ٱلرَّحۡمَٰنُ
(Allah) Mai rahama
عَلَّمَ ٱلۡقُرۡءَانَ
Shi Ya koyar da Alqur’ani
خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ
Ya halicci mutum
عَلَّمَهُ ٱلۡبَيَانَ
Ya koyar da shi bayani
ٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ بِحُسۡبَانٖ
Rana da wata (suna tafiya) a tsare
وَٱلنَّجۡمُ وَٱلشَّجَرُ يَسۡجُدَانِ
Tsirrai da bishiyoyi suna yin sujjada[1]
1- Watau tsirrai waxanda ba sa tashi tsaye da bishiyoyi masu tsayawa a kan sandunansu.
وَٱلسَّمَآءَ رَفَعَهَا وَوَضَعَ ٱلۡمِيزَانَ
Sama kuma Ya xaga ta, Ya kuma kafa adalci
أَلَّا تَطۡغَوۡاْ فِي ٱلۡمِيزَانِ
Don kada ku yi zalunci a abin awo
وَأَقِيمُواْ ٱلۡوَزۡنَ بِٱلۡقِسۡطِ وَلَا تُخۡسِرُواْ ٱلۡمِيزَانَ
Kuma ku tabbatar da awo da adalci kada kuma ku tauye abin awo
وَٱلۡأَرۡضَ وَضَعَهَا لِلۡأَنَامِ
Qasa kuma Ya yi ta saboda talikai
فِيهَا فَٰكِهَةٞ وَٱلنَّخۡلُ ذَاتُ ٱلۡأَكۡمَامِ
A cikinta akwai abin marmari da dabinai ma’abota kwasfa
وَٱلۡحَبُّ ذُو ٱلۡعَصۡفِ وَٱلرَّيۡحَانُ
Da qwayoyi ma’abota qaiqayi da kuma ganyaye masu qanshi
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
To da waxanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke qaryatawa?
خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِن صَلۡصَٰلٖ كَٱلۡفَخَّارِ
Ya halicci mutum daga busasshen tavo kamar kasko
وَخَلَقَ ٱلۡجَآنَّ مِن مَّارِجٖ مِّن نَّارٖ
Ya kuma halicci aljani daga harshen wuta
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Da waxanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke qaryatawa?
رَبُّ ٱلۡمَشۡرِقَيۡنِ وَرَبُّ ٱلۡمَغۡرِبَيۡنِ
Ubangijin mahudar rana biyu da mafaxarta biyu[1]
1- Watau a lokacin sanyi da kuma lokacin zafi.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Da waxanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke qaryatawa?
مَرَجَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ يَلۡتَقِيَانِ
Ya gudanar da koguna guda biyu suna haxuwa (da juna)
بَيۡنَهُمَا بَرۡزَخٞ لَّا يَبۡغِيَانِ
A tsakaninsu (kuma) akwai wani shamaki da ya hana su shiga juna
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Da waxanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke qaryatawa?
يَخۡرُجُ مِنۡهُمَا ٱللُّؤۡلُؤُ وَٱلۡمَرۡجَانُ
Lu’ulu’u da murjani suna fita daga cikinsu
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Da waxanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke qaryatawa?
وَلَهُ ٱلۡجَوَارِ ٱلۡمُنشَـَٔاتُ فِي ٱلۡبَحۡرِ كَٱلۡأَعۡلَٰمِ
Jiragen ruwa kuma da aka yi su suna gudu a cikin kogi kamar manya-manyan duwatsu nasa ne
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Da waxanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke qaryatawa?
كُلُّ مَنۡ عَلَيۡهَا فَانٖ
Dukkan wanda yake kanta (qasar) qararre ne
وَيَبۡقَىٰ وَجۡهُ رَبِّكَ ذُو ٱلۡجَلَٰلِ وَٱلۡإِكۡرَامِ
Fuskar Ubangijinka kuwa Ma’abocin girma da karamci ne kawai take wanzuwa
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Da waxanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke qaryatawa?
يَسۡـَٔلُهُۥ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ كُلَّ يَوۡمٍ هُوَ فِي شَأۡنٖ
Duk wanda yake cikin sammai da qasa yana roqon Sa. Kowane lokacin Shi a cikin wani sha’ani yake
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Da waxanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke qaryatawa?