سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 181

لَّقَدۡ سَمِعَ ٱللَّهُ قَوۡلَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ فَقِيرٞ وَنَحۡنُ أَغۡنِيَآءُۘ سَنَكۡتُبُ مَا قَالُواْ وَقَتۡلَهُمُ ٱلۡأَنۢبِيَآءَ بِغَيۡرِ حَقّٖ وَنَقُولُ ذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ

Tabbas haqiqa Allah ya ji maganar waxannan da suka ce: “Lalle Allah mataulaci ne, mu ne mawadata.” Da sannu za Mu rubuta abin da suka faxa, da kuma kisan da suka riqa yi wa annabawa ba tare da wani haqqi ba, kuma za Mu ce: “Ku xanxani azaba mai quna



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 182

ذَٰلِكَ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيكُمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَيۡسَ بِظَلَّامٖ لِّلۡعَبِيدِ

“Wannan kuwa, saboda abin da hannayenku suka gabatar ne, kuma lalle Allah ba mai zaluntar bayinsa ne ba.”



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 183

ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ عَهِدَ إِلَيۡنَآ أَلَّا نُؤۡمِنَ لِرَسُولٍ حَتَّىٰ يَأۡتِيَنَا بِقُرۡبَانٖ تَأۡكُلُهُ ٱلنَّارُۗ قُلۡ قَدۡ جَآءَكُمۡ رُسُلٞ مِّن قَبۡلِي بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَبِٱلَّذِي قُلۡتُمۡ فَلِمَ قَتَلۡتُمُوهُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Su ne waxanda suka ce: “Lalle Allah Ya yi alqawari da mu kar mu yi imani da kowane manzo har sai ya zo mana da wata sadaka wadda wuta za ta cinye ta.” Ka ce: “Haqiqa manzanni sun zo muku tun kafin ni, da hujjoji da kuma abin da kuka ce xin, to don me kuka kashe su in kun kasance masu gaskiya?”



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 184

فَإِن كَذَّبُوكَ فَقَدۡ كُذِّبَ رُسُلٞ مِّن قَبۡلِكَ جَآءُو بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلزُّبُرِ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُنِيرِ

To idan sun qaryata ka, to haqiqa an qaryata manzanni kafinka, waxanda suka zo da hujjoji da littattafai da Littafi mai haskakawa



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 185

كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۗ وَإِنَّمَا تُوَفَّوۡنَ أُجُورَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ فَمَن زُحۡزِحَ عَنِ ٱلنَّارِ وَأُدۡخِلَ ٱلۡجَنَّةَ فَقَدۡ فَازَۗ وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا مَتَٰعُ ٱلۡغُرُورِ

Kowane rai zai xanxani mutuwa. Kuma a ranar alqiyama ne za a cika muku ladan ayyukanku; to duk wanda aka nisanta shi daga wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to haqiqa ya rabauta. Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face jin daxi mai ruxarwa



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 186

۞لَتُبۡلَوُنَّ فِيٓ أَمۡوَٰلِكُمۡ وَأَنفُسِكُمۡ وَلَتَسۡمَعُنَّ مِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِكُمۡ وَمِنَ ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُوٓاْ أَذٗى كَثِيرٗاۚ وَإِن تَصۡبِرُواْ وَتَتَّقُواْ فَإِنَّ ذَٰلِكَ مِنۡ عَزۡمِ ٱلۡأُمُورِ

Lalle za a jarrabe ku a cikin dukiyoyinku da rayukanku, kuma lalle za ku riqa jin cutarwa mai yawa daga waxanda aka bai wa Littafi kafinku, haka kuma daga waxanda suke mushirikai. Amma idan har kuka yi haquri, kuma kuka tsare dokar Allah, to lalle wannan yana daga cikin manyan al’amura



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 187

وَإِذۡ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَٰقَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ لَتُبَيِّنُنَّهُۥ لِلنَّاسِ وَلَا تَكۡتُمُونَهُۥ فَنَبَذُوهُ وَرَآءَ ظُهُورِهِمۡ وَٱشۡتَرَوۡاْ بِهِۦ ثَمَنٗا قَلِيلٗاۖ فَبِئۡسَ مَا يَشۡتَرُونَ

Kuma ka tuna lokacin da Allah Ya xauki alqawari daga waxanda aka bai wa Littafi cewa: “Lalle ku bayyana shi ga mutane, kuma kada ku voye shi.” Sai suka jefar da shi can bayansu, kuma suka musanya shi da wani xan farashi qanqani. To tir da abin da suke yin musanye da shi



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 188

لَا تَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ يَفۡرَحُونَ بِمَآ أَتَواْ وَّيُحِبُّونَ أَن يُحۡمَدُواْ بِمَا لَمۡ يَفۡعَلُواْ فَلَا تَحۡسَبَنَّهُم بِمَفَازَةٖ مِّنَ ٱلۡعَذَابِۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Kada ka yi tsammanin waxanda suke yin farin ciki da irin abin da suka aikata, kuma suna son a riqa yabon su da abin da ba su aikata ba, to kada ka yi tsammanin za su tsira daga azaba, kuma suna da azaba mai raxaxi



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 189

وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Kuma ga Allah ne mulkin sammai da qasa yake. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 190

إِنَّ فِي خَلۡقِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَٰفِ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ لَأٓيَٰتٖ لِّأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Lalle a cikin halittar sammai da qasa da sassavawar dare da rana, tabbas akwai ayoyi ga ma’abota hankula



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 191

ٱلَّذِينَ يَذۡكُرُونَ ٱللَّهَ قِيَٰمٗا وَقُعُودٗا وَعَلَىٰ جُنُوبِهِمۡ وَيَتَفَكَّرُونَ فِي خَلۡقِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ رَبَّنَا مَا خَلَقۡتَ هَٰذَا بَٰطِلٗا سُبۡحَٰنَكَ فَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ

Waxanda suke ambaton Allah a tsaye da kuma zaune da kuma kishingixe, suna kuma tunani a kan halittar sammai da qasa, (suna cewa): “Ya Ubangijinmu, ba Ka halicci wannan a banza ba, tsarki ya tabbata gare Ka, Ka tserar da mu daga azabar wuta



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 192

رَبَّنَآ إِنَّكَ مَن تُدۡخِلِ ٱلنَّارَ فَقَدۡ أَخۡزَيۡتَهُۥۖ وَمَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِنۡ أَنصَارٖ

“Ya Ubangijinmu, lalle duk wanda Ka shigar da shi wuta, to haqiqa Ka kunyata shi; kuma azzalumai ba su da mai taimakon su



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 193

رَّبَّنَآ إِنَّنَا سَمِعۡنَا مُنَادِيٗا يُنَادِي لِلۡإِيمَٰنِ أَنۡ ءَامِنُواْ بِرَبِّكُمۡ فَـَٔامَنَّاۚ رَبَّنَا فَٱغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَا وَكَفِّرۡ عَنَّا سَيِّـَٔاتِنَا وَتَوَفَّنَا مَعَ ٱلۡأَبۡرَارِ

“Ya Ubangijinmu, lalle mu mun ji wani mai kira yana yin kira zuwa imani cewa: “Ku yi imani da Ubangijinku;” sai muka yi imani. Ya Ubangijinmu, Ka gafarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare mana kurakuranmu, kuma Ka karvi rayukanmu tare da mutane masu xa’a



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 194

رَبَّنَا وَءَاتِنَا مَا وَعَدتَّنَا عَلَىٰ رُسُلِكَ وَلَا تُخۡزِنَا يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ إِنَّكَ لَا تُخۡلِفُ ٱلۡمِيعَادَ

“Ya Ubangijinmu, kuma Ka ba mu abin da Ka yi mana alqawari da shi ta harshen manzanninka, kuma kada Ka kunyatar da mu ranar alqiyama. Lalle Kai ba Ka sava alqawari.”



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 195

فَٱسۡتَجَابَ لَهُمۡ رَبُّهُمۡ أَنِّي لَآ أُضِيعُ عَمَلَ عَٰمِلٖ مِّنكُم مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰۖ بَعۡضُكُم مِّنۢ بَعۡضٖۖ فَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ وَأُخۡرِجُواْ مِن دِيَٰرِهِمۡ وَأُوذُواْ فِي سَبِيلِي وَقَٰتَلُواْ وَقُتِلُواْ لَأُكَفِّرَنَّ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَلَأُدۡخِلَنَّهُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ ثَوَابٗا مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ عِندَهُۥ حُسۡنُ ٱلثَّوَابِ

Sai Ubangijinsu Ya amsa musu (cewa): “Lalle Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki daga cikinku ba, namiji ne ko mace; sashinku yana tare da sashe. To waxanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidajensu kuma aka cutar da su wajen bin tafarkina kuma suka yi yaqi kuma aka kashe su, lalle zan kankare musu kurakuransu, kuma lalle zan shigar da su gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu. (Wannan) lada ne daga wajen Allah, kuma a wurin Allah ne mafi kyawun lada yake.”



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 196

لَا يَغُرَّنَّكَ تَقَلُّبُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي ٱلۡبِلَٰدِ

Kada zirga-zirgar kafirai a cikin garuruwa ta ruxe ka



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 197

مَتَٰعٞ قَلِيلٞ ثُمَّ مَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ

Wani xan jin daxi ne qanqani, sannan makomarsu Jahannama. Kuma tir da wannan shimfixar



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 198

لَٰكِنِ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ رَبَّهُمۡ لَهُمۡ جَنَّـٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا نُزُلٗا مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِۗ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ خَيۡرٞ لِّلۡأَبۡرَارِ

Amma waxanda suka bi dokokin Ubangijinsu suna da gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, za su dawwama a cikinsu, wannan liyafa ce ta musamman daga wajen Allah. Kuma abin da yake wajen Allah shi ne mafi alheri ga masu biyayya



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 199

وَإِنَّ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ لَمَن يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكُمۡ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِمۡ خَٰشِعِينَ لِلَّهِ لَا يَشۡتَرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ ثَمَنٗا قَلِيلًاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

Kuma lalle a cikin Ma’abota Littafi, tabbas akwai waxanda suke yin imani da Allah da kuma abin da aka saukar muku da kuma abin da aka saukar musu, suna masu qasqantar da kai ga Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da wani xan farashi qanqani. Waxannan suna da lada a wajen Ubangijinsu. Lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne



سوره: Suratu Ali-Imran

آيه : 200

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱصۡبِرُواْ وَصَابِرُواْ وَرَابِطُواْ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi haquri, kuma ku jure matuqa ga yin haquri, kuma ku tsare iyakokin qasa, kuma ku kiyaye dokokin Allah don ku sami rabauta