قٓۚ وَٱلۡقُرۡءَانِ ٱلۡمَجِيدِ
QAF[1]. Na rantse da Alqur’ani mai girma
1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.
بَلۡ عَجِبُوٓاْ أَن جَآءَهُم مُّنذِرٞ مِّنۡهُمۡ فَقَالَ ٱلۡكَٰفِرُونَ هَٰذَا شَيۡءٌ عَجِيبٌ
A’a, sun dai yi mamakin cewa, wani mai gargaxi daga cikinsu ya zo musu, sai kafirai suka ce: “Wannan abu ne mai ban mamaki!
أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗاۖ ذَٰلِكَ رَجۡعُۢ بَعِيدٞ
“Yanzu idan muka mutu muka zama qasa, (a ce za a komo da mu)? Wannan komowa ce mai nisa!”
قَدۡ عَلِمۡنَا مَا تَنقُصُ ٱلۡأَرۡضُ مِنۡهُمۡۖ وَعِندَنَا كِتَٰبٌ حَفِيظُۢ
Haqiqa Mun san abin da qasa take cinyewa daga gare su; a wurinmu kuma akwai wani littafi mai kiyayewa[1]
1- Watau Lauhul Mahfuz.
بَلۡ كَذَّبُواْ بِٱلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمۡ فَهُمۡ فِيٓ أَمۡرٖ مَّرِيجٍ
A’a, sun dai qaryata gaskiya ne lokacin da ta zo musu, don haka suna cikin al’amari rikitacce[1]
1- Watau game da Manzon Allah (), wani lokaci su ce matsafi ne, wani lokaci kuma su ce boka ne, wani lokaci kuma su ce mawaqi ne.
أَفَلَمۡ يَنظُرُوٓاْ إِلَى ٱلسَّمَآءِ فَوۡقَهُمۡ كَيۡفَ بَنَيۡنَٰهَا وَزَيَّنَّـٰهَا وَمَا لَهَا مِن فُرُوجٖ
Yanzu ba sa duban sama da take sama da su (su ga) yadda Muka gina ta, Muka kuma qawata ta, ba ta kuma da wasu tsage-tsage?
وَٱلۡأَرۡضَ مَدَدۡنَٰهَا وَأَلۡقَيۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ وَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوۡجِۭ بَهِيجٖ
Qasa kuma Muka shimfixa ta, Muka kuma sanya turaku a cikinta, Muka kuma tsirar da kowane irin nau’in (tsiro) mai qayatarwa a cikinta
تَبۡصِرَةٗ وَذِكۡرَىٰ لِكُلِّ عَبۡدٖ مُّنِيبٖ
Don jan hankali da wa’azantarwa ga duk wani bawa mai mayar da al’amarinsa ga Allah
وَنَزَّلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ مُّبَٰرَكٗا فَأَنۢبَتۡنَا بِهِۦ جَنَّـٰتٖ وَحَبَّ ٱلۡحَصِيدِ
Muka kuma saukar da ruwa mai albarka daga sama sai Muka tsiro da lambuna da shi da kuma qwayoyin da ake girba
وَٱلنَّخۡلَ بَاسِقَٰتٖ لَّهَا طَلۡعٞ نَّضِيدٞ
Da kuma itatuwan dabinai dogwaye da suke da ‘ya’ya dodo-dodo
رِّزۡقٗا لِّلۡعِبَادِۖ وَأَحۡيَيۡنَا بِهِۦ بَلۡدَةٗ مَّيۡتٗاۚ كَذَٰلِكَ ٱلۡخُرُوجُ
Don arzuta bayi, Muka kuma raya busasshen gari da shi. Kamar haka ne fitowa (daga qabari) take
كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ وَأَصۡحَٰبُ ٱلرَّسِّ وَثَمُودُ
Mutanen Nuhu da ma’abota rijiyar Rassu da Samudawa (duka) sun qaryata (annabawa) a gabaninsu (watau mutanen Makka)
وَعَادٞ وَفِرۡعَوۡنُ وَإِخۡوَٰنُ لُوطٖ
Da kuma Adawa da Fir’auna da ‘yan’uwan Luxu (su ma sun qaryata)
وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡأَيۡكَةِ وَقَوۡمُ تُبَّعٖۚ كُلّٞ كَذَّبَ ٱلرُّسُلَ فَحَقَّ وَعِيدِ
Da kuma ma’abota surquqi[1] da mutanen Tubba’u[2]. Kowannensu ya qaryata manzanni, sai azabata ta tabbata (a kansu)
1- Watau mutanen Annabi Shu’aibu ().
2- Tubba’u shi ne sarkin Yaman.1- Watau mutanen Annabi Shu’aibu ().
2- Tubba’u shi ne sarkin Yaman.
أَفَعَيِينَا بِٱلۡخَلۡقِ ٱلۡأَوَّلِۚ بَلۡ هُمۡ فِي لَبۡسٖ مِّنۡ خَلۡقٖ جَدِيدٖ
Shin Mun gaza ne da halittar farko? A’a, su dai suna cikin shakka ne game da sake halitta
وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ وَنَعۡلَمُ مَا تُوَسۡوِسُ بِهِۦ نَفۡسُهُۥۖ وَنَحۡنُ أَقۡرَبُ إِلَيۡهِ مِنۡ حَبۡلِ ٱلۡوَرِيدِ
Haqiqa kuma Mun halicci mutum, kuma Mun san abin da ransa yake saqa masa; kuma Mu Muka fi kusa da shi fiye da jijiyar wuyansa
إِذۡ يَتَلَقَّى ٱلۡمُتَلَقِّيَانِ عَنِ ٱلۡيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ قَعِيدٞ
Yayin da (mala’iku biyu) masu haxuwa suka haxu ta dama da ta hagu suna zaune
مَّا يَلۡفِظُ مِن قَوۡلٍ إِلَّا لَدَيۡهِ رَقِيبٌ عَتِيدٞ
Ba wata magana da zai furta face a tare da shi akwai (mala’ika) mai kula kuma halartacce
وَجَآءَتۡ سَكۡرَةُ ٱلۡمَوۡتِ بِٱلۡحَقِّۖ ذَٰلِكَ مَا كُنتَ مِنۡهُ تَحِيدُ
Kuma magagin mutuwa ya zo da gaskiya; wannan ne abin da ka kasance kana kakkauce wa
وَنُفِخَ فِي ٱلصُّورِۚ ذَٰلِكَ يَوۡمُ ٱلۡوَعِيدِ
Aka kuma yi busa a qaho[1]. Wannan ita ce ranar narko
1- Watau busa ta biyu.
وَجَآءَتۡ كُلُّ نَفۡسٖ مَّعَهَا سَآئِقٞ وَشَهِيدٞ
Kuma kowane rai ya zo a tare da shi akwai mai kora da mai shaida[1]
1- Watau mala’iku biyu tare da kowane mutum, xaya yana kora shi; xaya kuma mai ba da shaida game da shi.
لَّقَدۡ كُنتَ فِي غَفۡلَةٖ مِّنۡ هَٰذَا فَكَشَفۡنَا عَنكَ غِطَآءَكَ فَبَصَرُكَ ٱلۡيَوۡمَ حَدِيدٞ
Haqiqa ka kasance a cikin gafala game da wannan, sai Muka yaye maka yanarka, to ganinka a yau tangaran yake
وَقَالَ قَرِينُهُۥ هَٰذَا مَا لَدَيَّ عَتِيدٌ
Mala’ikan da yake tare da shi kuma ya ce: “Wannan shi ne abin da yake hallare a tare da ni.”
أَلۡقِيَا فِي جَهَنَّمَ كُلَّ كَفَّارٍ عَنِيدٖ
(Aka ce da mala’ikun): “Ku jefa duk wani kafiri mai taurin kai cikin Jahannama
مَّنَّاعٖ لِّلۡخَيۡرِ مُعۡتَدٖ مُّرِيبٍ
“Mai yawan hana alheri, mai ta’addanci, mai shakka
ٱلَّذِي جَعَلَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَأَلۡقِيَاهُ فِي ٱلۡعَذَابِ ٱلشَّدِيدِ
“Wanda ya sanya wani abin bauta daban tare da Allah, saboda haka ku jefa shi cikin azaba mai tsanani.”
۞قَالَ قَرِينُهُۥ رَبَّنَا مَآ أَطۡغَيۡتُهُۥ وَلَٰكِن كَانَ فِي ضَلَٰلِۭ بَعِيدٖ
Shaixaninsa ya ce: “Ya Ubangijina, ni ban vatar da shi ba, sai dai kawai ya kasance cikin vata mai nisa.”
قَالَ لَا تَخۡتَصِمُواْ لَدَيَّ وَقَدۡ قَدَّمۡتُ إِلَيۡكُم بِٱلۡوَعِيدِ
(Allah) ya ce: “Kada ku yi husuma a gabana, haqiqa tuni Na gabatar muku da gargaxin azaba
مَا يُبَدَّلُ ٱلۡقَوۡلُ لَدَيَّ وَمَآ أَنَا۠ بِظَلَّـٰمٖ لِّلۡعَبِيدِ
“Ba a sauya magana a gabana, kuma Ni ba mai zaluntar bayi ba ne.”
يَوۡمَ نَقُولُ لِجَهَنَّمَ هَلِ ٱمۡتَلَأۡتِ وَتَقُولُ هَلۡ مِن مَّزِيدٖ
A ranar da za Mu ce da Jahannama: “Shin kin cika?” (Ita) kuma ta ce: “Shin akwai wani qari?”