قُلۡ تَرَبَّصُواْ فَإِنِّي مَعَكُم مِّنَ ٱلۡمُتَرَبِّصِينَ
Ka ce, “To ku saurara, ni ma lalle ina cikin masu sauraron.”
أَمۡ تَأۡمُرُهُمۡ أَحۡلَٰمُهُم بِهَٰذَآۚ أَمۡ هُمۡ قَوۡمٞ طَاغُونَ
Ko kuwa hankullansu ne suke umartar su da wannan? A’a, su dai mutane ne masu tsaurin kai
أَمۡ يَقُولُونَ تَقَوَّلَهُۥۚ بَل لَّا يُؤۡمِنُونَ
Ko kuwa suna cewa: “Ya qago shi?” A’a, su dai ba sa yin imani ne kawai
فَلۡيَأۡتُواْ بِحَدِيثٖ مِّثۡلِهِۦٓ إِن كَانُواْ صَٰدِقِينَ
To su zo da wani zance irinsa idan sun kasance masu gaskiya
أَمۡ خُلِقُواْ مِنۡ غَيۡرِ شَيۡءٍ أَمۡ هُمُ ٱلۡخَٰلِقُونَ
Ko kuwa an halicce su ne ba da wani mai halitta ba, ko kuwa su ne masu halittar (kansu)?
أَمۡ خَلَقُواْ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۚ بَل لَّا يُوقِنُونَ
Ko kuwa su suka halicci sammai da qasa? A’a, ba sa dai sakankancewa ne
أَمۡ عِندَهُمۡ خَزَآئِنُ رَبِّكَ أَمۡ هُمُ ٱلۡمُصَۜيۡطِرُونَ
Ko kuwa taskokin Ubangijinka suna wurinsu ne, ko kuwa su ne masu iko?
أَمۡ لَهُمۡ سُلَّمٞ يَسۡتَمِعُونَ فِيهِۖ فَلۡيَأۡتِ مُسۡتَمِعُهُم بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ
Ko kuwa suna da wani tsani ne da suke jiyo (zancen Allah) ta kansa[1]? To mai jiyowar tasu ya zo da wata hujja mabayyaniya
1- Watau cewa su ne masu gaskiya, Annabi () maqaryaci ne?
أَمۡ لَهُ ٱلۡبَنَٰتُ وَلَكُمُ ٱلۡبَنُونَ
Ko kuwa Shi ne zai zama mai ‘ya’ya mata, ku kuwa ku zamanto da ‘ya’ya maza?
أَمۡ تَسۡـَٔلُهُمۡ أَجۡرٗا فَهُم مِّن مَّغۡرَمٖ مُّثۡقَلُونَ
Ko kuwa kana tambayar su wani lada ne, saboda haka bashi ya yi musu nauyi?
أَمۡ عِندَهُمُ ٱلۡغَيۡبُ فَهُمۡ يَكۡتُبُونَ
Ko kuwa sun san gaibu ne, saboda haka su ne suke rubutawa
أَمۡ يُرِيدُونَ كَيۡدٗاۖ فَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ هُمُ ٱلۡمَكِيدُونَ
Ko kuwa suna nufin (yi maka) makirci ne? To waxanda suka kafirce su ne waxanda makircinsu zai kama su
أَمۡ لَهُمۡ إِلَٰهٌ غَيۡرُ ٱللَّهِۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Ko kuwa suna da wani abin bauta ne ba Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke tara (Shi da shi)
وَإِن يَرَوۡاْ كِسۡفٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ سَاقِطٗا يَقُولُواْ سَحَابٞ مَّرۡكُومٞ
Da kuwa za su ga wani yanki na azaba mai faxowa daga sama da sai su ce: “Hadari ne haxaxxe.”
فَذَرۡهُمۡ حَتَّىٰ يُلَٰقُواْ يَوۡمَهُمُ ٱلَّذِي فِيهِ يُصۡعَقُونَ
To ka rabu da su har sai sun haxu da ranarsu wadda za a karvi rayukansu a cikinta
يَوۡمَ لَا يُغۡنِي عَنۡهُمۡ كَيۡدُهُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ
Ranar da makircinsu ba zai maganta musu komai ba, kuma su ba za a taimake su ba
وَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ عَذَابٗا دُونَ ذَٰلِكَ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Lalle kuma waxanda suka yi zalunci suna da wata azabar daban[1] ban da wannan (ta lahira), sai dai kuma mafi yawansu ba su sani ba
1- Watau a nan duniya ta hanyar kisa a wajen yaqi ko kamu a matsayin ribatattu ko kuma azabar qabari bayan sun mutu.
وَٱصۡبِرۡ لِحُكۡمِ رَبِّكَ فَإِنَّكَ بِأَعۡيُنِنَاۖ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ حِينَ تَقُومُ
Kuma ka yi haquri da hukuncin Ubangijika, don ko lalle kana qarqashin lurarmu; kuma ka yi tasbihi da yabon Ubangijinka lokacin da za ka tashi (daga bacci)
وَمِنَ ٱلَّيۡلِ فَسَبِّحۡهُ وَإِدۡبَٰرَ ٱلنُّجُومِ
Da daddare kuma sai ka tsarkake Shi da kuma lokacin da taurari suka ba da baya