بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin qai[1]
1- Bisimilla Alqur’ani ce, kuma aya ce a ‘Suratun Namli aya ta 30’; sannan ita aya ce a farkon ‘Suratul Fatiha’, sannan an saukar da ita a farkon kowace sura don bambance tsakanin qarshen sura da farkon wata sura. Amma ban da tsakanin ‘Suratul Anfal’ da ‘Taubah’.
ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai
ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
Mai rahama Mai jin qai[1]
1- Allah, suna ne na wanda ya cancanta a bauta masa shi kaxai. Ba a kiran wani da shi. Arrahman wanda yake nuna yalwatacciyar rahmar Allah wadda take shafar kowa da komai a nan duniya da kuma sunansa Arrahim, wanda yake nuna kevantacciyar rahamarsa a lahira ga muminai kawai masu tsoran sa.
مَٰلِكِ يَوۡمِ ٱلدِّينِ
Mamallakin ranar sakamako
إِيَّاكَ نَعۡبُدُ وَإِيَّاكَ نَسۡتَعِينُ
Kai kaxai muke bautata wa, kuma Kai kaxai muke neman taimakonka
ٱهۡدِنَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ
Ka shiryar da mu tafarkin nan madaidaici
صِرَٰطَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمۡتَ عَلَيۡهِمۡ غَيۡرِ ٱلۡمَغۡضُوبِ عَلَيۡهِمۡ وَلَا ٱلضَّآلِّينَ
Tafarkin waxanda Ka yi wa ni’ima[1], ba waxanda aka yi fushi da su ba[2], ba kuma vatattu ba[3]
1- Su ne waxanda aka ambata a aya ta 69 a Suratun Nisa’i.
2- Watau waxanda suka san gaskiya suka take, kamar Yahudawa.
3- Watau waxanda suke bautar Allah da jahilci, kamar Nasara.