قَالُواْ يَٰوَيۡلَنَآ إِنَّا كُنَّا طَٰغِينَ
Suka ce: “Kaiconmu, lalle mu mun kasance masu shisshigi
عَسَىٰ رَبُّنَآ أَن يُبۡدِلَنَا خَيۡرٗا مِّنۡهَآ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا رَٰغِبُونَ
“Tsammanin Ubangijinmu zai musanya mana wadda ta fi ta, lalle mu masu kwaxayi ne a wurin Ubangijinmu[1].”
1- Watau zai ba su wata gonar da ta fi tasu, suna kuma fatan zai yi musu afuwa ya yafe musu kurakuransu.
كَذَٰلِكَ ٱلۡعَذَابُۖ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَكۡبَرُۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ
Kamar haka ne azaba take tabbata; kuma tabbas azabar lahira ta fi girma. Da sun kasance sun san haka
إِنَّ لِلۡمُتَّقِينَ عِندَ رَبِّهِمۡ جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ
Lalle masu taqawa suna da gidajen Aljannar ni’ima a wurin Ubangijinsu
أَفَنَجۡعَلُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ كَٱلۡمُجۡرِمِينَ
Yanzu za Mu sanya Musulmi kamar kangararru?
مَا لَكُمۡ كَيۡفَ تَحۡكُمُونَ
Me ya same ku ne, yaya kuke irin wannan hukuncin?
أَمۡ لَكُمۡ كِتَٰبٞ فِيهِ تَدۡرُسُونَ
Ko kuna da wani littafi ne wanda a cikinsa kuke karantawa?
إِنَّ لَكُمۡ فِيهِ لَمَا تَخَيَّرُونَ
(Cewa) a cikinsa lalle kuna da abin da kuke zava?
أَمۡ لَكُمۡ أَيۡمَٰنٌ عَلَيۡنَا بَٰلِغَةٌ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ إِنَّ لَكُمۡ لَمَا تَحۡكُمُونَ
Ko kuwa kuna da wasu alqawura na rantsuwa ne (tabbatattu) a kanmu har zuwa ranar alqiyama cewa, lalle kuna da abin da kuke hukunta wa (kanku)?
سَلۡهُمۡ أَيُّهُم بِذَٰلِكَ زَعِيمٌ
Ka tambaye su wane ne a cikinsu ya yi lamuni game da wannan?
أَمۡ لَهُمۡ شُرَكَآءُ فَلۡيَأۡتُواْ بِشُرَكَآئِهِمۡ إِن كَانُواْ صَٰدِقِينَ
Ko kuwa suna da wasu ababan tarayya ne? To su kawo ababan tarayyar tasu idan sun kasance masu gaskiya
يَوۡمَ يُكۡشَفُ عَن سَاقٖ وَيُدۡعَوۡنَ إِلَى ٱلسُّجُودِ فَلَا يَسۡتَطِيعُونَ
(Ka tuna) ranar da za a yaye qwauri[1] a kuma kirawo su zuwa yin sujjada sannan su rasa ikon yi
1- Watau ranar da Allah () zai kware qwaurinsa mai daraja wanda bai yi kama da wani abu na halittarsa ba.
خَٰشِعَةً أَبۡصَٰرُهُمۡ تَرۡهَقُهُمۡ ذِلَّةٞۖ وَقَدۡ كَانُواْ يُدۡعَوۡنَ إِلَى ٱلسُّجُودِ وَهُمۡ سَٰلِمُونَ
Idanuwansu a qasqance, wulaqanci ya lulluve su. Haqiqa kuwa a duniya sun kasance ana kiran su zuwa yin sujjada alhali suna lafiyayyu
فَذَرۡنِي وَمَن يُكَذِّبُ بِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِۖ سَنَسۡتَدۡرِجُهُم مِّنۡ حَيۡثُ لَا يَعۡلَمُونَ
Saboda haka ka bar Ni da wanda yake qaryata wannan Alqur’ani; ba da daxewa ba za Mu yi musu talala ta inda ba za su sani ba
وَأُمۡلِي لَهُمۡۚ إِنَّ كَيۡدِي مَتِينٌ
Kuma zan saurara musu. Lalle kaidina mai qarfi ne
أَمۡ تَسۡـَٔلُهُمۡ أَجۡرٗا فَهُم مِّن مَّغۡرَمٖ مُّثۡقَلُونَ
Ko kuwa kana tambayar su wani lada ne, saboda haka biyan (wannan lada) ya yi musu nauyi?
أَمۡ عِندَهُمُ ٱلۡغَيۡبُ فَهُمۡ يَكۡتُبُونَ
Ko kuwa sanin gaibu a wurinsu yake, saboda haka suke rubuto shi?
فَٱصۡبِرۡ لِحُكۡمِ رَبِّكَ وَلَا تَكُن كَصَاحِبِ ٱلۡحُوتِ إِذۡ نَادَىٰ وَهُوَ مَكۡظُومٞ
To ka yi haquri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar ma’abocin kifi (Yunus) a yayin da ya yi kira, alhali shi yana cike da baqin ciki
لَّوۡلَآ أَن تَدَٰرَكَهُۥ نِعۡمَةٞ مِّن رَّبِّهِۦ لَنُبِذَ بِٱلۡعَرَآءِ وَهُوَ مَذۡمُومٞ
Ba don wata rahama daga Ubangijinsa ta riske shi ba, da an jefar da shi a qungurmin daji alhali shi yana abin suka
فَٱجۡتَبَٰهُ رَبُّهُۥ فَجَعَلَهُۥ مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
Sai Ubangijinsa Ya zave shi Ya sanya shi daga (bayi) nagari
وَإِن يَكَادُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَيُزۡلِقُونَكَ بِأَبۡصَٰرِهِمۡ لَمَّا سَمِعُواْ ٱلذِّكۡرَ وَيَقُولُونَ إِنَّهُۥ لَمَجۡنُونٞ
Lalle kuma waxanda suka kafirta sun yi kusa su kayar da kai da kallonsu yayin da suka ji Alqur’ani, suka kuma riqa cewa: “Lalle shi tabbas mahaukaci ne!”
وَمَا هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ لِّلۡعَٰلَمِينَ
Shi kuwa (Alqur’ani) ba wani abu ba ne face gargaxi ga talikai