Ya riqe arzikinsa? A’a, kawai dai sun yi zurfi ne cikin taurin kai da fanxarewa



سوره: Suratul Mulk

آيه : 22

أَفَمَن يَمۡشِي مُكِبًّا عَلَىٰ وَجۡهِهِۦٓ أَهۡدَىٰٓ أَمَّن يَمۡشِي سَوِيًّا عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Shin wanda yake tafiya a kife a kan fuskarsa shi ya fi zama a kan daidai ko kuma wanda yake tafiya a miqe kan hanya madaidaiciya?



سوره: Suratul Mulk

آيه : 23

قُلۡ هُوَ ٱلَّذِيٓ أَنشَأَكُمۡ وَجَعَلَ لَكُمُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَٱلۡأَفۡـِٔدَةَۚ قَلِيلٗا مَّا تَشۡكُرُونَ

Ka ce: “Shi ne (Allah) Wanda Ya fare ku Ya kuma sanya muku ji da gani da zukata; kaxan ne kawai kuke godewa.”



سوره: Suratul Mulk

آيه : 24

قُلۡ هُوَ ٱلَّذِي ذَرَأَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَإِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ

Ka ce: “Shi ne wanda Ya halicce ku a kan qasa, kuma zuwa gare Shi za a tattara ku.”



سوره: Suratul Mulk

آيه : 25

وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡوَعۡدُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Suna kuma cewa: “Yaushe ne wannan alqawarin, idan kun kasance masu gaskiya?”



سوره: Suratul Mulk

آيه : 26

قُلۡ إِنَّمَا ٱلۡعِلۡمُ عِندَ ٱللَّهِ وَإِنَّمَآ أَنَا۠ نَذِيرٞ مُّبِينٞ

Ka ce: “Saninsa yana wurin Allah kawai, kuma ni kawai mai gargaxi ne mai bayyana (gargaxin).”



سوره: Suratul Mulk

آيه : 27

فَلَمَّا رَأَوۡهُ زُلۡفَةٗ سِيٓـَٔتۡ وُجُوهُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَقِيلَ هَٰذَا ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تَدَّعُونَ

To lokacin da za su gan shi a kurkusa, sai fuskokin waxanda suka kafirce suka yi baqi, aka kuma ce: “Wannan ne abin da kuka kasance kuna neman zuwansa.”



سوره: Suratul Mulk

آيه : 28

قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِنۡ أَهۡلَكَنِيَ ٱللَّهُ وَمَن مَّعِيَ أَوۡ رَحِمَنَا فَمَن يُجِيرُ ٱلۡكَٰفِرِينَ مِنۡ عَذَابٍ أَلِيمٖ

Ka ce: “Ku ba ni labari, idan Allah Ya hallaka ni da waxanda suke tare da ni, ko kuma Ya ji qan mu, to wane ne zai kare kafirai daga azaba mai raxaxi?”



سوره: Suratul Mulk

آيه : 29

قُلۡ هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ءَامَنَّا بِهِۦ وَعَلَيۡهِ تَوَكَّلۡنَاۖ فَسَتَعۡلَمُونَ مَنۡ هُوَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ

Ka ce: “Shi ne (Allah) Mai rahama, mun yi imani da Shi, kuma a gare Shi muka dogara, to da sannu za ku san shin wane ne yake cikin vata mabayyani?”



سوره: Suratul Mulk

آيه : 30

قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِنۡ أَصۡبَحَ مَآؤُكُمۡ غَوۡرٗا فَمَن يَأۡتِيكُم بِمَآءٖ مَّعِينِۭ

Ka ce: “Ku ba ni labari, idan ruwanku ya wayi gari a qafe, to wane ne zai zo muku da ruwa mai vuvvugowa?”