وَفَٰكِهَةٗ وَأَبّٗا
Da kayan marmari da makiyaya
مَّتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ
Don jin daxinku da na dabbobinku
فَإِذَا جَآءَتِ ٱلصَّآخَّةُ
Sannan idan mai sa kurunta ta zo (watau busa ta farko)
يَوۡمَ يَفِرُّ ٱلۡمَرۡءُ مِنۡ أَخِيهِ
A ranar da mutum yake guje wa xan’uwansa
وَأُمِّهِۦ وَأَبِيهِ
Da uwarsa da ubansa
وَصَٰحِبَتِهِۦ وَبَنِيهِ
Da matarsa da ‘ya’yansa
لِكُلِّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ يَوۡمَئِذٖ شَأۡنٞ يُغۡنِيهِ
Kowane mutum daga cikinsu a wannan ranar yana da lamarin da ya sha kansa
وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ مُّسۡفِرَةٞ
Wasu fuskoki a wannan ranar masu haske ne
ضَاحِكَةٞ مُّسۡتَبۡشِرَةٞ
Masu dariya, masu farin ciki
وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذٍ عَلَيۡهَا غَبَرَةٞ
Wasu fuskokin kuma a ranar akwai qura a kansu
تَرۡهَقُهَا قَتَرَةٌ
Baqin ciki zai lulluve su
أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَفَرَةُ ٱلۡفَجَرَةُ
Waxannan su ne kafirai mavarnata