سوره: Suratul Isra’i

آيه : 1

سُبۡحَٰنَ ٱلَّذِيٓ أَسۡرَىٰ بِعَبۡدِهِۦ لَيۡلٗا مِّنَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ إِلَى ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡأَقۡصَا ٱلَّذِي بَٰرَكۡنَا حَوۡلَهُۥ لِنُرِيَهُۥ مِنۡ ءَايَٰتِنَآۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ

Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi Isra’i da bawansa cikin dare daga Masallaci mai alfarma[1] zuwa Masallaci mafi nisa (na Qudus) wanda Muka albarkaci kewayensa, don Mu nuna masa wasu daga ayoyinmu. Lalle Shi Mai ji ne, Mai gani


1- Watau masallacin Ka’aba da yake Makka.


سوره: Suratul Isra’i

آيه : 2

وَءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلۡنَٰهُ هُدٗى لِّبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ أَلَّا تَتَّخِذُواْ مِن دُونِي وَكِيلٗا

Kuma Mun bai wa Musa Littafi Muka kuma sanya shi ya zama shiriya ga Banu Isra’ila cewa: “Kada ku riqi wani wakili ba ni ba.”



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 3

ذُرِّيَّةَ مَنۡ حَمَلۡنَا مَعَ نُوحٍۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَبۡدٗا شَكُورٗا

(Ya ku) zurriyar waxanda Muka xauko tare da Nuhu (a cikin jirgi). Lalle shi ya zamanto bawa ne mai yawan godiya



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 4

وَقَضَيۡنَآ إِلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ فِي ٱلۡكِتَٰبِ لَتُفۡسِدُنَّ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَرَّتَيۡنِ وَلَتَعۡلُنَّ عُلُوّٗا كَبِيرٗا

Muka kuma qaddara ga Banu Isra’ila cikin Littafin (Attaura) cewa: “Lalle tabbas za ku yi varna a bayan qasa sau biyu, kuma lalle tabbas za ku yi girman kai mai tsanani



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 5

فَإِذَا جَآءَ وَعۡدُ أُولَىٰهُمَا بَعَثۡنَا عَلَيۡكُمۡ عِبَادٗا لَّنَآ أُوْلِي بَأۡسٖ شَدِيدٖ فَجَاسُواْ خِلَٰلَ ٱلدِّيَارِۚ وَكَانَ وَعۡدٗا مَّفۡعُولٗا

“To idan alqawarin ta farkonsu (varna) ya zo sai Mu aiko muku da bayinmu masu tsananin qarfi sai su kutsa tsakiyar gidajen (naku). Kuma (wannan) ya zamanto alqawari ne mai faruwa



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 6

ثُمَّ رَدَدۡنَا لَكُمُ ٱلۡكَرَّةَ عَلَيۡهِمۡ وَأَمۡدَدۡنَٰكُم بِأَمۡوَٰلٖ وَبَنِينَ وَجَعَلۡنَٰكُمۡ أَكۡثَرَ نَفِيرًا

“Sannan kuma Muka ba ku damar galaba a kansu, Muka kuma qare ku da dukiyoyi da ‘ya’ya, Muka kuma sanya ku kuka zama mafi yawan jama’a



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 7

إِنۡ أَحۡسَنتُمۡ أَحۡسَنتُمۡ لِأَنفُسِكُمۡۖ وَإِنۡ أَسَأۡتُمۡ فَلَهَاۚ فَإِذَا جَآءَ وَعۡدُ ٱلۡأٓخِرَةِ لِيَسُـُٔواْ وُجُوهَكُمۡ وَلِيَدۡخُلُواْ ٱلۡمَسۡجِدَ كَمَا دَخَلُوهُ أَوَّلَ مَرَّةٖ وَلِيُتَبِّرُواْ مَا عَلَوۡاْ تَتۡبِيرًا

“Idan kun kyautata to kanku kuka kyautata wa, idan kuma kuka munana to kanku kuka yi wa. To idan alqawarin (varnar) ta qarshe ya zo (sai maqiyanku su zo) don su wulaqanta ku su kuma shiga masallaci (na Baitul Maqadis) kamar yadda suka shige shi tun farko, kuma za su yi raga-raga da (duk) abin da suka biyo ta kansa



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 8

عَسَىٰ رَبُّكُمۡ أَن يَرۡحَمَكُمۡۚ وَإِنۡ عُدتُّمۡ عُدۡنَاۚ وَجَعَلۡنَا جَهَنَّمَ لِلۡكَٰفِرِينَ حَصِيرًا

“Mai yiwuwa ne Ubangijinku ya ji qan ku. (Amma) kuma idan kuka dawo (kan varnar sai) Mu dawo (da azabtar da ku). Mun kuma sanya Jahannama ta zama shimfixa ga kafirai.”



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 9

إِنَّ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ يَهۡدِي لِلَّتِي هِيَ أَقۡوَمُ وَيُبَشِّرُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ أَنَّ لَهُمۡ أَجۡرٗا كَبِيرٗا

Lalle wannan Alqur’anin yana shiryarwa ne ga (hanya) mafi miqewa, yana kuma yi wa muminai waxanda suke yin kyawawan ayyuka albishir cewa, lalle suna da lada mai girma



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 10

وَأَنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ أَعۡتَدۡنَا لَهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا

Waxanda kuwa ba su yi imani da ranar lahira ba lalle Mun tanadar musu azaba mai raxaxi



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 11

وَيَدۡعُ ٱلۡإِنسَٰنُ بِٱلشَّرِّ دُعَآءَهُۥ بِٱلۡخَيۡرِۖ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ عَجُولٗا

Kuma mutum yakan roqi sharri[1] kamar yadda yake roqon alheri; mutum kuwa ya zamanto mai gaggawa ne


1- Watau idan ya yi fushi yakan yi wa kansa ko ‘ya’yansa ko dukiyarsa mummunar addu’a.


سوره: Suratul Isra’i

آيه : 12

وَجَعَلۡنَا ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ ءَايَتَيۡنِۖ فَمَحَوۡنَآ ءَايَةَ ٱلَّيۡلِ وَجَعَلۡنَآ ءَايَةَ ٱلنَّهَارِ مُبۡصِرَةٗ لِّتَبۡتَغُواْ فَضۡلٗا مِّن رَّبِّكُمۡ وَلِتَعۡلَمُواْ عَدَدَ ٱلسِّنِينَ وَٱلۡحِسَابَۚ وَكُلَّ شَيۡءٖ فَصَّلۡنَٰهُ تَفۡصِيلٗا

Muka kuma sanya dare da rana su zama ayoyi guda biyu; sai Muka shafe ayar dare (ta zama duhu) Muka kuma sanya ayar rana ta zama mai haskakawa, don ku nemi falala daga Ubangijinku, don kuma ku san yawan shekaru da lissafi. Kowane abu kuwa Mun rarrabe shi filla-filla



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 13

وَكُلَّ إِنسَٰنٍ أَلۡزَمۡنَٰهُ طَـٰٓئِرَهُۥ فِي عُنُقِهِۦۖ وَنُخۡرِجُ لَهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ كِتَٰبٗا يَلۡقَىٰهُ مَنشُورًا

Kuma kowane mutum Mun xaura masa littafin aikinsa a wuyansa, za kuma Mu fito masa da wani littafi a ranar alqiyama da zai same shi a buxe



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 14

ٱقۡرَأۡ كِتَٰبَكَ كَفَىٰ بِنَفۡسِكَ ٱلۡيَوۡمَ عَلَيۡكَ حَسِيبٗا

(A ce da shi): “Karanta littafinka; a yau ka isa ka yi wa kanka hukunci da kanka.”



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 15

مَّنِ ٱهۡتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهۡتَدِي لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيۡهَاۚ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۗ وَمَا كُنَّا مُعَذِّبِينَ حَتَّىٰ نَبۡعَثَ رَسُولٗا

Wanda ya shiriya to lalle yana shiriya ne don kansa; wanda kuwa ya vata to lalle yana vata ne don kansa. Ba kuwa wanda zai xauki nauyin laifin wani. Kuma ba Mu zamanto Masu azabtarwa ba har sai Mun aiko da manzo



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 16

وَإِذَآ أَرَدۡنَآ أَن نُّهۡلِكَ قَرۡيَةً أَمَرۡنَا مُتۡرَفِيهَا فَفَسَقُواْ فِيهَا فَحَقَّ عَلَيۡهَا ٱلۡقَوۡلُ فَدَمَّرۡنَٰهَا تَدۡمِيرٗا

Idan Muka nufi hallakar da wata alqarya sai Mu sanya ‘yan ta-moren cikinta su aikata fasiqanci a cikinta, sai kalmar azaba ta tabbata a kanta (watau alqaryar) sai Mu rugurguza ta ragaraga



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 17

وَكَمۡ أَهۡلَكۡنَا مِنَ ٱلۡقُرُونِ مِنۢ بَعۡدِ نُوحٖۗ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ بِذُنُوبِ عِبَادِهِۦ خَبِيرَۢا بَصِيرٗا

Al’umma nawa ne Muka hallaka bayan Nuhu? Kuma ai ya isa Ubangijinka Ya zamana Mai cikakken sani ne da gani ga zunuban bayinsa



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 18

مَّن كَانَ يُرِيدُ ٱلۡعَاجِلَةَ عَجَّلۡنَا لَهُۥ فِيهَا مَا نَشَآءُ لِمَن نُّرِيدُ ثُمَّ جَعَلۡنَا لَهُۥ جَهَنَّمَ يَصۡلَىٰهَا مَذۡمُومٗا مَّدۡحُورٗا

Wanda ya kasance yana nufin duniya ne (kawai) to za Mu gaggauto masa a cikinta abin da Muka ga dama ga wanda Muka yi nufi; sannan Mu sanya masa Jahannama, ya shige ta (a lahira) yana abin zargi, korarre (daga rahamar Allah)



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 19

وَمَنۡ أَرَادَ ٱلۡأٓخِرَةَ وَسَعَىٰ لَهَا سَعۡيَهَا وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَأُوْلَـٰٓئِكَ كَانَ سَعۡيُهُم مَّشۡكُورٗا

Wanda kuma ya nufi lahira ya kuma yi aiki irin nata dominta alhalin yana mumini, to waxannan aikinsu ya zamanto abin godewa ne (a wurin Allah)



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 20

كُلّٗا نُّمِدُّ هَـٰٓؤُلَآءِ وَهَـٰٓؤُلَآءِ مِنۡ عَطَآءِ رَبِّكَۚ وَمَا كَانَ عَطَآءُ رَبِّكَ مَحۡظُورًا

Dukkansu Muna wadata su ne da baiwar Ubangijinka; waxannan da kuma waxancan. Baiwar Ubangijinka kuwa ba ta zamo abar hanawa ba



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 21

ٱنظُرۡ كَيۡفَ فَضَّلۡنَا بَعۡضَهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۚ وَلَلۡأٓخِرَةُ أَكۡبَرُ دَرَجَٰتٖ وَأَكۡبَرُ تَفۡضِيلٗا

Dubi yadda Muka fifita wasunsu a kan wasu. Lalle kuwa lahira ita ta fi girman darajoji, kuma ta fi girman fifiko



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 22

لَّا تَجۡعَلۡ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتَقۡعُدَ مَذۡمُومٗا مَّخۡذُولٗا

Kada ka haxa wani abin bauta daban tare da Allah, sai ka zama abin zargi tavavve



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 23

۞وَقَضَىٰ رَبُّكَ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّآ إِيَّاهُ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنًاۚ إِمَّا يَبۡلُغَنَّ عِندَكَ ٱلۡكِبَرَ أَحَدُهُمَآ أَوۡ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُل لَّهُمَآ أُفّٖ وَلَا تَنۡهَرۡهُمَا وَقُل لَّهُمَا قَوۡلٗا كَرِيمٗا

Ubangijinka kuwa Ya hukunta cewa, kada ku bauta wa (wani) sai Shi kaxai, kuma ku kyautatawa iyaye. Ko dai ya zamanto xayansu ne ya manyanta tare da kai, ko kuma dukkansu, to kada ka nuna qosawarka da su, kada kuma ka daka musu tsawa; ka yi musu magana ta girmamawa



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 24

وَٱخۡفِضۡ لَهُمَا جَنَاحَ ٱلذُّلِّ مِنَ ٱلرَّحۡمَةِ وَقُل رَّبِّ ٱرۡحَمۡهُمَا كَمَا رَبَّيَانِي صَغِيرٗا

Ka kuma qasqantar da kai gare su don tausayawa, ka kuma ce: “Ubangijina Ka ji qan su kamar yadda suka raine ni ina xan qarami.”



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 25

رَّبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِمَا فِي نُفُوسِكُمۡۚ إِن تَكُونُواْ صَٰلِحِينَ فَإِنَّهُۥ كَانَ لِلۡأَوَّـٰبِينَ غَفُورٗا

Ubangijinku ne Mafi sanin abin da yake zukatanku. Idan kuka zamanto nagari, to lalle Shi Ya tabbata Mai gafara ne ga masu komawa gare Shi da tuba



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 26

وَءَاتِ ذَا ٱلۡقُرۡبَىٰ حَقَّهُۥ وَٱلۡمِسۡكِينَ وَٱبۡنَ ٱلسَّبِيلِ وَلَا تُبَذِّرۡ تَبۡذِيرًا

Kuma ka bai wa makusanci haqqinsa, da miskini da matafiyi, kada kuma ka yi kowane irin almubazzaranci



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 27

إِنَّ ٱلۡمُبَذِّرِينَ كَانُوٓاْ إِخۡوَٰنَ ٱلشَّيَٰطِينِۖ وَكَانَ ٱلشَّيۡطَٰنُ لِرَبِّهِۦ كَفُورٗا

Lalle masu almubazzaranci sun tabbata dangin shaixanu; Shaixan kuwa ya zamanto mai yawan kafirce wa Ubangijinsa ne



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 28

وَإِمَّا تُعۡرِضَنَّ عَنۡهُمُ ٱبۡتِغَآءَ رَحۡمَةٖ مِّن رَّبِّكَ تَرۡجُوهَا فَقُل لَّهُمۡ قَوۡلٗا مَّيۡسُورٗا

Idan kuwa ka kau da kanka daga gare su don neman wata rahama daga Ubangijinka da kake sa ran samun ta[1], to sai ka yi musu magana mai daxi


1- Watau idan masu neman taimako a wurinsa suka zo ba ya da shi, shi ma yana jiran Allah ya hore masa.


سوره: Suratul Isra’i

آيه : 29

وَلَا تَجۡعَلۡ يَدَكَ مَغۡلُولَةً إِلَىٰ عُنُقِكَ وَلَا تَبۡسُطۡهَا كُلَّ ٱلۡبَسۡطِ فَتَقۡعُدَ مَلُومٗا مَّحۡسُورًا

Kada kuma ka ququnce hannunka a wuyanka (ka qi yin kyauta), kada kuma ka shimfixa shi gaba xaya (watau ka saki komai), sai ka wayi gari abin zargi (saboda rowa), mai nadama (saboda almubazaranci)



سوره: Suratul Isra’i

آيه : 30

إِنَّ رَبَّكَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرَۢا بَصِيرٗا

Lalle Ubangijinka Yana shimfixa arziki ga wanda Ya ga dama, kuma Yana quntatawa (ga wanda Ya ga dama). Lalle Shi Ya tabbata Masani ne, Mai ganin bayinsa