وَأُزۡلِفَتِ ٱلۡجَنَّةُ لِلۡمُتَّقِينَ غَيۡرَ بَعِيدٍ
Aka kuma kusantar da Aljanna ga masu tsoron Allah, ba tare da nisa ba
هَٰذَا مَا تُوعَدُونَ لِكُلِّ أَوَّابٍ حَفِيظٖ
(Sai a ce da su): “Wannan ne abin da ake yi muku alqawarinsa, (ga shi nan a tanade) ga duk wani mai yawan komawa ga Allah, mai kiyaye (dokokinsa)
مَّنۡ خَشِيَ ٱلرَّحۡمَٰنَ بِٱلۡغَيۡبِ وَجَآءَ بِقَلۡبٖ مُّنِيبٍ
“Wanda ya ji tsoron Allah a voye, ya zo kuma da zuciya mai komawa ga Allah.”
ٱدۡخُلُوهَا بِسَلَٰمٖۖ ذَٰلِكَ يَوۡمُ ٱلۡخُلُودِ
(Za a ce da su): Ku shige ta da aminci; wannan ita ce ranar dawwama
لَهُم مَّا يَشَآءُونَ فِيهَا وَلَدَيۡنَا مَزِيدٞ
Suna da duk abin da suka dama a cikinta, kuma wurinmu akwai wani qari[1]
1- Watau qarin wasu ni’imomi, daga cikinsu akwai ganin Fuskar Allah da samun yardarsa ta har abada.
وَكَمۡ أَهۡلَكۡنَا قَبۡلَهُم مِّن قَرۡنٍ هُمۡ أَشَدُّ مِنۡهُم بَطۡشٗا فَنَقَّبُواْ فِي ٱلۡبِلَٰدِ هَلۡ مِن مَّحِيصٍ
Al’ummu nawa Muka hallaka a gabaninsu waxanda suka fi su tsananin qarfi, sai suka riqa bincike cikin garuruwa ko akwai wata matsera
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَذِكۡرَىٰ لِمَن كَانَ لَهُۥ قَلۡبٌ أَوۡ أَلۡقَى ٱلسَّمۡعَ وَهُوَ شَهِيدٞ
Lalle game da wannan tabbas akwai wa’azi ga wanda ya kasance yana da hankali ko kuma ya karkaxe kunne (don sauraron wa’azi), alhali zuciyarsa tana tare da shi
وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ وَمَا مَسَّنَا مِن لُّغُوبٖ
Haqiqa kuma Mun halicci sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu cikin kwana shida, kuma wata gajiya ba ta shafe mu ba
فَٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ قَبۡلَ طُلُوعِ ٱلشَّمۡسِ وَقَبۡلَ ٱلۡغُرُوبِ
To ka yi haquri a kan abin da suke faxa, ka kuma yi tasbihi da yabon Ubangijinka kafin fudowar rana da kuma kafin faxuwarta
وَمِنَ ٱلَّيۡلِ فَسَبِّحۡهُ وَأَدۡبَٰرَ ٱلسُّجُودِ
Da daddare kuma sai ka tsarkake shi, da kuma bayan salloli
وَٱسۡتَمِعۡ يَوۡمَ يُنَادِ ٱلۡمُنَادِ مِن مَّكَانٖ قَرِيبٖ
Ka kuma saurara ranar da mai kira zai yi kira[1] daga wani wuri makusanci
1- Watau mala’ikan da aka wakilta domin busa qaho.
يَوۡمَ يَسۡمَعُونَ ٱلصَّيۡحَةَ بِٱلۡحَقِّۚ ذَٰلِكَ يَوۡمُ ٱلۡخُرُوجِ
A ranar da (talikai) za su ji tsawa ta gaskiya[1]. Wannan ita ce ranar fitowa (daga qabari)
1- Watau busa ta biyu.
إِنَّا نَحۡنُ نُحۡيِۦ وَنُمِيتُ وَإِلَيۡنَا ٱلۡمَصِيرُ
Lalle Mu ne Muke rayawa, Muke kuma kashewa, kuma makoma zuwa gare Mu ne
يَوۡمَ تَشَقَّقُ ٱلۡأَرۡضُ عَنۡهُمۡ سِرَاعٗاۚ ذَٰلِكَ حَشۡرٌ عَلَيۡنَا يَسِيرٞ
A ranar da qasa za ta tsattsage musu (su fito) da gaggawa. Wannan tattarawa ce mai sauqi a gare Mu
نَّحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَقُولُونَۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيۡهِم بِجَبَّارٖۖ فَذَكِّرۡ بِٱلۡقُرۡءَانِ مَن يَخَافُ وَعِيدِ
Mu ne Muka fi sanin abin da (kafiran Makka) suke faxa; kuma kai ba mai tilasta musu ba ne; saboda haka sai ka yi wa’azi da Alqur’ani ga wanda yake tsoron azabata